Monday, December 20, 2010

SARKAR BEGE


SAR{AR BEGE

Akwai wata yarinya da na so ta matu}a. Mun yi soyayya ta ban mamaki har wajen shekaru hu]u.

Kodayake daga }arshe Allah bai }addara akwai aure a tsakanina da wannan
yarinya mai suna Zainab M. Tukur ba.

To a wani lokaci cikin watan Satumba na shekarar 2001 ta bar garin Zariya kacokan ta
koma Abuja wajen wata yayarta. Shi ne sai ta bai wa wani abokina adireshinta a
birnin tarayya, ta ce ya kawo mini tare da wasi}a wacce a ciki ta bayyana cewa tana in
je Abuja don in ziyarce ta.

Da na tashi tafiya sai na rasa me ya kamata in kai mata a matsayin tsaraba. Shine sai
na zauna na rubuta wannan wa}ar a daren da zan yi tafiyar a wayewar garin shi.

Sai na sa wa wa}ar suna Sar}ar Bege.

Karin ta na Larabci ne ana ce da shi Kamil

Ga wa}ar:

1.         Na fara wa}ata da sunan Rabbana
            Allah Tabaraka, Rabbi nai masa godiya.

2.         Sannan salati gun habibi Ahmadu
            Manzo Muhammadu shugaban duka Anbiya.

3.         Ashabu, Alul-baiti Azwajur Rasul
            Nai gaisuwa a gareku manyan duniya.

4.         Har ma da sauran sallafawa bai ]aya
            Sune suke bin ]an Amina da gaskiya

5.         Allah ka ban lura ka ba ni idaniya
            Wa}a na shirya za na yi wa masoyiya

6.         Karo fasaha Rabbi don in bayyana
            Zafi na bege wanda ke cin zuciya

7.         In farfa]a mata duk irin ciwon da yau
            Begenta yah haifar gareni a tun jiya

8.         Manufa ta gane ni matacce ne a kan
            Begenta, wa}ata batu ne gaskiya
9.         Ki tsaya ki saurara inai miki tambaya
            Ya wagga ‘ya mai kyan hali da na kwalliya

10.    Mene ki ke so ko ki ke }auna na yi
            Domin ki tabbata na mace kan ke ]aya

11.       Komai ki ke so babu haufi ambato
            Zan aikata shi in da]a]a maki zuciya

12.       No idea, ban san a yaushe ne ba har
            Kika sace heart ]i na madubin zuciya

13.       Na dai sani na tsinci kai na ne kawai
            Na dulmiya kogi na son ki gaba ]aya

14.       Zainab Dear, mai kyan kama mai zakira,
            Zan ba ki labari asirin zuciya

15.       I miss your love all the moments, babu shi
            Loton da nam manta da ke ko da ]aya

16        Ni ko a yaushe ina tuna ki ina fa]in
            Sunanki, just for some relief in zuciya


17.       Koda a barci I dream of you through
            Haka nan da na farka na ambaci gimbiya

18.       Hold on, here is just a joke ki tsaya ki ji
            In na fa]i kya ]an tsaya ki yi dariya.

19.       Wasu lokuta da yawa nakan buga ]imuwa
            Sunanki nak ke bai mutane bai ]aya

20.       Wani ]an uwa har sai da yai mini tambaya
            Don ya ji na ce nai da shi ke gimbiya

21.       Nai murmushin ya}e gare shi na ce da shi,
            Ka yi hankuri waswasi nay yi a zuciya

22.       Yau ban da buri duk a fa]in duniya
            Illa na aure wagga ‘ya kyakkyawiya

23.       Ha}uri a yanzun ba shi yin wani magani
            In dai akwai so bai rage masa kaifiya.

24.       Tauraruwar mata abin so ce ga duk
            [a mai sa’a, da]a na wa tsara zarciya


25.       Na za~i mai kyawun hali da]a nai sa’a
            Sannan da Addini take yin kwalliya

26.       Ilimi na boko ga na addini duka
In tai }ira’a sai ka ce Ba}uraishiya

27.       Halinta addini da kunya, kamila
Surarta mai kyau, Abu ga ta da juriya

28.       Mai murmushi, muryarta za}i Abuwa
Hanci, ido, kai kin haye galleliya

29.       ’Yar dariyar nan birge K.B. ai ta ke
            Dan }ara yin ta ki sanyaya mini zuciya

30.       Ko gun tsayi ke medium ce ko ina,
            Matar shiga mota kike ke gimbiya

31.       Da Hijab yana sharar }asa ta sa Ni}ab
Kune waliyyai masu bin Allah ]aya.

32.       Ba tantama, Sunna ki ke bi sahiba
Salafiyyatun, Alarammiya kyakkyawiya


33.       Sai dai yawan kishi, yawan zargi haka
            Ba kya ragowa sanda za ki yi tankiya

34.       Ai na sani in na yi laifi kan}ani
            Na sha masifa, lokacin ba dariya!

35.       Ba kya barin ta-kwana, don Allah tsaya
            Zainab ki saurara ki bar yin }yaliya.

36.       Ke ce uwa a gida, sarauta ta ki ce,
            Koda akwai wasu ai ki nai musu zarciya

37.       Ai ke ka]ai ce, ba irin ki a zuciya
Ni ke nake so ba irinki a Zariya

38.       Matan }asan nan duk cikar su tsaya ki ji
            Da maza da su duka ]ai suke ga idaniya

39.       Mamansu Abdul ni fa ke ]ai nas sani
            Ki yi murmushi ki sake  ki wala ke ]aya.

40.       Kullum tunanina na gan ni da ni da ke
            Da]a mun yi aure za mu zauna waje ]aya.


41.       Allah cika mana wanga buri nan kusa,
            Zainab ki ce “amin” mu amsa bai ]aya

42.       K.B. yana ango amarya Zainabu
            Rannan akwai shagali gidan ga na duniya.

43.       Mun tsunduma, kogi na }auna mun nutse
            Allah ya }addara za mu haura lafiya.

44.       Mun ]an]ana, za}i na }auna mun jiya,
            Rikici na so tabbas muna kan shan wuya.

45.       Ni yau ina ro}o gare ki guda ]aya
            Ki ri}an da alkawari mu zauna lafiya

46.       Ki sani Ilahi za ya saka min a kai
            In kin ka }ona min muhallin zuciya.

47.       Ni sa sani abadan ba zan cuce ki ba
            Ha}}inka Allah ne wakili shi ]aya

48.       Na san kina }auna kina so na }warai
            Na gode Allah Rabbana mai duniya.


49.       Don Allah kar ki gaza da sauraron batun
            Sauran bayani ]an ka]an ne zan biya

50.       {arshe a yanzun godiya zan bayyana
Ke gimbiya I am grateful gaskiya

51.       Tabbas ha}i}a kin kasance ‘yar halas
            Kin sha wuya, don ni kina yin juriya

52.       Mai hankali ce ke da lura my dear
Mai gaskiya ce ke da saurin yafiya

53.       You are smart, gifted, sweetheart Zainabu
            Ke first class ce duk a matan Zariya.

54.       Allah cika wa K.B. burin rayuwa
Aurenta Abu, da mallakar ta gaba ]aya.

55.       I wish ki zamto kin amince gimbiya
            Da batun da nai har ma kina yin dariya

56.       Nan zan tsaya na }are wa}ata a nan
            Allah ka taimaki masu bin ka da gaskiya.


57.       Sai an jima Zainab inai miki sallama
            K.B. yana cewa a huta lafiya.  

4 ga watan Oktoba, 2001.

Zariya


No comments:

Post a Comment