TURA TA KAI BANGO
Wa}a ce da ke da ma’aunin Larabci mai karin
Faa-i-laa-tun Faa-i-laa-tun
Wato karin da a ke ce wa Ramlu a larabce.
Na yi ta ne a kan soyayyarmu da Zainab M. Tukur da na ba da labari a baya. Lokacin da na ga cewa mutanen da suka shiga tsakanin soyayyarmu da tsakanin cin nasararmu sun tsaya tsayin daka don ganin cewa sun kawo }arshen dangantakarmu ko ta halin }a}a.
Ga wa}ar:
1. Asgari zai rera wa}a
Rabbi }ara min haza}a
Baitukan su yi kyau ya sa}a
In gama ban karare ba
2. Nai salati gun Rasulu
Amadi shi ne Khalilu
Gun Ilahi Zul Jalalu
Ban ga gwarzo ni ya kai ba
3. Alu baiti ina yabon ku
Ku sahabbai na sako ku
Masu ]akin Mahi har ku
Ni ba zan ware guda ba
4. Yau }asidar ba nisha]i
Baitukan sam babu da]i
Yau tsaya ki ji wanga ta]i
Abu ba zan ba da ke ba
5. Rayuwata ta yi }unci
Na nutse a cikin ka]aici
Ba ni ko da cin abinci
Lafiya ba dai garan ba
6. Ko da yaushe ina tunani
Ko ka ji ni ina bayani
Sai ka ce wani mai jununi!
Ba jununin ko garan ba
7. Sai bala’in so da }auna
Ni da Abu muke wa juna
‘Yar da yanzu tana Kaduna
Abu ba yau za ta zo ba
8. {ila ma ta wuce Abuja
Kai batun nan babu ko ja
In ta je ta garin Abuja
Ta yi nisa ba ka]an ba
9. Abu ‘ya ce mai mutunci
Ta kasance mai karamci
Yanzu ta fa]a ka]aici
Don ba ta gana da ni ba
10. Tun da dai kin }aunace ni
Ba ki son aibi gare ni
Abu ni kin tallafe ni
Ni ba zan manta da ke ba
11. Ni ha}i}a kin biya ni
Kin ka killace so gare ni
Shi ya sanya kin ka gan ni
Ban ha]a ki da kishiya ba
12. Duk wuya kin sha a kai na
Har bala’i har da }una
Kin ka nunan so da }auna
Ba ki yaudari zuciya ba
13. Zan ri}e ki bisa amana
Rabbi }aro so da }auna
Har ya zam mun auri juna
Ba mu zam mun tarwatse ba
14. Hassada da yawan mugunta
‘Yan uwa ku bari da }eta
{addarar Allah ku bar ta
Ba ku ce wai za ku ja ba
15. Kun ka tsangwani ‘yar uwarku
Kun hana ta zama cikinku
Don tana so na, ganin ku
“Wai ba zai dace da ke ba”
16. Annabinmu ko ya hane ku
Kun sani, kun kau da kanku
Ba da hujja ko guda ba
17. Ni yabo na gun Ilahi
Don a}idata falahi
Ban da shi Allah Ilahi
Ban fa yarje ma wani ba
18. }addara Allah ka yin ta
Rabbi mai tsarin bajinta
Mai cikar }udurar sarauta
Bai yi tsara ko guda ba
19. To idan shi yan nufata
Za na zam fa miji gare ta
Walla dole ku ban hanunta
Ku ba za ku iya da ni ba
20. In ko Allah bai nufa ba
Bai zamo ya }addara ba
Sam ba zan aure da ke ba
Ko ba kui lura a kai ba
21. Na sani in har na samu
Rabbi ne ya nufa na samu
Sanda duk na rasa Alimu
Shi ya tsara ba da wai ba
22. Dan Adam sarki na rauni
Bai da }arfi don ya ba ni
Ni da ku sam babu raini
Da a ce ba ku tsangwaman ba
23. Ko ya ce wai zai hana ni
Wagga }arya ce ta raini
Rabbi dai shi za ya ba ni
Ba da sa hannun mutum ba
24. Ni da ku mu zuba mu je mu
Kar ku fasa nufinku har mu
Rabbi Allah agaje mu
Ba ka bar mu da ‘yan uba ba!
25. Kan kwa]ai kun kau da kanku
Kun rufe ijiya da jin ku
Za ku fa]a ku a teku
Can cikinta ba za ku sha ba
26. Wai a samo masu harka
Alhazai manya na Makka
Mai zuwa safara Amurka
Ba student wai ya ni ba
27. Wai batunku a sami dokta
Mai yawan naira ku ba ta
Wanda zai tsotse jininta
Ba da alfarma ta so ba
28. Ko a ce manaja na banki
Ko sarakai masu doki
Masu ji da isa da mulki
Inda sam ba a san wuya ba
29. Arziki Allah ka yin shi
Har talauci kishiyar shi
Babu wanda ka yi da kan shi
Rabbi bai ga sa’a da]ai ba
30. Ba yabon kaina nake ba
Kun ga ni ba jahili ba
Ba kamar wanen ku ne ba!
Ba da}i}i ne fa ni ba
31. [alibi ne mai haza}a
Mai cikar ladabi a hal}a
Kar ku nuna min zala}a
Don ko walla ba za ku sha ba
32. Don akwai future gare ni
Mai alamar kece raini
Don akwai baiwa gare ni
Ba kucaki zan zamo ba
33. Kai ku koma hankulanku
Don ku daina zubar da kanku
Sai ku }yale ‘yar uwarku
Ba ku zam ‘yan tsangwama ba
34. Sai ku tuba gurin Ilahi
Don ku zam samun falahi
Rabbi shi yay yo subahi
In ka }i shi ba za ka sha ba
35. Zuciyata ta yi }una
Yau tsaya ka ji martinina
Kun ci bashi walla guna
Sam ba zai da]in biya ba
36. [an halas ku ka wa fitsara
Kar ku ]auka za ku dara
Don ko fansa za na tsara
Ni ba zan yafe da]ai ba
37. Basuka na kun ka ]auka
Ran biya ai za ku koka
Ran da fansa za na ]auka
Ba da tausai za na zo ba
38. Ramuwa ai ta fi gayya
An wuce zamani na kunya
Ba kawaici babu sanya
Ni ba zan sake nufi ba
39. Wanga aiki ya ishe ni
Babu sauran }yale raini
Ba ]agu na kafa gare ni
Martani ba za ya kau ba
40. Rabbana Sarki Alimu
Mu gare ka muke batunmu
Addu’ar da muke ka ba mu
Khairi, karami da babba
41. Laifuka Allah ka yafe
Tun na da, har yau da safe
Har na nan gaba duk ka yafe
Babu mai haka ban da kai ba
42. Dukanin khairi ka ba mu
Hassada, Allah tsare mu
Har da makirci da jurmu
Ba mu zam mun karkace ba
43. Nan nake so za na huta
Wagga ‘yar wa}a da nai ta
Tuntuni ne kar ku manta
Kar ku ce ai ban fa]a ba
44. Sallama naka yi gare ku
Sai ku amsa ban da tsurku
Bai da amfani gare ku
Ko da dai ba ku san hakan ba
27 ga watan Yuliya, 2002.
Zariya
Allah Ya kare mana Malam
ReplyDelete