Sunday, December 26, 2010

SAI WATA RANA

SAI WATA RANA

A shekarar karatu ta 2003/04 na rike aji shida na babbar sakandaren koyar da ilimin Larabci da Addinin Musulunci ta Abubakar Gumi da ke Zariya bangaren mata a matsayin baban aji.

Bisa al’adar makarantar akwai bikin yayen ]alibai da ake yi wa masu fita a }arshen kowace shekarar karatu bayan kamamla jarabawar }arshe, duk wanda aka bai wa baban irin wannan ajin dole ne ya yi ruwa ya yi tsaki don ganin cewa bikin ‘ya’yan nashi ya yi armashi.

Akan gudanar da abubuwa iri-iri a wajen bikin na wuni ]aya, kama daga kan jawabai, wasannin kwaikwayo, lacca ko wa’azi, walima da dai sauransu.

To shi ne ni kuma na rubuta wannan wa}ar a daren ranar da za a yi bikin na ba ]aya daga cikin ]alibai masu fita ]in, sunanta Hajara AbdurRahman Muhammad ta rera wa}ar a filin wannan taro, abin da ya jawo da dama daga cikin ]aliban suka bar dandalin taron suna share hawaye.

Wa}ar kwar biyu ce. Na kuma yi ta ne da wani karin Larabci wanda ake ce da shi Hazaj.

A sha karatu lafiya


1.   Inai muku sallama dangi
      Ku amsa min ma}ala ta

2.   In mi}a yabo ga manyana
      Iyayena mafifita

3.   Wa]anda su kai ta koya min
      Karatu har zuwa na fita

4.   Iyayena a gaishe ku
      A aikin naku ba wauta

5.   Dukan wahala fa sun jure
      Wajen koyar da makaranta

6.   Kuna koyar da ‘ya’yanku
      Dukan fanni su ilmanta

7.   Kuna ha}uri da shirmenmu
      Da duk aiki na mai wauta

8.   Kuna “Allah ya shirye mu”
      Kuna adu’a da yin kyauta


9.   Ha}i}a kun jihadin ku
      Ilahi ya sa ku nanata     

10. Ya sa ku cika da imani
      Ya sa ku cikin ma’azzurta

11. Ya ]aukaka martabarku duka
      Ya sa ku zamo mafifita

12.  Ina ro}on iyayena
       Ku yafe kure da ma wauta

13.  Da ni da dukan sa’o’ina
       Aji shida wanda za su fita

14.  A ban kwanan da za na muku
       Hawayena suna ta fita. 

15.  Saboda ina ta alhini
       A kan rabuwar da ba mafita

16.  Ina kuke ‘yan uwa na aji
       Kiranku nake da muryata


17.  Ina so ne ku yafe ni
       Ku rangwanta ma heart ]i ta

18.  Mu yayyafe wa junanmu
       Mu ]au hali na manyanta

19.  Ku san cewa a yau ]in nan
       Batun rabuwar mu ba mafita

20.  Hala ha]uwa ta ]an yi wuya
       Da }yar ne ma ta maimaita

21.  A gai da Principal baba
       Nasiha mun ji da]inta

22.  A gai da Munir yana son mu
       Yana aiki na jarumta

23.  Da shi da Kabir Mahaifinmu
       Da Uncle R. da Barista

24.  Abu Jummai a gaishe ka
       Sa’annan har da Hedmasta


25.  Da Malam Salisun Higher
       Da duk sauran mahallarta

26.  Aliyu Rufai gaishe ka
       Da sauran masu yin bauta

27.  Na safe da malaman yamma
       [iyarku tana ta zancenta

28.  Hakan nan ‘yan uwa dangi
       [iyan Higher ta ‘yan mata

29.  Ina cewa da ku bye-bye
       Da alheri nake fata

30.  Kuren da na yi ku yafe ni
       Ku ]an daure ku gafarta

31.  A wanye lafiya dangi
       Cikin aiki na jarunta

32.  Salamu alaikumu na fa]a
       Ku amsa don na ]an huta


33.  Ma-faa-ii-lun Ma-faa-ii-lun
       A nan zan }are wa}ata.

13 ga watan July, 2004.

 Zariya











                                      

Saturday, December 25, 2010

TSULIYAR DODO

tsuliyar dodo

Malam Ja’afar Mahmud Adam[1] da ke Kano shahararren malami ne, masanin Al}ur’ani da Sunnah. Ya }ware wajen wa’azin Sunna, tafsirin Al}ur’ani mai girma da maida martani ga a}idojin ‘yan bidi’a da shubuhohinsu.

Wannan irin salo na wa’azi da karantarwa irin na magabata ya jawo mishi shahara da farin jini a wajen masoya Sunna. A ]ayan ~angaren kuma ya jawo masa ba}in jini a wajen }ungiyoyi na ‘yan bidi’a tun daga kan ‘yan ]ari}u da ‘yan shi’a da dai sauran mabiyan wasu hanyoyi da suka sa~a wa Sunna.

Wannan ya jawo wata }ungiyar mawa}an mandiri a Kano wadda ke kiran kanta da sunan Ussha}un Nabiy suka yi wa}a suka zambace shi a ciki ta hanyar zage-zage da yi masa sharri iri-iri. Ba don komai ba sai don ya }ure malamansu, ya wargaza kayan tiredar damfararsu.

Wannan wa}a da suka yi sun yi ~atanci }warai a cikinta, da na saurare ta a kaset hankalina ya tashi, sai na ce da wani abokina mai suna Muhammad Nura Yahya ya kamata a mayar musu da martani.

To shi ne fa muka zauna muka sake sauraron kaset ]in daga nan muka du}ufa wajen mai da martani akan abubuwan da suka farfa]a.

Mun yi amfani da karin wa}ar da suka yi amfani da shi, wanda asalin sa karin wa}a ne da wasu masu mawa}an siyasa suka yi amfani da shi can wani lokaci da da]ewa, tun lokacin jamhuriya ta biyu.

Wa}ar tana da layi biyar-biyar da amshi. A nasu amshin cewa suke yi

Jafaru mun gane nufinka
Ba gina addini kake ba   





Mu kuma sai muka ce

            {arya ‘yan Ussha}u ke yi
            Jafaru ba bidi’a ya ke ba

Ga wa}ar:

1.         Ya Allah sarkin iyawa
Mai kyauta mai kyautatawa
Kai ke rayawa, kashewa
Bayarwa hakanan hanawa
Allah ba tamkar mutum ba

2.         Allah kai ]ai ni nake ro-
}o, ka da]o Allah ka }aro
Min hikima baiwa na tsaro
Wa}e ba shakka da tsoro
Kan Ussha}awa na zamba

3          ’Yan ussha}u ku daina }wange
Kun wa}a kun zage-zage
Mu kuwa damtse za mu zage
Kan muku raddi za mu dage
Ba kuma tare da karkata ba

4.         ’Yan ussha}u kuna da wauta
Har kun kai matu}a a kanta
Kun taba Jafaru za ku sha ta
Ba}ar Magana, don mun iya ta
Amma ba sharri muke ba

5.         Malam Jafaru kun ka sara
Kun mai sharri har fitsara
Ga kuma }arya kun sharara
Kun saki layi kun asara
Ku ba ‘yan kirki ba ne ba


6.         Kun tono dubura ta dodo
Kun yi tsirara babu wando
Sharri da man kun yi gado
Gun Fir’auna da masu dodo
Ba kuma bin Sunna kuke ba

7.         Jarafu malam ne fa babba
Ba ku da tsara gun shi duba
Ya }ure malam na ku babba
Shi ne sai kuka ]auki gaba
Sai aikin sharri da zamba

8.         Ga shi fasihi ga karatu
Shi yas sa shaihi ya zautu
Ya }ure duk wani mai gulatu
Da ma dai kun nemi shantu
Don ba addini kuke ba

9.         Malam Jafaru ya yi zarce
Ya zam babba abin kwatance
Kai ba ma a Kano ba na ce
Duk a }asa ya zam fitacce
Sannan shi bai fariya ba

10.       Kowa na son gayyatar sa
Yai wa’azi da karatukansa
Bauchi da Yobe suna ta son sa
Ana ta yaba masa kan kiransa
Zuwa bin Sunnar [an Suwaiba

11.       Ban da [arikawa ~atattu
Don su ba sa son karatu
Ba sa }aunar mai karatu
Su dai bar su ki]a da fatu
Ba }aunar Manzo suke ba

12.       Jafaru ]an Mamudu sannu
Ka tsone musu ‘yan idanu
Don kan Sunna kai ka zaunu
Su bidi’a suka sa wa hannu
Ba son mai Sunnar suke ba

13.       Ka san Sunna ka karanta
{ur’ani, kuma ba ka maita
Ba ka yin fahari da wauta
Sunna tabbas ka rike ta
Mun gaishe ka bama bari ba

14.       Ka koyar da Kano dukanta
Har da na Barno ha]a da Kaita
Zariya ma duka mun fahimta
Kowa ya san kai bajinta
Kan tafsiri ba ba’a ba

15.       Jafaru babban malami ne
Shi a ]abi’u kamili ne
Gun wa’azin Sunna gwani ne
Ya wayar fa da kan mutane
Musulmi, ba wai ‘yan ki]a ba


16.       Don ya ce Sunnar Ma’aiki
Zai kare, ku kun ka soki
Wannan harka, kun ka ]auki
Gaba, kun zagi na baki
Wai ku sam ba ku yarda yai ba

17.       Komai za su fa]a wa Malan
Na sharri ai mun san hakannan
Yahudawa danginsu daman
Sun yi wa Musa ]a ga Imran
Ba mamaki za mu yi ba

18.       Sawun arna kun ka taka
Sun wa Manzo ma a Makka
Sharri, }age da nuna hauka
Kuma shi ne kun ka dauka
Sam ba ku sha bambam da su ba

19.       Sun san in Sunna ta zaunu
Duk wata cuta za ta tonu
Sai jama’a ka ga sun idanu
Sun zama wayayyu sanannu
Ba dolaye ra}uma ba


20.       Malam komai za su ce ma
Bar su da Allah zai gwada ma
{arshe yaya za su koma
Don tabbas sai sun nadama
Wanga batu ba kuskure ba

21.       Kun zagai mu mun tare mai
Ya fi gaban shehi a komai
Ciwon ru]ewa ya sa mai
Ba tsaran ku ba ne a komai
Jafaru ba bidi’a ya ke ba

22.       ’Yan ussha}u ku ba ni amsa
Don mene ne ba ku son sa
Sunna ba kwa son ya wasa
Wai ko addini na wasa
Kuke, ba wai Islam kuke ba?

23.       Ko don ya tono asiri
Na shehunnan }arya da sharri
Macuta ‘yan sane da tsari
Duk aikinsu fa ba na khairi
Ba aikin Allah suke ba


24.       Don haka yau ni ga ni ga ku
Zan fa]i halin shaihunanku
Zaluncin da suke da tsurku
Neman mata har da shunku
Koko ku ba ku san hakan ba?

25.       Ka ga a addinin [arika
Shaihi zai zina ko da jaka
Zai iya yin hu]uba ta shirka
Wai haka ]in daraja ya dauka
Yin haka ba shegantaka ba

26.       Akwai cire gashin munkirawa!
Su suka furta suna cirewa
Sadda suke son shakatawa
Ba sharri a batun ga nawa
Sannan ba }azafi nake ba

27.       Ko ka ji an ce wa mutane
Wai can Allah ne a zaune!
Komai gun su Ubangiji ne!
Ni na san wannan ~ata ne
Ba a cikin Islamiya ba


28.       Allah [ai ne bai da tamka
Bai da uwa, kuma bai da jika
Ba mata haka bai da kaka
Yana bisa Arshi ban da shakka
Na kuma san ban kuskure ba

29.       Kan Arshi Allah yana nan
Shi ya fa]a mun yarda san nan
Kun ce }arya duk bayanan
Kun mur]e ma’ana hakan nan
Ba kuma kan hujja bane ba

30.       Don haka dai Allah Guda ne
Na sama kan Arshinshi shi ne
Ai ya fa]a har gu bakwai ne
Amma daidaitonshi shi ne
Ban san yaya yai hakan ba

31.       Ka ga ]arikawan ga }atti
Sun je sun }ero salati
Sun ce kowa yai salati
Na manzo baba gun su Fati
Lada nai ba zai yawa ba


32.       Salatul fatin nan fa taku
Kun ce lada za ya ninku
Ga wanda yayi ta cikin batunku
Ta zarce wahayi a bar ku
Da kafirci ba }an}ani ba

33.       Zindi}anci kun iya shi
Kafirci kun tallata shi
Iskanci kun ha~~aka shi
Shashanci ku kambama shi
Ba son Annabi ai ku ke ba.

34.       Girman Manzo kun ka ]auke
Kun ba wawaye ba}a}e
Sai }arya sai sa}e-sa}e
Sharri, ba wani no}e-no}e
Ba aikin kirki suke ba

35.       Masu ki]a a wurin ibada
Ga su da wa kabari sujuda!
Sannan kowa ya fa shaida
An cinye makara sa’adda
Nasiru yam mutu ba ba’a ba


36.       T.J. shehi ne na zamba
Wai shi bai tsoron azaba
Ka ji mutum da hali na dabba!
Ga jahilci ba ka]an ba
Bai iya yin ko da ]igon ba!

37.       Tijjanin ga ma}aryaci ne
Na rantse shi makiri ne
Dan 419 ne ku gane!
Ai }arya ya ka wa mutane
Ba wai bin Manzo yake ba

38.       Nairorin jabu ya buga su
An kama shi yana buga su
Ya sha bulala a kan su
To ya za ai wai mu gamsu
Da cewa ba mugu ba ne ba
             
39.       Wai wannan shi ne waliyyi
Mai cuta babban gabiyyi
To Jafar sam bai da koyi
Da masu irin halin sha}iyyi
Ba kuma zai mai rangwame ba


40.       Wai wannan shi ne abin bi
Waye zai bi ba}in garibi
Ya sa ka kana yawo da carbi
Sannan ranar yin hisabi
Ka tashi a layin masu gaba

41.       Kun ce T.J. malami ne
Mu kuwa mun ce jahili ne
To ku taho bainar mutane
Ku kawo hujjoji a gane
In ba }arya ce kuke ba

42.       Ku kawo sunayen rubutu
Na littafai da ya yi fitattu
Da wanda ya koya mai karatu
Da ]alibban da ya yi wa satu
Ba su Harazimi ‘yan tasha ba!

43.       Shi kuwa wancan {adirawi
Nasiru bai son Kalarawi!
Allah ji }an shehi Kanawi
Babban malam {alarawi
Bai ma ‘yan bidi’a ragi ba


44.       Nasiru wai me za ya ce ma?
Cikin Ramalana ya zo da yamma
Gurasa tai ya ri}o a dama
Yana ci ga rana na a yamma
Cikin jama’a, ba wai ba’a ba

45.       Dangi za na yi ]an bayani
Na shehi [ahiru ]an Fulani
Kun san shi sam bai tunani
Sai fahari sai gani-gani
Don ba jin kunya yake ba

46.       Alfahari da yawan karatu
Sai }aryar da ta sa ya zautu    
Ga maula a wurin fitattu
Masu ku]i na giya ~atattu
Kun ]auka ba mu san hakan ba

47.       Ku iliminku na yaudara ne
Kun yi karatu kun yi zaune
Ba kwa koya wa mutane,
Muridanku, sai dai ]iya ne
Ke more ilimi na Baba!


48.       Malammanmu na al’uma ne
            Ba sa tsubbu ba su binne
Ba kuma sa cutar mutane
Ba sa duba ba su zane
Don mai yi ba zai haye ba

49.       Ku manufar ku a daina yi ne
Aikin tsamowar mutane
Kansu dake a cikin tukwane
Na jahilci da yawan bata ne
Shehunnanku ba sa iya ba

50.       Sai cutar jama’a kuke yi
Kun hana bayi yau su koyi
Sunnar Manzona Nabiyyi
Wai ku sai }aunar waliyyi
Na }arya ba mai hankali ba

51.       Don ko waliyyan damfara ne
|arayin imanin mutane
Su da su Pastor ‘yan uwa ne
Su }wace ku]in mabiya mutane
Ko ba su san cuta a ke ba?


52.       Kun saki Allah kun ri}e su
{attin banza ma irinsu
Me suka tanadda wa kansu
Balle ku ‘yan kore gun su
Anya ba hauka kuke ba?

53.       Kun mana sharri kan waliyyi
Kun ce ba ma son waliyyi
Wai har mun ce ba waliyyi
To duk }arya ce kuke yi
Don mu ba arna ba ne ba

54.       Mu mun yarda da auliyawa
Na gaske na sosai masu baiwa
Wa]anda ka bin Sunna da tsaiwa
Kan addinin Annabawa
Wannan tabbas ban musa ba

55.       To amma ku auliyanku
Wa]anda ku kai wa na]i da kanku
Tijjani ko Kaulahinku
Mummuna da kama ta tunku
Duk ba bin Allah su ke ba


56.       Ka ji mutane kangararru
Wanda suke da yawan dabaru
Sun iya sa fitina ta faru
Ta shirka, Allah wadan fujaru
Don ba addini suke ba

57.       Kafircinku yawa yake yi
{ur’ani ku ba ku koyi
Da shi, Allah wadaran ~arayi
Dake sace Tauhid na bayi
Su ba tsira za su yi ba

58.       Sunnoni duk kun aje su
Sai iskanci ba ku son su
Da izgilanci ma a kan su
Ranmu Musulmi ya fa sosu
Mun san ba Islam kuke ba

59.       Malam Jafaru ya }ure ku
Ya }ure }aryar malumanku
Ya katse carbin shehunanku
Ya ture rawanin su tunku!
Har malafar duka bai bari ba!


60.    To shine duk kun ]imauce
         Kun gigice kun makance
         Duk kun ru]e kun fukace
         Kun yi kamar motar itace!
         Don ba son Allah kuke ba

61.   Shehunnanku gaba ]ayan su
        Bayan Jafaru ya }ure su
        Gun Sarki suka kai batunsu
        Wai a hana shi ya bar ta~a su
        Sarki ba wauta ya ke ba

62.   Malam gun Sarki ya je shi
        Shi da mutum ]aya yar raka shi
        Su ko bila-adadin akan shi
        Ya dosa ruwan aya da kan shi
        Yak }ure dokin masu zamba

63.  ’Yan ussha}u kuna za}ewa
       Wai har Jafaru za ku ce wa
       Za ku buge shi ku daina shewa
       Zan muku warning ba da]ewa
       Ba da raha kuma za na yi ba


64.  In har kun cika ‘yan ta’adda
       To bisimillah ‘yan ta’adda
       Wanda ya fasa Rabbi mai da
       Min shi siriri ya sanda
       Ko ya gaza bai kai hakan ba

65.  Tunku]e hular Jafarun mu
       To daidai yake mu a gun mu
       Da ran shehunnai masu jurmu
       Yanzun ba sauran ragi mu
       Ba tsoron ta-kife muke ba

66.  Duk }azafin da kuke biyawa
       Kun ga alamu ne na cewa
       Ku Fir’auna kuke biyewa
       Ko ko Abu Jahalin kuke wa
       Aiki, ku ba ku san hakan ba

67.  Mun gama gano lungunanku
       Na cuta, zamba da damfararku
       Don haka yau sai kui ta kanku
       Ku kama sana’ar ci da kan ku
       Ba ku tsaya maula kawai ba


68.  {arya, sharri kun wa Manzo
       Malamman Sunna da kwazo
       An musu wai don sun bi Manzo
       Don haka kar ku bari ku cazo
       Sababbin sharri na gaba

69.  Ni ban }aunar ma ku fasa
       Wa}ar sharri kar ku nisa
       Kar ku bari mu za mu amsa
       Duk kule ai cas na jiran ta!
       Ba za mui muku rangwame ba

70.  Don kuwa mun rantse da Allah
       Duk wani mai warin jahala
       Wanda yake raini ga Allah
       In ya kuma sai ya yi }walla
       Ba zai huta duniya ba

71.  Maulidi bidi’a kuke yi
       Domin Manzona masoyi
       Bai ta~a yi ba kuna ta koyi
       Da ‘yan coci, sune su ke yi
       Bai da shiga gun ]an Suwaiba


72.   Ko [an Fodiyo ya rubuta
        Cikin Ihya’u mun karanta
        Amma don tsaba ta maita
        Kun }i ku daina mun fahimta
        Ba }aunar shiriya kuke ba.

73.   Hujjar nan da kuke kafawa
        Kui ta sakin baki da cewa
        Ai hujja ita ce hanawa
        Ta Annabi, dangi kun ji wawa!
        Ai hujja ce kanka babba

74.   Don ko Annabi ya hana mu
        Yin sababbin ayyukanmu
        Wanda dalili ba shi gun mu
        Kan shi, kamar maulud a gunmu
        Ya shiga iyyakum ku duba

75.    Tabbas bege ja’izi ne
         Shi ko guluwwi karkata ne
         Mu mun tabbata ai ~ata ne
         Amma duk kun toshe kunne
         Don ba son ha}}un ku ke ba


76.    Cin doki tabbas halas ne
         An ci gidan Manzon ku gane
         Ni na san ku jahilai ne
         Don ko karatun ]an ka]an ne
         Ba wani mai zurfi ba ne ba

77.    Don haka mu kam mun ci doki
         Nama mai da]i a baki
         Kai ma in da ka ci doki
         To da ya sanya ka ]oki
         Kai ta zuba ba ka ko sani ba

78.   Doki naman Annabawa
        Babu rabo gun {adirawa
        Ko kuma ku Tijjaniyawa
        Kai duk ]an iska da wawa!
        Doki ba naman shi ne ba

79.   Ni na san hauka kuke yi
        Tun da Tahajjud ba ku koyi
        Wai jam’i bisa me ake yi
        Ga hujjoji nan na koyi
        Da aikin Manzo ]an Suwaiba


80.   In dai har kun san karatu
        Duba Buhari kar ka zautu
        Kar ka biye wa ki]a da shantu
        Mandiri da kuke ta ~a~atu
        Ba addini ba ne ba

81.   Sannan Manzona mutum ne
        {ul innama ana bassharun ne
        Mislikumu, malam ka gane
        Cikin Kahafi, Fusilat a can ne
        Za ka ka duba ba fa]a ba

82.   Shi daraja tai ta yi zarce
        Ta fi gaban a tsaya kwatance
        Don kuwa ba wani ]a na macce
        Wanda ya kai shi wajen kwatance
        Ko a ina shi ya yi babba

83.   Ku sufaye nai kiran ku
        In har hujja ke gare ku
        Kan kare shegantakarku
        To ku taho ku baje batunku
        Don mu ba tsoro muke ba


84.   In dai ba tsoro ku ke ba
        In kuma ba }arya ku ke ba
        Ku kawo shehin naku babba
        Ya zo a kara ba wai ki]a ba
        Jafaru ba tsoro yake ba

85.   In dai har hujja ta sosai
        Za a kafa mana ai fa to sai
        Ai ta ruwan aya, hadisai
        Ingantattun nan na sosai
        Ba zagi da ashariya ba

86.   Bisa tafsirin Annabinmu
        Ko na Sahabbai malamanmu
        Su magabata ne garemu
        Manyan dattawa a gunmu
        Ba tsofaffin ‘yan tasha ba

87.   Kai jama’a anya da Allah
        Cikin aikin nan na su kalla
        Kullum sai zagin Izala
        Wai don ta zamto fitilla
        Ba hanyar cuta ba ce ba


88.   Ja-in-ja daga yau ta }are
        An }ure }arya babu bore
        Ba sauran yawo na kore
        Tuba ku bar }arya ku tare
        Kan Sunna ba karkata ba

89.    Jafaru ya }ure malumanku
         Mu kuma mun }ure baitukanku
         Ya}in maimai mun yi kan ku
         Sunna ta baje teburanke
         Ba daraja yanzun ku ke ba

90.   Ya Allah Sarkin sarauta
        Tona asirin masu ~ata
        Tauhidin bayi da maita
        Ta cin Sunnar baban su Binta
        Masu ~akar aniya ta zamba

91.   Wannan tarin baituka ne
        Mun yi wa masu batun kawai ne
        Masu nufin kore mutane
        Ga bin Sunnar kakan Hasan ne
        Shi ne Manzo ]an Suwaiba


92.    Mu mun shirya ba mu tsoro
         Ba ja baya ku je ku tsaro
         Sai a kara don babu tsoro
         Rago ya yi wuya ga toro
         Jafaru ba tsoro yake ba

93.    Nan ne za mu tsaya mu bar ku
         Don ku tsaya ku tuna da kanku
         In udtum udna a kan ku
         Mui ta fa]in shegantakarku
         Ba za mui muku rangwame ba

94.    Ga tanbihi nai gare ku
         Ku daina fa]in }arya da tsurku
         Ku bar ]aga tutar masu shunku
         In kuwa kun ce ku a bar ku
         Ba za ku ji da]in lahira ba

95.    Bayan Jafaru Malaminmu
         Ga wasu manyan malamanmu
         Shehunnai masana Ulumu
         Wanda muke }auna a ranmu
         Tun da suna bin ]an Suwaiba


96.     Za mu ziyara ne Kanonmu
          Don mu ga Dokta Amadunmu
          Dattijo mai kyau da gemu
          Dan Ibrahim ka aza mu
          Kan Sunna ba }ir}ira ba

97.     AbdulWahabi a gai da babba
          Sannu da aikin karya zamba
          Ka zama gwarzo mai takubba
          Na sare kan bidi’a ku duba
          Bai mata sauki ko ta}i ba

98.     [an Usman liman na Kundi-
          la, ka zamto mai jihadi
          Na tallan Sunna babu haddi
          ‘Yan bidi’a kuma sui ta raddi
          Za su gaza ba za su kai ba

99.     Sai na sako Malam Aminu
          Na Daurawa kai ma fa sannu
          Ka tsole musu ‘yan idanu
          Sun zama ‘yan tanka da shanu
          Allah da]o ilimi da haiba


100.   Za mu tsaya Zazzau mu gaisa
          Da Auwalu Albanin matasa
          Wanda gaba ]aya rayuwarsa
          Yai wa}afin ta a kan ya wasa
          Sunnar Manzo ]an Suwaiba

101.   Mu kam Zazzau mun yi sa’a
          Don kuwa da har ma da shi’a
          Amma Auwalu hina ja’a
          Sai ya diran mata kaifa sha’a
          Bai }yale ta ta kai tudu ba

102.   Ga malam Ahmad na Kauru
          Shi ma yai aiki tu}urru 
          Kan ya ga Sunna ta fa gyaru
          Malam ya sha kafsa daru
          Da ‘yan bidi’a ba }an}ani ba

103.   Malam Garkawi na biya na
          Wanda ya ke a garin Kaduna
          Saboda kiran shi a tsai da Sunna
          Ko daga jin sunan shi auna
          Ba zai wa bidi’a ragi ba


104.   Bello na Yabo ina yaba ma
          Ko ma}iya sun }untata ma
          Bayyana ha}}un ba ka }yama
          Ba ka ragi ko za su far ma
          Ba tsoron ta-kife ya ke ba

105.   Ku mabiyan Sunna kiran ku
          Nake kan girmama malamanku
          Ku kare mutuncin malamanku
          Kar ku sake ku saka su tasku
          In kuma kun }i ba ta yi }yau ba

106.    Kan ilimi kowa ya dage
           Mui maza kan ilimi mu zage
           Damatsa kar mu sake mu toge
           In ka }i ko sai waige-waige
           Da sun ritsa ka ba ka iya ba

107.    Rabbi tsare mu ga kama shirme
           Ko mu bi }arya  ko mu zarme
           Allah Rabbi ka sa mu kame
           Mu bar bidi’a ko bin kurame
           Bebaye maciya na gumba


108.   Wa}ar nan da muke ta yin ta
          Kan baitin nan ta ta}aita
          ‘Yan ussha}u ku dosa bin ta
          Allah sa dai kun fahimta
          Ba da]a ~arna za ku yi ba

109.   Wanda su kai wa}ar ga sune
          Asgaru ]a ga Abubakar ne
          Nura Yahayya ]a ga Hanne
          Masu kwatanta biyar Salaf ne
          Ba kuma alfahari mu ke ba

110.   Ga adreshin masu wa}a
          In ka zo Zazzau a kai ka
          In da a ke sallah ya Makka
          Markazu nan ne za a kai ka
          Mu ba ~oyayyu bane ba

17 Ga watan Disemba, 2003

Zariya.





[1] Allah ya ji kan sa y a ba shi darajar shahada! A ranar Juma’a 13 ga watan Afrilun 2007 wasu ‘yan ta’adda suka shigo masallacin gidansa a Dorayi, Kano, suka harbe shi da harsashin bindiga yana limancin sallar asuba. Ya rasa rayuwarsa a sakamokon wannan harbi. Allah yatona asirin wadannan ‘yan ta’adda ya tozarta su. Amin .