Wednesday, April 6, 2011

MAKOMA

MAKOMA[1]

Tun sanda nai wa}ar Tazarce nake son in yi wa }iyama wa}a. Allah bai sa na sami ikon yin hakan ba sai a wannan lokacin.

Na yi amfani da Karin wa}ar baka ne a wa}ar. Asalin karin na ji shi ne a wata wa}a ta ]an uwa Zil}ifilu Muhammad Basir.

Na kawo ta a }arshen wannan kundi nawa ne bisa la’akari da cewa makomarmu itace }iyama. To bisa hakan sai na sanya wa}ar da ke batu a kan wannan makoma a matsayin }arshen kundin. Kamar dai ace ina mai yin arashi ne da ita. Don haka ne ma na kiraye ta da sunan Makoma.

Allah ka sa mu yi }ya}}yawan }arshe ka kuma bam u makoma mai }yau ta ni’ima. Amin.

Ga wa}ar:

1.  Zan wa}e ran }iyama Rabbi Sarki ka }ara ban hikima

2.  In na tuno ta zuciya da dukkan jiki su ]au kyarma

3.   Hantar cikin jikina sai ta motsa kai har da ma nama
 
4.   Kullum ina nadama laifukana da nay yi ko zulma

5.   Lakar jiki ta narke sai ka ce wanda yaf fito fadama

6.   Domin tuno da lokacin da ranar ga za ta sauko ma

7.   Ranar da za a tara duk halitttu rannan akwai fama

8.   Kowa ya zo tsirara babu wanda ya zo da takalma

9.   Matar da ke da juna biyu nan take za ta haife ma

10. [an }an}anin mutum  a lokacin nan zai zama mai girma

11.  Har ma da furfura, kowa tsaye don ko babu tabarma

12.  Kowa ka gan shi ya firgita ya }e}ashe kamar tsumma

13.  Rana tana ta }ara zafafa kuma ba batun lema

14.  Don bainaha wa baina ‘yan adam mil guda take a sama

15.  Ba wane babu mai mu}ami sai Jalla Rabbi mai rahama

16.  Har za ya tambaya ya ce “A yau wai ina mazo girma?”

17.  Ba wanda za ya amsa wanga question kowa yana kyarma

18.  Sai shi da kansa za ya ba da amsa  ya Rabbi mai hikima

19.  Baki ]aya mu amsa babu ya Rabbi dole an bar ma

20.  Dogon wunin ga za a sha wuya ‘yan uwa mu ]au himma

21.  Kowa yana shiru abin da ke faruwa akwai girma

22.  Ceto a lokacin ga ran }iyama shi ne abin nema

23.  Babanmu Adamu, da Nuhu in an ka ce su je su ma

24.  Musa Kalimu har da ]an gidan Maryamu ha]a har ma

25.  Babban bada]iyi gurin Ta’ala ba wata alfarma

26.  Kowa cikin biyar ]in ga ya ce walla yau fa ba dama

27.  Amma ku je ga wane ni da kaina a yau nake fama

28.  Na tafka laifuka, gun Rabbana yau ina bi]ar rahama

29.  {arshe a zo ga ]an Amina manzonmu sai ya ]au azama

30.  Zai je wurin Ilahi ni da kai mu fa za ya ro}o ma

31.  Sau}i da rangwame wurin hisabi, dangi mu ]au himma

32.  Domin mu san shiga cikin shi ceton nabiyyi mai girma

33.  Sannan a ce da shi ya kwashi dubbai cikinmu al’umma

34.  Aljanna za ya kai dukansu sun tsira sun shige ni’ima

35. Allah Ubangiji nake ta ro}o yai mini alfarma

36.  Domin na zam cikin wa]anda Allahu zai yi wa rahama

37.  In tsallake sira]i ni da abbanmu har da ma umma

38.  In sha ruwa a tafkinsa na haura cikin yawan salama

39.  In tsere duk azaba ta wutar Hawiya da Jahannama

40.  Duk wanda ran }iyama a ka }ona shi ba shi ba girma

41.  Ya zam abin kwatanci na asara ya rasa duk }ima

42.  Dangi mu ba da gaskiya da Allah mu daina yin zulma

43.  Sannan mu daina shirka da fasadi da duk abin }yama

44.  In mun tuna da laifuka mu tuba, mu daina yin gulma

45.  Sannan mu dinga bin rasuluna za mu sami alfarma

46.  In mun biye wa zuciya da son ranmu walla ma zarma

47.  Don ran da za a ta da mu nadama ba ta da da ko }ima

48.  Duk masu yin ta za su ]an]ana, za su fa]i ba girma

49.  Ni ko da yaushe tausaya wa kaina nake musamman ma

50.  In na tuna da laifukan da nai  wanda ba su }irgo ma

51.  Allah ka yafe ]an Abubakar Asgari yana nema

52.  Tsira gurin ka kai ka]ai Ta’ala kai ne kake rahama

53.  Ranar da za a auna ayyuka, litattafai a kwaso ma

54.  In ka yi ayyukan kwarai a mi}a a ce ka sa dama

55.  In ayyukan ko sun zamo na banza to sai ka sha fama

56.  Kowa a rarraba a kai musulmai cikin gidan ni’ima

57.  Su ko munafikai da kafirai sai a kai su Jahannama

58.  Ni ko a nan nake nufin na }are batun ga don da ma

59.  [an tsokaci nake nufin na furta gare ku al’umma

60.  Allah ka yafe kuskuren da nai har da inda naz zarma

61.  Nan za na sa ]igo na tashi, }arshen batun da nai salama

07 ga watan Nuwamba, 2007

Zariya

[1] Ita ce wa}ar da nai ishara a can baya a cikin wa}ar Tazarce cewa zan yi wa}a akan lahira 

Three in one

DA{I{AI; YARAN MAKARANTA

A watan Disemba na shekarar 2006 muka je garin Jos da ]aliban makarantar Higher Islam, tafiyar ta ilimi ce, wato excusion a turance. To a hanyar wannan tafiyar ne fikirar yin wannan wa}ar ta zo mini. Dama ina da niyyar na yi wata sabuwar wa}a a kasuwar Ukazan da a lokacin bai wuce saura mako guda ta fara ci ba.

Ina son yin wa}ar amma ba na so na maimaita wani kari ko jigo da na ta ba yin wa}a da shi ko wani ya yi makarantar, musamman saboda ganin cewa na ta~a yi wa makarantar, malamanta, ]alibanta da wasu abubuwa da suka shafe ta wa}a.

Kawai sai abin ya fa]o mini a raina cewa ai kuwa ban ta~a jin wani ya yi wa da}i}ai wa}a ba a makarantar.

Nan take na ji ya kamata in yi musu wa}a! Sai na ]auki al}alami na rubuta wannan wa}a mai zuwa.

Karin wa}ar na aro shi ne daga wata wa}ar hijabi wadda wani mutumin Potiskum ya yi wadda ke da amshi kamar haka:
            
         Ku sanya hijabi ‘yan mata
           Ku daina yawo a gari banza

Ni kuma sai na ce:

           Ku dinga karatu ‘yan yara
           Ku bar gasa bencin makaranta

Wa}ar kwar uku ce. Sannan tana da gajeren amshi a karshen kowane layi shi ne

“makaranta”

Ga wa}ar:

1.   Allahu Sarki kai na kira ban sa}e-sa}e
      Ka ba ni fasaha ya Allah zan rera wa}e
      Na mi}a nasiha gun yara da ke gasa bencin makaranta

2.   Kafin na yi nisa zana tsaya na mi}a salati
      Gun sayyadina Manzo, baba gun su Fati
      Na ha]a ciki da sahabbai nai, da Alul-Baiti managarta

3.    Ina so in yi kira gun yara ‘yan haya ne                                                                                                          
       Wa]anda suke yawa a wajen darasi a zaune
       Suna yin surutu a aji, suna gasa bencin makaranta

4.    Sune suke yin wasa ba sa son karatu
       Ba sa fahimta ba su da kai, hala ma su zautu
       Allah ka shirye su ya Rabbi ka ]aukaka su a makaranta

5.    Ya ku da}i}ai na yi kira ku amsan kirana   
          Na san kuna jin haushi na, kuma ba ku so na
        Amma ku gane cewa wa}an nan nasiha manufata

6.    Fata nake yi za ku tsaya, kuma za ku lura    
   Ku gane abin da ya kawo ku ya zarce fira
   Iyayenku su turo ku domin ku zamto managarta

7.     Amma a yanzun kun manta kun kama shirme
   Ba kwa da aiki in bayan ]abi’ar kurume
   Shine yawan gulma, satar amsa da fashin makaranta

8.     To ga nasiha zan jero ku tsaya ku kar~a
        In na fa]i ku rike ta duka, kuma ban da za~a
        Sannan ku aikata tsarina, ku ma a san ku a makaranta

9.     Farko ku sa niyya ta-gari kan ayyukanku
        Sannan du’a’i kar ku gaza ba mai hana ku
        Ro}on Shi Allah Sarkin nan da shi ]ai za a yi wa bauta

10.   Sannan idan aka zo a aji kada kui ta wauta
        Kada kui ta surutu a aji, ko jita-jita
        Ku dinga zama, yawon banza ku bar kawo shi a makaranta

11.   Nazarin karatunku a gida kar kui ta zaune
        Kar kui ta fira ba ma’ana, aikin kawai ne
        Hakanan sana’ar kallon fim, ba za tai kyau ba ga ‘yan mata

12.   Idan aka zo jarabawa yara ban da le}e
        Koko ki dauko ‘yar paper ki shigo a sa}e
        [abi’a ce wannan mara kyau, ku bar kawo ta a makaranta

13.   Nasihohin da na yo Allah sa an ji sosai
        Sannan ya zamto kun gane su, don yanzu ba sai
        Na zo ina maimaitawa, a nan gaba loton makaranta

14.   Ya Rabbi kai nar ro}a yau bayinka ga su
        [a}i}an da suke a Higher bu]e kawunansu
        Wa]anda suke da basira ko ka }ara yawan su a makaranta

15.  Ya Rabbi ka sa musu imani a zuci dukansu
        Sannan ka sa su a turbar sunnar annabinsu
        Muhammadu angon Aisha, baba gun Rukayyatu [angata

16.    Duk addu’oin da na yi Allah ka kar~a
         Kai dai ya dace in ro}a, kai za kar~a
         Sarkin sarauta ya Allah ka ]aukaka wannan makaranta

17.    Wa}ar ga nan zan huta na kawo ta }arshe
         Kun ji ta na koro tsarinta kamar adashe
         Sunanta kun ji shi a farko, da}i}ai yaran makaranta

18.    Sunan mawa}in Asgar ba ba}o ba ne ba
         A wurin Ukazar Higher ba sabo ba ne ba
         Na saba yin wannan harka tun ba a yau ba a makaranta

19.    Nai sallama na gaishe ku, kuma na yi ro}o
         Ku yafe min in kun yi fushi , na zo da }o}o
         Na neman afuwa gun yaran da ke gasa bencin makaranta

21 ga watan Disemba, 2006

Jos

MARABA DA UKAZA

A kasuwar Ukazan da ta ci a Disembar shekarar 2006 ne muka yi wannan wa}ar ni da wani abokina mai suna Malam Yusuf Abdullahi Imtihani. Malami ne mai koyar da darussan Larabci kuma }wararren marubucin da ke da wa}o}i barkatai.

A sanda muke yin wa}ar muna yin ta ne kawai da ka. Abin nufi shi ne ba mu rubuta ta ba, sa~anin yadda muka saba yin wa}o}inmu. Kuma muna rera ta ne ta hanyar musaffar ]angwayenta, wa]anda dama layuka ne ]ai-]ai. Wato wannan ya fa]i layi ]aya a ba da amshi sai ]ayan ma ya fa]i layi ]aya a ba da amshi. Sai daga baya muka ga dacewar mu rubuta ta.

Wa}ar ba ta da kari sai na wa}ar baka, kuma mun yi ta ne kawai dama don nisha]antarwa da }ara wa dandalin armashi

Amshin da ake yi bayan kowane ]ango shine

          Ukaza 2006

Ga wa}ar nan:

1.          Bisimillahi ina farawa
2.          Nai sallama ku zam amsawa
3.          Ni yau Ukaza zan wa}ewa
4.          Ya Rabbana ka }aro baiwa
5.           Mui baituka su zam gamsarwa
6.           Wasu tambaya suke jefawa
7.           Wai me Ukaza ke koyarwa
8.           Amsarku ga ta ba wahalarwa
9.           Ku biyo ni don ku zam ganewa
10.        Ilimi Ukaza ke koyarwa
11.        Kana sa}afa mai gamsarwa
12.        Udaba’u na ta nuna }warewa
13.         Khudaba’u na ta nuna iyawa
14.         Shu’ara’u na ta nuna gwanewa
15.          In ka iya ka nuna }warewa
16.          In ba ka yi ka bar kushewa
17.          Harkar Ukaza ba fasawa
18.          Don ]alibai suna cashewa
19.           Har malamai suna rerawa
20.           Alkalanmu ma suna ]anawa
21.           AbdulBasir yana da iyawa
22.           Kowaf fa]a yana }arawa
23.           Baiwarshi ta ]ara wa tawa
24.            Malam Aliyu mai rannawa
25.            Mun gan shi ai yana tsarawa
26.            Malam Nasiru mai saitawa
27.            Amma huluna yake saitawa
28.            Malam Muniru na rerawa
29.            Baban Ukaza ban mantawa
30.          Na ga Principal yana tsarawa
31.          Wata rana ma yana rerawa
32.           Har kyautuka yake bayarwa
33.           Gun ba ka har kuna gaisawa
34.           Har addu’a yake }arawa
35.            Ai azama }warai a bar kasawa
36.             Jaddul Ukaza ban mantawa
37.             AbdulBasiru babbar giwa
38.            Duk shekara yana tsarawa
39.             Kai na ga ma yana rerawa
40.            Malam Kabiru bai tsarawa
41.            Amma da shi a ke tacewa
42.            Malam Bizara wayyo nawa
43.            Shi ma yakan kwatanta iyawa
44.             Malam Salisu birni nawa
45.             Ko yaushe ni kake birgewa
46.  Har ]alibai suna shedawa
47.        Sheshi Ummaru dawo nawa
48.        Gemunka ya fi }arfin nawa
49.        Amma fa mai yake shafawa!
50.        Malam Rabi’u Uncle nawa
51.        Kayan wuta yake jonawa
52.        Ya Rabbana ya zam sakawa
53.        Barister Lawal ina kake nawa
54.         Na so a ce kana rerawa
55.         Malam Bala yana da }warewa
56.         Samaruddani ya kake nawa
57.         Da na san da kai ake cashewa
58.         Yaya yanzu sai kake no}ewa?
59.         Angon Fatima kar ka yi yawa
60.         Malam Nura mai gida ne nawa
61.         A gidan ka ba a kukan yunwa
62.         Ya ayyuka? Muna godewa
63.         Malam Yusufu wayyo nawa
64.        In kai kira ina amsawa
65.        Nan zan tsaya ina hutawa
66.        Ai ka da]e kana rerewa
67.        Kowa yag gaji sai hutawa
68.        Sai wata rana ko muna }arawa
69.         Ku ]alibai ina ta yabawa
70.         Har malamai ina sanyawa
71.         Ma’assalam nake ma cewa
26 ga watan Disemba 2006.
            Zariya

TA’AZIYYAR KHADIJA

Khadija Lawal wata ]aliba ce a makarantar Higher Islam, Allah ya yi mata rasuwa a cikin shekarar 2005.

Kafin rasuwarta wadda ta faru ta hanyar haihuwarta ta farko, ta kasance ]aya daga cikin shahararrun ]alibai ba a kasuwar Ukaza kawai ba, kusan in ce a makarantar baki ]aya.

Lokacin da na sami labarin mutuwarta na girgiza kwarai. Daga baya na ga dacewar na yi mata wa}ar ta’aziyya da fatan Allah ya ji kanta

Karin wa}ar ]aya ne da na wa}ar Gaisuwa ga Albani. Sai dai amshin  wannan shi ne
           
Allah ka ji kan ta Khadija Lawal
            Da tai mana wa}en Kur’ani

Na za~i karin ne bisa la’akari da cewa wa}arta ta }arshe da ta yi a dandalin Ukaza ta yi ta ne da irin wannan karin kuma ta yi ne tana yabon Al-Kur’ani mai gurma.

Shi kuwa }aramin amshin wanda ya ka zo a }arshen kowane layi shi ne  

Rahmani

Ga wa}ar nan:

1.    Da sunan Sarki wanda ya }era dukka halitta
       Nake farawa ya Allah ka sa ta huta
       Khadija Lawal yarinyan nan da tai mana wa}en Kur’ani

2.    Kafin na yi nisa za na tsaya na mi}a salati
  Gurin Manzona, sannan har da Alul-baiti
  Da su da Sahabbai sun yi ri}o ga sunnar Manzo Adnani

3.   Wa}en dana ke yi yau ]in nan akwai alhini
  Akwai juyayi mun yi rashi muna ta tunani
  Allah ka saka ta a Aljanna Khadija Lawal don Kur’ani

4.   Mutanen Higher ku duka yau inai muku jaje
        Allahu ya sanya kun jure, hali na mazaje
      Ku dinga du’a’i gun Allah ya sa ta a ceton Kur’ani
5.    Ina tuna Dije da wa}enta akan Kur’ani
       A bara da tai ta a nan a Ukaza ta birge ni
       Allah ka cika mata ladanta, ka sa mu mu jure alhini

6.    Ina miki fata Dije ya zam ki sami shahada
       Domin ko akwai a cikin jerangiya ta shahada
       Irin mutuwarki don angon Safiyyatu ne yay yi bayani 

7.    {awayen Dije da danginta ku zam ha}urewa
       Ku dinga du’a’i, har kullum ku daina gazawa
       Ku bar yin kuka, don kuka a gun mamaci bai amfani
  
8.    Allah ya fa]a a cikin Kur’ani kar fa mu manta
       Dukannin mai rai zai fa mace ku bar yin wauta
       Wannan magana sam ba }arya akwai ta cikin Al-Kur’ani

9.    Allahu mu ke ro}o domin ya ba ta sabati
       Ta amsa jawabin mala’iku ta sami najati
       Ta ba da bayani dukkan tambayar da su kan yi malakani

10.  Tabaraka ya Allah Sarkin da shi ya yi kowa
       Ka gafarta wa musulminmu dake a kushewa
       Idan mun zo mutuwa, mu ko ka sa mu cika fa da imani

11.  Ba za na tsawaita gun wa}en ba nan zan huta
       A nan zan kwana bayan ]an abin da na furta
       Ni dai manufata ta sami shahada gun mai aiken Kur’ani
                 
23 ga watan Satumba, 2006

Zariya