GAISUWA GA ALBANI
Malam Muhammad Auwal Adam Albani na Zariya sanannen mutum ne da ya shahara a harkar karantar da Sunna da a}idar salafiyya.
Tun wajejen 1997 nake koyon karatuka da dama a wajen shi, musamman a fannonin Hadisi, A}ida, Usul, da sauran fannoni na addinin musulunci.
Na da]e ina tunanin in yi mishi wa}a, amma hakan bai samu cikin gaugawa ba. Sai a shekarar 2005, sa’adda na sami damar yi masa wannan wa}a.
Karin wa}ar na same shi ne a wajen wani mawa}i da ya yi wa {ur’ani wa}a a gidan rediyon Nagarta. Shi cewa yake yi a amshinsa
Mu kama karatu
Mui ta riko da zancen Allah
Kur’ani
Ni kuwa sai na ce:
A gai da min kai
Babban malamin salafiyya
Albani
Ga wa}ar:
1. Da sunan Allah Sarki ni nake farawa
Ina ro}on Allah Sarki ya karan baiwa
Cikin wa}en da a yau zan yi wa ]a mai baiwa
Muh’d Auwal Adamu wanda shi aka ce wa
Albani
2. Ina ta salati gun Manzo uba gun Fati
Sa’annan na sanyo a ciki da Alul-baiti
Da su da sahabbai manya ne da sun yi wafati
Akan bin sunnar Manzona da tsantsar aikin
Imani
3. Masoya Sunna yau ku tsaya ku ]an saurara
Ku karka]e kunne zan wa}a ga masu basira
Uban AbdulBarri gwarzon da ya wuce tsara
Ba}iyyatu ahlil-khairi wajen hadisi da sanin
Kur’ani
4. Idan fa ana dara dole uwa akan fid da ta
Wajen ilimi Malam Auwal yana da bajinta
Ina gai da ka ina ta yaba wa wannan gwarzon
[anmasani
5. A fannin ilimin {ur’ani ha]a da Hadisi
{wararre ne shi bai saba wa khairin-nasi
Wurin fatawa in dai har ya tarar da hadisi
Ba zai mai tawili ba a gai da kai ya Malam
Albani
Ina gai da ka
Allah ya tsare ka
Ya kare nufinka
Ya ]aukaka harka
Ba shakka
Kana da nufin kashe sa~ani
6. Sa’annan ya san fannoni na duk tarihi
Da fannonin Larabci duk yanai masu sharhi
Wajen kafa hujja bai hada munkari da sahihi
Wajen fikihu ma ya yi fice da gaske nake ba
Tsammani
7. Ku gai da min Malam masani akan komfuta
Yana da sani kan duk ilimin da yas shafe ta
Ku bar mamaki don nace da ku ya san kowane
Fanni
8. Mutum ne mai baiwa da take da ban mamaki
Masoya Allah sun san ba guluwwi a ciki
Idan nac ce Albani za ya cinye maki
Idan da za ai mai exam wajen maki kuma ai
Tsanani
9. Ba zan ~oye ba Albani yana burge ni
Saboda biyar sunnar Manzonmu dan Adnani
A kanta Muhammadu ke wa’azi yana ta bayani
Sa~ani
10. Yana ta kiran dangi don ]ai su bi magabata
Su daina biyewa jahilci da aikin wauta
Su gyara a}ida kan Sunna su inganta ta
Ya ce wannan hanya ita ce ka]ai a ciki ba
Ru]ani
Ina gai da ka
Allah ya tsare ka
Ya kare nufinka
Ya ]aukaka harka
Ba shakka
Kana da da nufin kashe sa~ani
11. {wararren malam ya yafe wa mai zaginsa
Ya ce ba komai don Allah yake aikinsa
Ya ce da masoya su da wa]nda ke }yamarsa
Dukansu guda ne don yace dukanku Musulmi
Ikhwani
12. A gaida min kai, kai mana maganin‘yan shi’a
Da su da iyayensu manya dake masha’a
Gaba ]aya su da wa]anda suke ta aikin bidi’a
Ka tona asirin tsarinsu da ~arnarsu kai ta
Bayani
13. Wa]anda suke zagin sunna ko ka bi ta kansu
Wajen yin raddi ba ka yin ragi a garesu
Kana kyararsu da tsabagen ba}in aikinsu
Nufinka ya zam tsantsar sunna ta danne aiki
Mai muni
14. Muhammadu Auwal malam ne da bai da mugunta
Wajen koyar da karatu ba ya yi ma }eta
Yana yin dalla-dalla mas’ala ya baje ta
Wajen reference zai baka tuli ka je ka ji }ari
Na bayani
15. A halayenshi Muhammadu babu yanke zumunta
Da]ai ba ya zagi, }arya ko bai }aunar ta
Ka bar shi wurin tallan sunna da kuranta ta
Da bayyana ha}}un ko da ‘yan ]ari}a za sui
Gurnani
Ina gai da ka
Allah ya tsare ka
Ya kare nufinka
Ya ]aukaka harka
Ba shakka
Kana da da nufin kashe sa~ani
16. Ina kake malam wanda ku]i baza su saye ba
Ku daina tayawa don ni na sani ba riba
Ba zai canza ba don ‘yan kyautukanku na zamba
A don haka ne ma bai kar~a, bare wa’azi nai
Yai rauni
17. Ina kake malam ]an baiwa da babu irinka
Wajen iliminka da tsarin rayuwar da ka ]auka
Da gogewa kan harkar rayuwa da nufinka
Na alheri, kullum sunna ta }ara gaba kowane
{arni
18. Ina ro}on Allah Sarki ya }ara haza}a
Da ]umbin ilmi, don da’awa ta zam ta mi}a
Ku zo ku bi sunna ‘yan bidi’a ku daina zala}a
Idan kun bi ta, kun dace da tsarin Allah
Kur’ani
19. Ka je maktab ]in malam don ka sha mamaki
Ka bai wa idonka abinci ya kalli kayan aiki
A nan ne za ka ga littaffi ka bu]e baki
Muhammadu Auwal ya tara su ya tsara fanni-
Fanni
20. Yabon da nake wa malam ni a nan zan huta
Idan an kwana biyu wata}il na ]an maimaita
Ya Rabbi ka kare min malam ka }ara fahimta
Ka sa mu ci amfanin ilmin Muhammadu Auwal
Albani
Ina gai da ka
Allah ya tsare ka
Ya kare nufinka
Ya ]aukaka harka
Ba shakka
Kana da da nufin kashe sa~ani
21. Inai muku bankwana danginmu sai wata rana
Idan kuka tad da Muhammadu sai ku mi}a yabo na
Ku ce masa Asgar ya gaishe shi, nai masa murna
A kan kyan aikin da yake ya]a sunnar Manzo
Adnani
22. Ku ce masa Allah na ro}a ina }arawa
Ya ba shi sawaba har ranar shigar shi kushewa
Ya sa Manzona zai cece shi ranar tsaiwa
Ya zarce Aljanna, Allah ka kare min Sheik
Albani
23. A wannan baitin zana rufe ku ]an ban uzuri
Ina da larura zan tare ya-nawa da sauri
Ku mun ha}uri don wa}ar tawa ba ta da tsari
Saboda }arancin baiwata da tsantsar fikira
Mai rauni
Ina gai da ka
Allah ya tsare ka
Ya kare nufinka
Ya ]aukaka harka
Ba shakka
Kana da da nufin kashe sa~ani
23 ga watan Agusta, 2005
Zariya.
M.Allah ya saka da alkhairi,shikuma da Allah ya dauki kwanansa Allah ya yasa mutuwan shahadah yayi ya kuma albarkaci iyalansa da ya bari da kuma dalibansa
ReplyDeleteAllah Ya Gafartama Malam
ReplyDeleteAllah ya jikan malam da rahma
ReplyDeleteAllah ya karbi shahadar shi
Allah ya haskaka qabarinsa
Allah ya kyautata tamu bayan tashi
Allah SWT ya Saka da alkhairi , ya Kai haske qabarin Malam.
ReplyDelete