KAFIN MU JE DA NISA
Na da]e ina rubuta wa}o}i iri-iri, akan abubuwa dabam-dabam. Duk da yake yana da ]an wuya in iya tuno wa}ar da na fara yi. Musamman saboda akwai wasu wa}o}ina da suka ~ata. Zan dai iya tuna cewa lokacin ina aji biyu na babbar sakandaren Larabci ta Jama’atu da ke Zariya, Malam Ma}ari Sa’id, wanda shi ne shugaban makarantar a lokacin, ya koya mana Arulin Larabci. Yai ta kwa]aitar damu mu dinga }o}arin tsara wa}a, wannan ya taimaka mini }warai wajen gane cewa ina da baiwar rubuta wa}a.
Baya ga haka mutanen da nake sa ran su karanta wa}e-wa}ena a karo na farko sune Hausawa. Har ila yau ina ]aukar wa]annan wa}o}i a matsayin wata ‘yar gudummowa tawa ga ci gaban Adabin Hausa. Wannan ya sa na ke fatar kundin wa}o}in ya yi tsawon rai da farin jinin da zai sanya manazarta Adabin Hausa su waiwaye shi.
Wa]annan da ma wasu dalilai suka sanya ni rubuta wa}o}i da dama cikin harshen Hausa.
A wannan kundin zan yi }o}arin tattara wa]anda Allah Ma]aukakin Sarki ya ba ni ikon tattarawa ne kawai. Zan kuma ]ebo mafi yawan su ne daga asalin rubutun hannun da na yi na wa}o}in.
Zan yi }o}arin zayyana dalilin da ya sa na rubuta kowace wa}a kafin in kawo mataninta. Tare da fa]in ma’auninta da dai duk wani bayani da na ga dacewar kawo shi a matsayin shimfi]a ga wa}ar in Allah ya so.
Sai kuma kare-karen wa}o}in wa]anda mafi yawansu na samo su ne daga wasu wa}o}i da na ji ko na karanta. Wannan kuwa ni a ra’ayina ba satar fasaha ba ne ba kuma laifi ba ne, don shi kari na kowa ne in dai yana da abin da zai fa]i da shi. A gani na kari kamar yare ne; wanda wani bai isa ya hana wani magana
da shi ba, abin nema kawai a ce kana jin yaren yadda ya kamata ka iya magana da shi.
Don haka nake ganin cewa kare-karen wa}o}in da na ]auko daga wasu wa}o}i na wasu mawa}a ba satar fasaharsu bane, ko ba komai su ma ko kuma in ce wasu daga cikinsu ]auko su suka yi daga wasu wa}o}in na wasu mawa}an dabam. Don haka nai ta bayyana inda na samo kowane kari a inda ya dace in bayyana hakan
Ba na cewa zan jero su a kan wani tsari na musamman. Zan kawo su ne kawai yadda na samu dama, ba wai don kasala ko rashin tsari ba, sai don }arancin lokaci da rashin sukuni.
Ko da wasa ba na jin cewa aikina kammalalle ne, don haka kamar ko wane aiki a fagen Adabi, wannan kundi karan bara ne ga masana, malamai da masu nazarin Adabi.
Fatana su yi ma wa}o}in nazari da na}adin da zai taimaka wajen gyara kurakurena, }ayata wa}o}in fiye da yadda suke a yanzu da taimaka wa masu karatu }ara fahimtarsu. Da hakan ya zama wani aiki da zan kasance mutum na farko da zai yi farin ciki da shi.
Ina neman taimakon Allah nake cewa a sha karatu da nazari lafiya.
Kabir Abubakar Al-Asgar
25 ga watan Satumba, 2006
Zariya.
No comments:
Post a Comment