TUWON GANDU
A watan Agusta na shekarar 1997 na kammala karatuna na Difuloma a Misau. Lokacin ne na rubuta wannnan wa}a. Na yi ta ne da nufin zaburar da matasa akan su tashi su yi karatu. Saboda a lokacin na lura da cewa matasanmu ba wai suna wani son karatu ne ba. Mafi yawa suna kwana ne su tashi da burin su yi ku]i dare ]aya ba tare da sun yi wata wahala ba.
Wa}ar mai }war hu]u ce, don haka take da ]angon ciki da na waje kamar yadda mai karatu zai gani.
Karinta na wa}ar baka ne, tana da amshi kamar haka:
Neman ilimi a yanzu shi ne ja baya
Don haka arzikinmu kullum ba ya nuna.
Sunan wa}ar Tuwon Gandu. Na sa mata wannan sunan ne saboda la’akari da cewa kowa na bu}atar ya yi amfani da abin da ta ke karantarwa kamar yadda ya ke bu}atar tuwon gandu.
Ga wa}ar nan:
1. Allah ya Tabara kai ne Babban Sarki
Ro}ona gareka Allah ni zan ]auki
Al}alami in zana wa}a domin ]oki
Ka ban fasaha Allah in cika burina
2. Allah Rabbi kar ka sa in yi halin jaki
Ka ban fasaha, ilimi har da yawan baki
Ka kare sharri a garan ya Allah Sarki
Ka bani kaifin lura ya kar Maulana
3. Allah salli ya Ilahi gun manzona
Alayensa har sahabbai gun mai suna
Ahmadu ]an Amina zainun nurun fina
Har matansa sayyadi ]a ne ga Amina
4. Wasu ‘yan baituka nake son yi don na kira
Yara ‘yan uwa musulmai sai a yi lura
Duk mu zage mu nemi hanyarmu ta Aljanna
5. Kar ki yi wauta ki gane jigon zancena
Ba wata tsada gare ki ke ‘yar babana
Sai dai ilimi ina fa]a maki Auntiena!
6. Kai ma ]an samari zancena na kanka
Ba daraja gareka sai ka san dininka
Ka san Rabbana da tarihin Manzonka
Sannan sai ka nemi hanyar nan Aljanna
7. Girman kanka jingine kar ka bi ‘yan baya
[au allonka ko takardunka ka ]au hanya
Je gun malami ka ce masa “Na zo koya”
Kar ka yi wasa wata ran kai ma ka nuna
8. In ya biya ma ka ro}i Allah ka yi bita
Ka zage damtse kar ka bi hanyar ‘yan mata
Kar ka sake a bar ka can baya kana wauta
{arshe ma ka zam kamar ~era kaicona
9. Ke ma ‘yar uwa ina fayyace sa}ona
Gare ki, zancen ilimi shi ne burina
Kar ki biye ta mai yawan shirme mummuna
In kuwa kin }i ji ko kin tabbata dai sauna
10. Talla zuwanki ]akunan gayu shirme ne
Gulma da yin acha~a aikin matsiyata ne
In kuwa kin }i sai mu ce wannan ai cus ne
Ba ki da martaba idon mu da ke sai zana
11. Saurara in ba ki haske ke yarinya
Ai daraja tana ga mai ilimi, tarbiyya
Ba wai sa skirt da anko ba da yin }arya
Ba kuma bin maza da talla ba har can gona
12. In ma ban da sakarai mai wauta ke ma
Ba ki ganin samarunkan ko da sun nema
In sun gane jahila ce sai su ji }yama
Waye za ya saura sai dai wawa sauna
13. Ilimi garkuwa ta ya}in neman hanya
Ta zuwa Jannatun-na’im ka ji wurin hayya
Tashi ka nemi garkuwa kar ka ji ‘yar kunya
In ka sake ko ba ruwana ko oho na
14. Zan maka tambaya ka amsa in za ka iya
Ka ta~a cin karo da mai ilimi na baya?
Ko kuwa bai da martaba ko kuma ya kaya?
Amsa mana in ka na da amsar mutumina
15. Abin da zan ce maka har ke ma ‘yar gata
{arshe ko in ce da ku babbar manufata
In nushe ku martabar ilimi da nagarta
Addininmu sai da ilmi ya dangina
16. Boko ma muna bu}atar mu karanta shi
Musulunci da shi gaba ]ai mu nazarce shi
Nau’in ilimi ko wanne mu ka kalato shi
Ka sanya addini a gabanka abokina
17. Duk wani ~angare na ilmi babu na baya
Ko wanne ka sami damar shi ka ]au hanya
Kai dai kar ka zam kana layin ‘yan baya
Sune jahilai da kullum ba sa nuna
18. Mu jona ilmin mu da manyar makarantunmu
Har ma jami’a idan dai har mun samu
Amma sai mu gyara hali da ]abi’unmu
Halayenmu yau matasa sai an zauna
19. Abin takaici yanzun duk makarantunmu
Da jami’o’i da cibiyoyin iliminmu
Sun zama centres a nan muke ~ata halinmu
Holewa kawai matasanmu suke }auna
20. Wannan shi ya sa a kullum ba sa lura
Ba bitar karatuka kullum sai fira
Sai satar da in dubu tac cika sai kora
Don Allah mu gyara halaye dangina
21. Duk wani shirme ka bar shi ke ma sister ta
Ku ]au batun nan ilimi hanya ta nagarta
Ka bar Husaina ko kuma je ka ka aure ta
Ke kuma }yale ]an samari ya ji zancena
22. Shinkun nan ba}a da kin ka saka a gabanki
Ba daraja ba ce abin kunya ce gun ki
Kai ma mai biye ta za kui kunnen-doki
Sai an ba ka withdrawn ka gane batuna
23. Ka lalata rayuwar yarinya kai ma
Ka watsar da naka ilmin da ka zo nema
Ka zamto abin kwatance, kuma an sa ma
Suna wai ana fa]in gwarzo na Husaina
24. Kin tozarta ‘yan uwa, dangi, babanki
Wanda ya yarda ke rashida ce yab bar ki
Kin ka taho wurin karatu amma kin }i
Sai shirme ki ke kina aiki mummuna
25. Ban ce kar ku nemi aure ba abokaina
Ku janye zargin ku a kai na sisters ]ina
Ba wai na hana ku soyayya ba batuna
Amma so irin na shirme shi nan nuna
26. In kuwa kun ga kun amince aure za kui
Kun kuma yarda babu shunku ba}a to sai kui
Soyayyarku, har ku cim ma buri har kui
Adu’a, Rabbi taimaka mana ya Maulana
27. Ba zagin ka nai ba sarki na gidan yamma
In ka lura duk nasiha ce da nake ma
Addininmu ko nasiha ne can dama
Duk wani huci da ka ke don Allah ka daina
28. Ke ma malama idan dai har kin lura
Na san za ki gane zancen ban da harara
Wata}il da kina jira ne sai na rera
Ki ce da ni zancen banza kai ne sauna
29. Kan zabon da angulun nan ta saka shi ma
Kifi na ganin ka ya kai mai jan koma
Gara ka bar halinka in ka }i ko to kai ma
Ka ta~e ka kauce layi ka zamo sauna
30. Ba wai na fi duk mutane baki ne ba
Ba kuma na fi duk na zaune karatu ne ba
Ba ilimi garan ba, ban ce ban nema ba
A ‘a sai yawan karambani aikina
31. Duk zancen da naf fa]a ba sabo ne ba
Sai dai tuntuni da kullum bai }are ba
Hanyar tsira Ubangiji Allah nuna
32. Wa}an nan a nan nake son na takaita ta
Allah kai min dacewa kan manufata
Allah sa mu gane zancen da na yo bita
Ban ilimi Tabara Sarki Mahaliccina
34. Sunana Kabir, a Zariya nai wayona
Ba na tantama dukanku kuna da sani na
Wa}an nan da nay yi ranar goma na zana
Ga watan Yuli, Rabbana sa na ga manzona
10 ga watan Yuli, 1997
Misau.