SAI WATA RANA
A shekarar karatu ta 2003/04 na rike aji shida na babbar sakandaren koyar da ilimin Larabci da Addinin Musulunci ta Abubakar Gumi da ke Zariya bangaren mata a matsayin baban aji.
Bisa al’adar makarantar akwai bikin yayen ]alibai da ake yi wa masu fita a }arshen kowace shekarar karatu bayan kamamla jarabawar }arshe, duk wanda aka bai wa baban irin wannan ajin dole ne ya yi ruwa ya yi tsaki don ganin cewa bikin ‘ya’yan nashi ya yi armashi.
Akan gudanar da abubuwa iri-iri a wajen bikin na wuni ]aya, kama daga kan jawabai, wasannin kwaikwayo, lacca ko wa’azi, walima da dai sauransu.
To shi ne ni kuma na rubuta wannan wa}ar a daren ranar da za a yi bikin na ba ]aya daga cikin ]alibai masu fita ]in, sunanta Hajara AbdurRahman Muhammad ta rera wa}ar a filin wannan taro, abin da ya jawo da dama daga cikin ]aliban suka bar dandalin taron suna share hawaye.
Wa}ar kwar biyu ce. Na kuma yi ta ne da wani karin Larabci wanda ake ce da shi Hazaj.
A sha karatu lafiya
1. Inai muku sallama dangi
Ku amsa min ma}ala ta
2. In mi}a yabo ga manyana
Iyayena mafifita
3. Wa]anda su kai ta koya min
Karatu har zuwa na fita
4. Iyayena a gaishe ku
A aikin naku ba wauta
5. Dukan wahala fa sun jure
Wajen koyar da makaranta
6. Kuna koyar da ‘ya’yanku
Dukan fanni su ilmanta
7. Kuna ha}uri da shirmenmu
Da duk aiki na mai wauta
8. Kuna “Allah ya shirye mu”
Kuna adu’a da yin kyauta
9. Ha}i}a kun jihadin ku
Ilahi ya sa ku nanata
10. Ya sa ku cika da imani
Ya sa ku cikin ma’azzurta
11. Ya ]aukaka martabarku duka
Ya sa ku zamo mafifita
12. Ina ro}on iyayena
Ku yafe kure da ma wauta
13. Da ni da dukan sa’o’ina
Aji shida wanda za su fita
14. A ban kwanan da za na muku
Hawayena suna ta fita.
15. Saboda ina ta alhini
A kan rabuwar da ba mafita
16. Ina kuke ‘yan uwa na aji
Kiranku nake da muryata
17. Ina so ne ku yafe ni
Ku rangwanta ma heart ]i ta
18. Mu yayyafe wa junanmu
Mu ]au hali na manyanta
19. Ku san cewa a yau ]in nan
Batun rabuwar mu ba mafita
20. Hala ha]uwa ta ]an yi wuya
Da }yar ne ma ta maimaita
21. A gai da Principal baba
Nasiha mun ji da]inta
22. A gai da Munir yana son mu
23. Da shi da Kabir Mahaifinmu
Da Uncle R. da Barista
24. Abu Jummai a gaishe ka
Sa’annan har da Hedmasta
25. Da Malam Salisun Higher
Da duk sauran mahallarta
26. Aliyu Rufai gaishe ka
Da sauran masu yin bauta
27. Na safe da malaman yamma
[iyarku tana ta zancenta
28. Hakan nan ‘yan uwa dangi
[iyan Higher ta ‘yan mata
29. Ina cewa da ku bye-bye
Da alheri nake fata
30. Kuren da na yi ku yafe ni
Ku ]an daure ku gafarta
31. A wanye lafiya dangi
Cikin aiki na jarunta
32. Salamu alaikumu na fa]a
Ku amsa don na ]an huta
33. Ma-faa-ii-lun Ma-faa-ii-lun
A nan zan }are wa}ata.
13 ga watan July, 2004.
Zariya
No comments:
Post a Comment