DAMBEN KUTURU
Soyayya, kamar yadda ‘yan magana ke fa]i makauniya ce. Akwai wata yarinya ana ce da ita Zainab Lawal. Allah ya ]aura mata bala’in son wani abokina kuma takwarana. Tana bala’in }aunar shi irin }aunar da ke hana ganin laifi da jure duk wani wula}anci da taka iya fuskanta daga gare shi. Kai abin dai har ya kai ma shi ma dole ya dawo yana son ta ba don yana tsantsar }aunarta a zuciyarsa ba, sai don tsabar tausayin irin halin da ta tsunduma kanta a ciki a sanadiyyar wannnan soyayya, duk da har izuwa yanzun da nake rubuta wannan rahoton bai aure ta ba.
To wannan wa}ar na yi ta ne a wani yammaci na wata Asabar muna zaune a ofishin shi abokin nawa sai ta zo tana ta }o}arin shawo kan shi ya saurare ta amma abin ya faskara.
Kamar da wasa sai na ]auki karin wata wa}a ta wani fim ]in Hausa. Duk da ban kalli fim ]in ba an ce min sunan shi Tijja, a cikin wa}ar ana yawan maimaita wannan ]angon a matsayin amshi
Ranar rabo da ke zan kuka
Ranar raboda ke ba shakka
Wallahi dole ne na yi kukan }auna
Ni kuwa sai na ce
Ranar rabo da Malam K.B.
Wallahi Abu za ta yi kukan }auna
Sai na ]au}i wannan a matsayin amshin wa}ar. Nan take sai na fara rero baitoci ina rubutawa, kafin na ankara sai na ga baitocin sun taru a cikin wa}ar mai }war uku.
Na kiraye ta da sunan Damben Kuturu ne bisa la’akari da yanayin abin da ke faruwa na naci, wanda ake ce wa “damben kuturu” a cikin harkar.
Ga wa}ar:
1. Allah raban da ciwon }auna
Don kar na dinga ma kai kaina
Wurin da ba bu so raina zai }una.
2. Na tausaya wa ‘yar yarinya
Zainab tana cikin soyayya
Amma tana cikin wahala kan }auna
3. Malam Abu-Nusaiba ta kama
Wai shi take ta so sai fama
Take ta yi nufinta su aure juna
4. Ta sha wuya tana kan shan ta
Nacin ta ya wuce }imarta
Amma ta bangaren K.B. ba }auna
5. Son wanda ba ya son ka wuya ne
Kai ni ina ganin hauka ne
Amma da }yar ki yarda da ni ra’ayina
6. Ga shawara free zan ba ki
Tsaya ki karka]e kunnenki
In kin }i walla to ni babu ruwana
7. Daure ki }yale Malam K.B.
Sanya wa zuciyarki nasibi
Na dangana ki daina halin dangina
8. Ki ro}i Rabbana ya hane ki
Son wanda ba ya ma }aunar ki
In kin }i na sani ke ce ai sauna
9. Ki dosa addu’a gun Allah
In kin }i za ki sha bulala
Ta damuwa da cizon yatsar }auna
10. Auren ku zai wuya ke Abu
Ki daina bibiye wa gaibu
Harkar da babu riba babu ruwana
11. Malam gare ka ni zan juyo
Na san ka ka }ware gun wayo
Amma ka gane bai aiki gun }auna
12. Harkar ga ta wuce ta ]abi’a
Ban ce ka ce ba eh ko a’a
Amma tsaya ka lura da kan zancena
13. {aunar da Abu walla ta ke ma
Ta zarce wacce Binta ta ka ma
Ta zarce ma ta duk wata ‘ya mummuna
14. Kan son ka za ta jure kome
Dukkan wuya, ta fa]i ta zame
Ba ta gani idonta da kwantsar }auna
15. Komai na ce kana da sanin sa
Sai tuntuni da ba ni barin sa
Sai na yi koda yaushe cikin wa}ena
16 To mafita a gun ka ka gane
[ayan biyun da za na fa]a ne
Ni zan fa]e su sai ka biyo baitina
17. Ko dai ka aure ‘yar Abulle
In ka }i son ta dole ka }yale
In ka }i ko akwai matsala a ganina
18. ‘Yan Hausa sun fa]a a batunsu
Ai “na }i” ta wuce wayon su
Ta sha gaban shi ta kuma maisai sauna
19 To sai ka daina sauraronta
Komai yawan irin nacinta
Ai dole ne a }arshe za ta tsugunna
20. Misbahu ya fada na yarda
Ya marka]e Hadisi ne da
Ke yin batu akan }wayoyin }auna
21. Son zuciya ta so mai sonta
Wannan da ke yawan }aunar ta
Har ma ya ke ta lallashi kan }auna
22. Har ma ya ke ta yi mata bauta
In dai ko har ana ~acin ta
To ba ta jure ]aci dole ta }una
23. Allah ya sanya kun ji batuna
Ni ko ya ba ni ladan kaina
Aikin da nai nasiha gun dangina
24. Na san batun ga sam ba da]i
Wa}ar ga walla babu nisha]i
Ku han}ure ku ]auki batun da na zana
25. Nai addu’a gurin Mai kowa
Ya amsa addu’ar ]an kowa
Ta gaskiya da }hairi ya Rabbana
26. {auna da ke wahal da halitttu
Ta sa su zam kamar sun zautu
Ya Rabbi kar ka sanya ta kawo kaina!
27. Tammat bi hamdi Rabbil Arshi
Sarkin da ni nake ro}on shi
Ya sanya Asgari a gidan Aljanna!
24 Ga watan Yuli, 2004
Zariya.
No comments:
Post a Comment