MAKOMA[1]
Tun sanda nai wa}ar Tazarce nake son in yi wa }iyama wa}a. Allah bai sa na sami ikon yin hakan ba sai a wannan lokacin.
Na yi amfani da Karin wa}ar baka ne a wa}ar. Asalin karin na ji shi ne a wata wa}a ta ]an uwa Zil}ifilu Muhammad Basir.
Na kawo ta a }arshen wannan kundi nawa ne bisa la’akari da cewa makomarmu itace }iyama. To bisa hakan sai na sanya wa}ar da ke batu a kan wannan makoma a matsayin }arshen kundin. Kamar dai ace ina mai yin arashi ne da ita. Don haka ne ma na kiraye ta da sunan Makoma.
Allah ka sa mu yi }ya}}yawan }arshe ka kuma bam u makoma mai }yau ta ni’ima. Amin.
Ga wa}ar:
1. Zan wa}e ran }iyama Rabbi Sarki ka }ara ban hikima
2. In na tuno ta zuciya da dukkan jiki su ]au kyarma
3. Hantar cikin jikina sai ta motsa kai har da ma nama
4. Kullum ina nadama laifukana da nay yi ko zulma
5. Lakar jiki ta narke sai ka ce wanda yaf fito fadama
6. Domin tuno da lokacin da ranar ga za ta sauko ma
7. Ranar da za a tara duk halitttu rannan akwai fama
8. Kowa ya zo tsirara babu wanda ya zo da takalma
9. Matar da ke da juna biyu nan take za ta haife ma
10. [an }an}anin mutum a lokacin nan zai zama mai girma
11. Har ma da furfura, kowa tsaye don ko babu tabarma
12. Kowa ka gan shi ya firgita ya }e}ashe kamar tsumma
13. Rana tana ta }ara zafafa kuma ba batun lema
14. Don bainaha wa baina ‘yan adam mil guda take a sama
15. Ba wane babu mai mu}ami sai Jalla Rabbi mai rahama
16. Har za ya tambaya ya ce “A yau wai ina mazo girma?”
17. Ba wanda za ya amsa wanga question kowa yana kyarma
18. Sai shi da kansa za ya ba da amsa ya Rabbi mai hikima
19. Baki ]aya mu amsa babu ya Rabbi dole an bar ma
20. Dogon wunin ga za a sha wuya ‘yan uwa mu ]au himma
21. Kowa yana shiru abin da ke faruwa akwai girma
22. Ceto a lokacin ga ran }iyama shi ne abin nema
23. Babanmu Adamu, da Nuhu in an ka ce su je su ma
24. Musa Kalimu har da ]an gidan Maryamu ha]a har ma
25. Babban bada]iyi gurin Ta’ala ba wata alfarma
26. Kowa cikin biyar ]in ga ya ce walla yau fa ba dama
27. Amma ku je ga wane ni da kaina a yau nake fama
28. Na tafka laifuka, gun Rabbana yau ina bi]ar rahama
29. {arshe a zo ga ]an Amina manzonmu sai ya ]au azama
30. Zai je wurin Ilahi ni da kai mu fa za ya ro}o ma
31. Sau}i da rangwame wurin hisabi, dangi mu ]au himma
32. Domin mu san shiga cikin shi ceton nabiyyi mai girma
33. Sannan a ce da shi ya kwashi dubbai cikinmu al’umma
34. Aljanna za ya kai dukansu sun tsira sun shige ni’ima
35. Allah Ubangiji nake ta ro}o yai mini alfarma
36. Domin na zam cikin wa]anda Allahu zai yi wa rahama
37. In tsallake sira]i ni da abbanmu har da ma umma
38. In sha ruwa a tafkinsa na haura cikin yawan salama
39. In tsere duk azaba ta wutar Hawiya da Jahannama
40. Duk wanda ran }iyama a ka }ona shi ba shi ba girma
41. Ya zam abin kwatanci na asara ya rasa duk }ima
42. Dangi mu ba da gaskiya da Allah mu daina yin zulma
43. Sannan mu daina shirka da fasadi da duk abin }yama
44. In mun tuna da laifuka mu tuba, mu daina yin gulma
45. Sannan mu dinga bin rasuluna za mu sami alfarma
46. In mun biye wa zuciya da son ranmu walla ma zarma
47. Don ran da za a ta da mu nadama ba ta da da ko }ima
48. Duk masu yin ta za su ]an]ana, za su fa]i ba girma
49. Ni ko da yaushe tausaya wa kaina nake musamman ma
50. In na tuna da laifukan da nai wanda ba su }irgo ma
51. Allah ka yafe ]an Abubakar Asgari yana nema
52. Tsira gurin ka kai ka]ai Ta’ala kai ne kake rahama
53. Ranar da za a auna ayyuka, litattafai a kwaso ma
54. In ka yi ayyukan kwarai a mi}a a ce ka sa dama
55. In ayyukan ko sun zamo na banza to sai ka sha fama
56. Kowa a rarraba a kai musulmai cikin gidan ni’ima
57. Su ko munafikai da kafirai sai a kai su Jahannama
58. Ni ko a nan nake nufin na }are batun ga don da ma
59. [an tsokaci nake nufin na furta gare ku al’umma
60. Allah ka yafe kuskuren da nai har da inda naz zarma
61. Nan za na sa ]igo na tashi, }arshen batun da nai salama
07 ga watan Nuwamba, 2007
Zariya
No comments:
Post a Comment