Saturday, January 22, 2011

AIKIN TELA


AIKIN TELA

A tsakanin shekarun 1998 zuwa 2002 na yi aikin tela, tun daga kan koyon sana’ar har zuwa }warewar da na samu.

Amma asalin dalilin da ya sa na yi wannan wa}ar shi ne, a watan Ramadan na shekarar 1423 bayan hijira na yi ]inkin da ya wahalar da ni }warai. 

Kusan kwana arba’in na yi ina kwana a shago in ka ha]a da ‘yan kwanakin da ke kafin azumin da kuma kwanakin bikin Salla don dukansu na yi su ne a shagon.

To da na auna sai na fuskanci ba wata riba ga irin wannan aiki na kwana ]inki. Duk da yake na sami ku]i sosai amma na rasa inda suka shiga, don ko ]inkin Sallah na al’ada ban yi ba, ma’ana ban sami halin ]inka yadin da na saya don kai na ba. Sannan ba wata ibadar kirki; Ba karatun {ur’ani, ba Tahajjud, ba zuwa wuraren Tafsiri! Wuni kawai nake ina kwana ]inki.

Ga mutane wa]anda ba su sami ]inkunansu ba suna ta ganin ba}ina. Da dai sauran matsaloli, wa]anda na ambaci mafi yawansu a wa}ar.
Wa]annan dalilan su suka sa na yi wannan wa}ar saboda takaici da ya addabe ni.

Wa}ar layi ]ai-]ai ce. Karinta na wata wa}ar fim ]in Hausa ne wadda Misbahu Ahmad yayi, ya na mata amshi da cewa

Iyye iye duniya labari

Ni ko sai na ce

Iyye iye tela sarkin aiki

Ga wa}ar:

1.    Allah ni nake yabo ban fasawa

2.    Gun manzo nake salati da yabawa

3.    Alaye, abokanai ban warewa

4.    Har matanshi Sayyadi na sanyawa

5.    Aikin tela yau na ke son wa}ewa

6.    Don na yi shi shekaru ban mantawa

7.    Na san duk lago da wayau da iyawa

8.    Gun koyon shi na iya har sabawa

9.    Bayan na iya na zam ban hutawa

10.   Aikin tela babu damar holewa

11.   Wahala ce kawai ciki ba }arewa
  
12.   Kullum ]inke-]inke ko ko farkewa

13.   Ko kuma yanka yaduka ko gogewa

14.   Ko facin da dole sai an toshe wa

15.   Wani tsoho ya takura bai }yalewa

16.   Al}awarinmu ba mu tsoron karyawa

17.   Costumer ido yake zazzarewa

18.   Ha}uri sai mu ce ya yi ko }yalewa

19.   Sai uzuri muke fa]a ko bayarwa

20.   Keken babu mai tana gun gyarawa
21.   Ai mutuwa akai, buki bai }arewa

22.   NEPA ba wuta zare na tsinkewa

23.   In azumi ya zo wuya aka ninkawa

24.   Kwana yanka riguna ko ]inkawa

25.   Yin rambul ga wanduna har hantsewa

26.   Aljihunmu bai cika bai batsewa

27.   Kai wata rana ban da asi na kashewa

28.   Ga basir yana shiga bai fasawa

29.   Ba ma yin tahajjudi don ta~ewa

30.   Sai neman ku]in da ma tarawa

31.   Ga }arya wajenmu ba ma jurewa

32.   Idi ban da mu ake lissafawa

33.   [inki bai barin mu domin holewa
34.   Kowa ya yi ]an wuya don ramewa

35.   Ga barci idonmu ya kusa cinyewa

36.   Ba ma yin shi ba mu samin hutawa

37.   Jam’i ban da tela komai dagewa

38.   Kifi ne a rijiya bai motsawa

39.   Bai jure wa zolaya bai daurewa

40.   Yadin ‘yan uwa ya zam zai cinyewa

41.   Ko ya sayar, ku]in ga banza ya kashewa

42.   Matsalolinmu ‘yan uwa ba }arewa

43.   Na bar tela ba ni fatan komawa

44.   Wannan ja’iba da]ai ban jurewa

45.   Laifin ya wuce batun iya yafewa

46.   Don jama’a suna yawan tsittsinewa
47.   Mu fatanmu Rabbana zai yafewa

48.   Dangi sai ku ba da }aimin dagewa

49.   Ko za}in aya ku san za ku yabawa

50.   Allah sa batun ku zam kun ganewa

51.   Nan zan dakata batu zai }arewa

52.   Sai wata rana Allah sa zamu gamewa

53.   Don wai kar ku zam da ni kun mancewa

54.   Dangi kun sani fa ai ba canzawa

55.   Nai salama ku tabbata kun amsawa

56.   Sunana Kabiru ko za ku ri}ewa

57.   Ya Allah ya ba mu mu duka dacewa

25 ga watan Yuli, 2002

Zariya.




Thursday, January 20, 2011

GAISUWA GA ALBANIY

GAISUWA GA ALBANI

Malam Muhammad Auwal Adam Albani na Zariya sanannen mutum ne da ya shahara a harkar karantar da Sunna da a}idar salafiyya.

Tun wajejen 1997 nake koyon karatuka da dama a wajen shi, musamman a fannonin Hadisi, A}ida, Usul, da sauran fannoni na addinin musulunci.

Na da]e ina tunanin in yi mishi wa}a, amma hakan bai samu cikin gaugawa ba. Sai a shekarar 2005, sa’adda na sami damar yi masa wannan wa}a.

Karin wa}ar na same shi ne a wajen wani mawa}i da ya yi wa {ur’ani wa}a a gidan rediyon Nagarta. Shi cewa yake yi a amshinsa

Mu kama karatu
Mui ta riko da zancen Allah
Kur’ani



Ni kuwa sai na ce:

A gai da min kai
Babban malamin salafiyya
Albani

Ga wa}ar:

1.    Da sunan Allah Sarki ni nake farawa
       Ina ro}on Allah Sarki ya karan baiwa
       Cikin wa}en da a yau zan yi wa ]a mai baiwa
       Muh’d Auwal Adamu wanda shi aka ce wa
       Albani

2.    Ina ta salati gun Manzo uba gun Fati
       Sa’annan na sanyo a ciki da Alul-baiti
       Da su da sahabbai manya ne da sun yi wafati
       Akan bin sunnar Manzona da tsantsar aikin
       Imani
  
3.    Masoya Sunna yau ku tsaya ku ]an saurara
       Ku karka]e kunne zan wa}a ga masu basira
       Uban AbdulBarri gwarzon da ya wuce tsara
       Ba}iyyatu ahlil-khairi wajen hadisi da sanin
       Kur’ani

4.    Idan fa ana dara dole uwa akan fid da ta
       Wajen ilimi Malam Auwal yana da bajinta
       Yana da fasaha sannan ba ya son mai wauta  
       Ina gai da ka ina ta yaba wa wannan gwarzon
       [anmasani

5.     A fannin ilimin {ur’ani ha]a da Hadisi
        {wararre ne shi bai saba wa khairin-nasi
        Wurin fatawa in dai har ya tarar da hadisi
        Ba zai mai tawili ba a gai da kai ya Malam
        Albani

Ina gai da ka
Allah ya tsare ka
Ya kare nufinka
Ya ]aukaka harka
Ba shakka
Kana da nufin kashe sa~ani

6.     Sa’annan ya san fannoni na duk tarihi
        Da fannonin Larabci duk yanai masu sharhi
        Wajen kafa hujja bai hada munkari da sahihi
        Wajen fikihu ma ya yi fice da gaske nake ba
        Tsammani

7.    Ku gai da min Malam masani akan komfuta
       Yana kera ta idan ta baci zai gyarata
       Yana da sani kan duk ilimin da yas shafe ta
        Ku bar mamaki don nace da ku ya san kowane
        Fanni 

8.     Mutum ne mai baiwa da take da ban mamaki
        Masoya Allah sun san ba guluwwi a ciki
        Idan nac ce Albani za ya cinye maki
        Idan da za ai mai exam wajen maki kuma ai
        Tsanani

9.     Ba zan ~oye ba Albani yana burge ni
        Saboda biyar sunnar Manzonmu dan Adnani
        A kanta Muhammadu ke wa’azi yana ta bayani  
        Yana cewa dangi sunna mu bi ta mu bar yin
        Sa~ani


10.   Yana ta kiran dangi don ]ai su bi magabata
        Su daina biyewa jahilci da aikin wauta
        Su gyara a}ida kan Sunna su inganta ta
        Ya ce wannan hanya ita ce ka]ai a ciki ba
        Ru]ani

Ina gai da ka
Allah ya tsare ka
Ya kare nufinka
Ya ]aukaka harka
Ba shakka
Kana da da nufin kashe sa~ani

11.    {wararren malam ya yafe wa mai zaginsa
         Ya ce ba komai don Allah yake aikinsa
         Ya ce da masoya su da wa]nda ke }yamarsa
         Dukansu guda ne don yace dukanku Musulmi
         Ikhwani

12.    A gaida min kai, kai mana maganin‘yan shi’a
         Da su da iyayensu manya dake masha’a
         Gaba ]aya su da wa]anda suke ta aikin bidi’a
         Ka tona asirin tsarinsu da ~arnarsu kai ta
         Bayani

13.    Wa]anda suke zagin sunna ko ka bi ta kansu
         Wajen yin raddi ba ka yin ragi a garesu
         Kana kyararsu da tsabagen ba}in aikinsu
         Nufinka ya zam tsantsar sunna ta danne aiki
         Mai muni

14.    Muhammadu Auwal malam ne da bai da mugunta
         Wajen koyar da karatu ba ya yi ma }eta
         Yana yin dalla-dalla mas’ala ya baje ta
         Wajen reference zai baka tuli ka je ka ji }ari
         Na bayani

15.    A halayenshi Muhammadu babu yanke zumunta
         Da]ai ba ya zagi, }arya ko bai }aunar ta
         Ka bar shi wurin tallan sunna da kuranta ta
         Da bayyana ha}}un ko da ‘yan ]ari}a za sui
         Gurnani

            Ina gai da ka
Allah ya tsare ka
Ya kare nufinka
Ya ]aukaka harka
Ba shakka
Kana da da nufin kashe sa~ani

16.    Ina kake malam wanda ku]i baza su saye ba
         Ku daina tayawa don ni na sani ba riba
         Ba zai canza ba don ‘yan kyautukanku na zamba
    A don haka ne ma bai kar~a, bare wa’azi nai
    Yai rauni

17.    Ina kake malam ]an baiwa da babu irinka
         Wajen iliminka da tsarin rayuwar da ka ]auka
         Da gogewa kan harkar rayuwa da nufinka
         Na alheri, kullum sunna ta }ara gaba kowane
         {arni

18.    Ina ro}on Allah Sarki ya }ara haza}a
         Da ]umbin ilmi, don da’awa ta zam ta mi}a
         Ku zo ku bi sunna ‘yan bidi’a ku daina zala}a
         Idan kun bi ta, kun dace da tsarin Allah
         Kur’ani

19.    Ka je maktab ]in malam don ka sha mamaki
         Ka bai wa idonka abinci ya kalli kayan aiki
         A nan ne za ka ga littaffi ka bu]e baki
         Muhammadu Auwal ya tara su ya tsara fanni-
         Fanni


20.    Yabon da nake wa malam ni a nan zan huta
         Idan an kwana biyu wata}il na ]an maimaita
         Ya Rabbi ka kare min malam ka }ara fahimta
         Ka sa mu ci amfanin ilmin Muhammadu Auwal
         Albani

Ina gai da ka
Allah ya tsare ka
Ya kare nufinka
Ya ]aukaka harka
Ba shakka
Kana da da nufin kashe sa~ani

21.    Inai muku bankwana danginmu sai wata rana
         Idan kuka tad da Muhammadu sai ku mi}a yabo na
         Ku ce masa Asgar ya gaishe shi, nai masa murna
         A kan kyan aikin da yake ya]a sunnar Manzo
Adnani

22.    Ku ce masa Allah na ro}a ina }arawa
         Ya ba shi sawaba har ranar shigar shi kushewa
         Ya sa Manzona zai cece shi ranar tsaiwa
         Ya zarce Aljanna, Allah ka kare min Sheik
         Albani

23.    A wannan baitin zana rufe ku ]an ban uzuri
         Ina da larura zan tare ya-nawa da sauri
         Ku mun ha}uri don wa}ar tawa ba ta da tsari
         Saboda }arancin baiwata da tsantsar fikira
         Mai rauni

Ina gai da ka
Allah ya tsare ka
Ya kare nufinka
Ya ]aukaka harka
         Ba shakka
Kana da da nufin kashe sa~ani

23 ga watan Agusta, 2005

Zariya.


Thursday, January 13, 2011

DARUL HADITH

Na yi hidimar }asa wayo a shekarar 2005 a garin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun. A lokacin da na zo tafiya sansanin matasa masu yi wa }asa hidima a Shagamu, sai na ga dacewar na yi wa wasu ]alibaina na makarantar Darul Hadith bankwana na musamman a wa}e. Don haka ‘yan kwanaki kafin na bar Zariya zuwa Shagamu sai nu rubuta wannan wa}ar.

Wa}a ce mai kwar hudu. Karinta ina tsammanin asalin shi na wa}ar ga]a ne. Amma ni dai na ]auko shi ne daga wakar ]an uwa Malam Adam Abul-Abbas wadda ya yi mai suna Hijabi.

Ga wa}ar:

1.    Darul Hadisi ina son ki
       Da ke da duk ma’abotanki
       Ina nufin ]alibbbanki
       Gare su nai shaidar kirki

2.    Darul Hadisi gidan Sunna
       Ajin da ya zarce ko ina
       Ga ]alibai marasa sakana
       Wa]anda raina ke }auna

3.    Mun yi karatoci da yawa
       Littattafai har saukewa
       Duk Juma’a ba fasawa
       Karatuka muka bayarwa

4.    A da mu kan yi da an sauko
       A juma’r kowane mako
       A yanzu ko loton farko
       Na safiyar Juma’ar mako

5.    Mun ka karanta [ahawiyya
       Wurin a}idar salafiyya
       Mun sauke Allah ya biya
       Ya ba mu iko na biyayya

6.    Da Tabsira mun sauke ta
       Ka sanya Umda bayanta
       Sanya Adab sai ka dakata
       Akwai ragowa zan furta

7.    Ina nufin Talkhisin nan
       Na Siffantun malam din nan
       Albani ta hadisan nan
       Da ma Janaza kuma san nan

8.    Mun ka yi littafin Nahawu
       Da Sarfu kui ta biyar sawu
       Na baitukan in nai sahawu
       Ku ]an tuna mani kui afwu

9.    Da Musdalah mun koye shi
       Shi da Usul don mun yi shi
       Dukan su komai da ka ji shi
       Dalla-dalla ba }unshi

10.  Ya ]alibai gani gareku
       Ina yabawa dukaninku
       Don kuwa in dai da ba ku
       To ai ba makarantarku

11.  Kuna ta jure zuwa darasi
       Ko da ba ku da ko sisi
       Allah ya sa ranar ba’asi
       Mu garzaya duka Firdausi

12.  Ai dole na jinjina ma wasu
       Wa]anda ke cika aikinsu
       Wa]anda ba sa latti da su
       Nake batu, ku kun san su

13.  Da masu latti da ‘yan fashi
       Da ni da su sam ba bashi
       Babu yabo izuwa sashi
       Na masu ]an banzan fashi

14.  Masu fahimtar darusana
       Allah ya sa ku a Aljanna
       Duk wacce ko ta zamo sauna
       To walla ni babu ruwana

15.   Na so a ce na kira suna
        One-by-one na mutane na
        Amma yawan ku shi ya hana
        Don kar a zo a ji haushina

16.   Don ko hala in mance wata
        Ko ko a ce na zage ta
        Amma ha}i}a ba mafita
        Don wasu kam sai na furta

17.   Irinsu A’isha mai naci
        Na tambaya ba ta sakaci
        Cikin aji ba ta barci
        Tana kiyaye da lokaci

18.   A’isha da ke da Firdausi
        Ai tuni nai muku lasisi
        Yaran da in dai ga nassi
        Ba sa sa~a wa hadisi

19.   Allahu Rabbi ya biya ku
        Ya sa ku aure tamkar ku
        Sannan ya }ara fahimtarku
        Ya yau}a}a muku }arshenku

20.   Kada ki ce na manta ki
        Asma’u yarinyar kirki
        Dukan ajin nan }annenki
        Don kin riga su a gaishe ki

21.   Dake da duk ‘yan }annenki
        Walla kuna nunan kirki
        Amma na kan sha mamaki
        Yadda kike fashin aiki

22.   Khadijah ke ba kya wasa
        Irinki yaya ga Nafisa
        Wacce a yanzun tai nisa
        Wacce a ke ce wa Hafsa

23.   Kada ki manta burinki
        [anki ya zam yaron kirki
        Ya zarce Ibnu Hajar, sonki
        Yai ta wa sunna jan aiki

24.   Ya karya wannan }alubale
        Da tuntuni aka daddale
        Allah ka sa yaron ya }ale
        Kar burin ya bi kwale-kwale

25.   ‘Yar Bilkisu da Jamila
        Har ma na sanya da ‘yar Sala
        Na kan tuno ku da madalla
        Ban so ai maku bulala

26.   Ku daina latti da ke Murja
        [iyar da ba ta da ja-in-ja
        Da Aisha sai kin canja
        Tsawon hijabi }asa ya ja

27.   Dole na sanyo Aishatu
        Da Rabi har da Suwaibatu
        Ko da a yanzun sun ‘yantu
        Sun sauke ba su karatu

28.   Ina kiran ku da alheri
        Allah ya kare dukan sharri
        Ya sa ku auri maza na gari
        Wa]anda basa yin mari

29.   Ina kike Auntie Sadiya
        Ya wacce ba ta jayayya
        Ina tuna ki a zuciya
        Allah yai maki sakayya

30.   In na tuno Auntie Sadiya
        Na kan ji }unci a zuciya
        Allah kai mata sakayya
        Ka ba ta lada na biyayya

31.   Kai mana canjin alheri
        A madadin wanga ha]]ari
        Allah ka }ara mana jari
        Na dangana bisa mu}addari

32.   Rashida yarinyar kirki
        A gai da ke har Antinki
        Ga shawara ta a gare ki
        Ki }ara }wazo gun aiki

33.   Kun ga cikin lissafina
        Dole na sanya da Hassana
        Sannan Nafisa Hasan na tuna
        Mata ga Garba na jinjina

34.   Halima T. Shehu na Kano
        Safiyya ma kan ki zan kwano
        Ke da Faridatu na gano
        Cewa kuna fa da alfano
 
35.   Fatima matar malam ce
        Bintoto mai son darasi ce
        Ki dinga rokon Rabbi ki ce
        Allahu ya sanya ki yi fice 

36.   Na kusa in manta da Sa’a
        Da ke da Safiyya mai sa’a
        ‘Yar Asama kin buga sa’a
        Tun da kina }in masha’a

37.   Dije Lawal }anwata ce
        Da Rabi sun }ulla }awance
        Allah ka sanya kin dace
        Aurenki da hankali kwance

38.   Ke Abu }anwa gun Dije
        Tsaya in ]an yi maki jaje
        Don kan fashi kin cije
        Da ke da Dijale kun saje

39.   Harira na can ]akinta
        Tana biyayya ga mijinta
        Ya Rabbi biya bukatunta
        Ka ninka lada a gareta

40.   Maryamu yaya ga Sakina
        A gai da babbar Antina
        Kanwarki ni ta shiga raina
        Ina ta nuna mata }auna

41.   Ke ko Sakina ki saurara
        Gare ki zan ]an yi ishara
        In dai har ni kika aura
        Wallahi kin tsere asara!

42.   Ya Rabbana na ro}e Ka
        Ka taimaka ma bayinKa
        Wa]anda ke bin manzonKa
        Wanda ya kawo sa}onKa

43.   Ya ‘yan uwana kui hakuri
        Wa]anda ba su cikin tsari
        Wa]anda nam manta, buri
        Na wa}e Daru bila fahari

44.   Ya ]alibaina ku ]an tsaya
        Ga hanzarina guda ]aya
        Don ko karatu za ya tsaya
        Ba na son mu yi jayayya

45.   Ni za na je NYSC
        Don haka dole mu bar darasi
        Kui hakuri kar kui kwafsi
        Duk farko sai yai akasi

46.   Allahu ]alibbai ga su
        Rabbi ka biya bukatunsu
        Ka yafe dukkan laifinsu
        Ka shirya dukkan zuriyarsu

47.   Ka sa su more wa ilimi
        Su dinga aiki da ilimi
        Don ya kasance ko lazimi
        Na zana wanga da al}alami

48.   Ina wa dangi ban kwana
        Ku yafe dukkan laifina
        Mu ro}i Allah duk ya mana
        Sakamakonmu da Aljanna

49.   Ai rabuwa ba ta da da]i
        Bayan sabo da nisha]i
        Mui hakuri har zuwa ba]i
        Mu jure dukkanin ra]a]i

50.   Allah na ke ro}o ya mana
        Falalar gamuwar mu da juna
        Ya sa mu jure da amana
        Da girmamawa gun juna

51.   Ma’assalam ni naka cewa
        Don lokaci na ta }urewa
        Zan ha]a duk nawa-ya-nawa
        In tafi neman dacewa

52.   Shi kenan sai na dawo
        Har tsaraba zan ]an kawo
        Ai baitukan sun ]an yi tsawo
        Amma a nan zan sa tsawo

53.   Nai adu’a a wajen Allah
        Tare da mammatse }walla
        Na ce ya }ara min falala
        Da gafara da yawan sallah

27 ga watan Yuli, 2004

Zariya.