Saturday, March 19, 2011

INA MAFITA?

INA MAFITA?

Wannan wata wa}a ce da na yi ta bisa lura da halin da rayuwar mutanen }asarmu ta shiga na matsalolin tarbiyya, tattali, siyasa, ilimi, addini da sauran bangarorin rayuwa.

Na tsakuro sunan ne daga cikin wa}ar. A matsayin tambaya wadda na so in amsa. Sannan na amsa tambayar da amsar da nake ganin ita ce mafita daga matsalolin da na ambata a cikin wa}ar

Wa}ar }war uku ce. Karinta na baka ne. Na same shi ne daga wa}ar ]an uwa Malam Yusuf Imtani; Daga wata shahararriyar wa}ar shi mai taken “Imtihani”. Wadda daga gareta ne ma ya sami wannan la}abi na shi na Imtihani

Ga wa}ar:

1.    Yabo nake ga Allah Sarki Ubangijina
       Ina ta yin salati da yabo ga Annabina
       Rasuluna Khalilul Lah ]a wajen Amina



2.    Bayan salati da yabo da sallamawa
       Wa}en da zan ku tsaya kar ku dinga shewa
       Don batun na zafi ne babu da]a]awa

3.    {asarmu ta shige matsala ta dulmiya
       Babu ci babu sha sai shan wuya
       Malamanmu ba sa }aunar gaskiya

4.    Yau kusan a ce fatara ta zamo uba
       Ko na ce uwa ce kuma la marhaba
       Ba ruwa cikin pampo sam bai zuba

5.    ’Yan fashi suna yayin cin kasuwa
       {auyuka da birni a gida ko dawa
       Ba su tausayi kuma ba sa }yale kowa

6.    Yanke kai da satar yara }an}ana
       {ungiya ta ‘yan tsafi yau ko ina
       Sun shigo kamar fa]owar damina

7.    Masu shugabanci yau ba gaskiya
       Ba su kare ha}}i yau ba gaskiya
       Ko da yaushe sai dai kwasar dukiya


8.    Yau wuta ta lantarki ba ta samuwa
       Sai wata idan ya doso }arikewa
       Sai su ba ka bill na ku]a]e mai yawa

9.    Laifukan zina, sata, har da ma luwa]i
       Su ake ta yayi har ma ana nisha]i
       Duniyarmu ta canza sam babu da]i

10.  Cin riba da ha’inci har tauye mudu
       Shi ko ci na hanci bi nai a yau ake da gudu
       Nau’uka na shai]anci har ma da ]an daudu

11.  Mata tsirara sannan ba su jin kunya
       Kullum akan addini ka ji jayayya
       Manya da jahilci yara ko sai kafiya

12.  Yau fina-finan shaidanci sun yawaita
       Su suke ta kawo tangar]a ga ‘yan mata
       Sun ~ata tarbiyya sun rarake ta

13.  Ba a tsai da sallah yau ba a nasiha
       Kullum abin masarufi ba ya arha
       Kullum gidan mutuwa sai ka ji nauha


14.  Kullum farashin fetir za a }ara
       Ba a taimakon dangi sai dai asara
       {wazon mutune yau sai dai gun bi]ar naira

15.  Magani cikin clinic sai dai a tarihi
       Kan batun ga don Allah wa ke bi]ar sharhi
       Sai ya tambaya ya jiya in bai da tarihi
  
16.  In kana da ciwo yau babu magani
       Ba likita, sai dai a sa ma jini
       Wanda bai da gata yau shine cikin tsanani

17.  Masu arziki ba sa jin tausayi
       Capitalism shi ake so a yi
       Ayyuka na fajirci sun dabaibayi

18.  Ga fari wanda ke ta da hankali
       Nomanmu ba riba sai jangali
       Ba ku]in sayen taki ba na burtali

19.  Shaye-shaye ya yi yawa yau ko ina
       Za ka tad da ‘yan }waya ko ‘yan zina
       Ko ka tad da an kashe bayin Rabbana


20.  Yau ku]in school fees duk an tsawwala
       Yau talaka babu yadda zai walwala
       Su ko shugabanni ba sa ko kula

21.  Ga ma’aikata ba albashi na kirki
       Shi ko student kullum a kwashe maki
       Kai kusan a ce yau kowa bai da kirki

22.  Yau ilimi ya yi }asa ya tarwatse
       Komai a yanzu tunin ya gwamutse
       Babu malamai masana sai ‘yan gatse

23.  Yau a ~angaren tarbiyya mun bani
       Sai idan ana gulma kowa gwani
       Kullum bala’in }arshen zamani

24.  Ba nufi na alheri sai dai tsiya
       Yau majoritinmu ba sa gaskiya
       Gaba tsakanin juna ko }iyayya

25.  Yaudara da 419 ma sun yawaita
       Masu cin amana sune ke bajinta
       Mas’alarmu ta yi yawa sai dai batun mafita


26.  Ai problems ba sa lissafuwa
       Komai yana negative bai gyaruwa
       Daminarmu ba ta kyau don ba ruwa
 
27.  Sai dai mu ce Allah ya Rabbi ya Ba}i
       Sa mu gama lafiya, Allah da]o sau}i
       Dole ne mu dinga du’a’i don bidar sau}i

28.  Mu muna cikin matsala to wai ina mafita?
       Ko hakan ga za mu kasance ba bi]ar mafita
       Lallai ba zai yiwu ba, lallai a san mafita

29.  Sai mu kama addinin Allah mu bar bidi’a
       Sannan jihadi, bin sunna da yin ]a’a
       Dole ne mu tuba, sai mun daina masha’a

30.  Dole ne mu tashi tsaye gun gyara tarbiyya
       Kan gyara yara mata dole ne mu tsaya
       Lallai akwai aiki, sam babu ja baya

31.  Dole ne ]abi’un kirki zamu kakkama
       Duk abin da za mui dangi sai mu bar tsama
       Allahu Sarki Shi ]ai zamu bauta ma


32.  Kowa ya je ya tunato don ya san mafita
       Wanda duk yake da nufin gyara ya san mafita
       Sai an bi dokar Allah za a sam mafita

33.  Sai an jima dangi ma’assalam na fa]i
       Wa}en da nai yau ]in nan babu ko da]i
       Don tai kama da miya ce wacce ba maha]i

34.  Allah ya sa mu gama lafiya da imani
       Gun shi mu muke ro}on gyara da tsantsaini
       Sarkin da shi ya ka sa sau}i akan tsanani

35.  Ya Rabbi Sarki Allah kai na ke ta kira
        Allah ka sa mu gama lafiya cikin nasara
        Ranar hisabi mu shige can gidan nasara

10 ga watan Disemba, 2004.

Zariya.