Wednesday, December 1, 2010

ALMAJIRI BARAN MALAMI

        ALMAJIRI BARAN MALAMI

Wannan wa}ar na yi ta ne a Kasuwar Ukaza[1] wacce ke ci duk }arshen zangon karatu na farko a Kwalejin Abubakar Gumi ta nazarin ilimin musulunci mai zurfi dake Tudun-Wadan Zariya.

Na kasance malami a mai koyar da Adabin Larabci a wannan Kwalejin tun 1998 har zuwa 2005.

Wannan kasuwa an }ir}iro ta ne a matsayin wata hanya ta raya Adabi, don haka a }arshen kowane zangon karatu na farko na kowace shekarar karatu. [alibai wa]anda Allah ya yi wa baiwar wa}a su kan gabatar da wa}o}insu, Daga }arshe al}alai su fitar da sakamako a kuma mi}a kyaututtuka ga wa]anda suka yi fice.

A wasu lokutan ma akan sami wasu daga cikin malamai su gabatar da wa}o}i a wannan dandalin na Ukaza don }ara wa ]aliban }warin gwuiwa ko wasu dalilai na dabam.

Ni kuwa kasancewa ta malamin Adabi, hakan ya ba ni damar tsoma hannu a cikin harkar dumu-dumu. {ar}ashin haka na kasance ni da wasu malamai wa]anda ke da basira ko sha’awar wa}a muna }ara wa ]aliban }warin gwuiwa ta hanyar jagoranta gasar, rubuta wa}o}i da gabatar da su a wannan dandalin.

A irin haka ne na yi wannan wa}ar da na sa wa suna Almajiri Baran Malami
Sunan yana da nasaba ne da irin abubuwan da na ambata a cikin wa}ar.

Karin wa}ar na baka ne, kuma na la}ance shi daga wani malamin Adabin Hausa wanda ya koyar a Kwalejin A.D. Rufa’i ta nazarin shari’a da ilimin addinin musulunci dake garin Misau, a lokacin ina ]alibi a Kwalejin a tsakanin shekarun 1995 zuwa1997, sunanshi Malam Ibrahim Boboh, mutumin garin Bauchi. Ya yi amfani da karin ne a wata wa}a da yai wa ]aliban shi da ya koyar na aji ]ayan a ’yan difuloma a Hausa na shekarar 1997 a lokacin ni ina aji biyu.

Wakar mai }war biyu ce, a sha karatu lafiya.


1.         To gaba dai gaba masu shuka hairan
Abadan ba kwa talautuwa.

2.         Rabbi da]an hikima ta shirya
            Wakar }arshen zango ga ‘yan uwa.

3.         In yabi manyan ]alibaina
             ‘Yan Higher Islam ta kowa.

4.         Duk jinsunsu maza da mata,
            Ni sam ba na rarrabewa.


5.         Ni sha’awa kuka ba ni ‘yan uwa
            Tun da kuna zimmar karantuwa.

6.         Kun ka baro harkarku kun
Ka zo neman ilmu, ku sami }aruwa.

7.         Kun bi umarnin Rabbana da Manzonshi
            Na ilmi don wadatuwa.

8.         Manzo yace wajibi ga kowa
            Ilimi, tushe na rayuwa.

9.         Girman kai kun kakkabar da shi.
            Don makasa ce gun wadatuwa.

10.       Kun yi dabara kun yi hattara,
            Kun shiga jirgi mai fiton ruwa.

11.       Na }i da}i}i na }i jahila,
            Ban }yale ta ba jinni doluwa.

12.       Kai raba kan ka da muguwar guba
            Ko ka aura ba ta zaunuwa.


13.       Duk lamari in dai da jahilai
            To yanke, }arshenshi kwaruwa.

14.       Ko jayayya ba na yi da su
            Don na san }arshen ta ru]uwa.

15.       Ba su da wayau babu hankali
            Taron shashasha da sulluwa.

16.       Kwashen dangi ne, }adangare
            Wawa, tunku mai karaurawa.

17.       Barka dangi kun yi arziki
            Kun kauce saran kububuwa.

18.       Kun yi karatu kun mutunta yau
            Kun zama manyan masu baiwa.

19.       Duk wani farau dole ne ya }are
            Koda zai shekaru nawa.

20.       Ga shi kamar jiya ne muke karatu
            Zango yau za mu cim ma wa.


21.       Mun yi karatoci da ku da dama
            Da yawa, ba sa }idayuwa.

22.       Mun gama aikin wanga term a yanzun
Hutu shi za mu far ma wa.

23.       Zafi, hunturu, ruwa da iska
            Duka ba su hana ku taruwa.

24.       An yi bayanai har gami da bita,
            Shifta ba ta tsagaituwa.

25.       Ga zulumin test, ga na jarrabawa
            Jinga mai cushe rayuwa.

26.       Ga fama da munafikin talaucin ]alibta
Ga rashin ruwa.

27.       Ga doka da yawan hukunta bulala,
            Sannan babu }yaluwa.

28.       Ka ga Imam da Habibu {a’ida ga
            Malam Rabo ba su ra~uwa.[2]

29.       In sun kama sun hukunta doka
            Tabbas ba ta ciratuwa.

30.       Sun kawo gyara a discipline,
            Sun hana ~arna ba su zaguwa.

31.       Ga shi aji malam yana biyar    malam
Kai ka ce tururuwa.

32.       Ba sassauci babu kama hannun yaro
Sai dai karantuwa.

33.       Ga Asgar sam bai da tausayi
            Ya ce sai an sai Ma}aluwa!

34.       Dangi sun koka saye ya zam ra]i
Na ce ba ya ra]uwa.

35.       Ba na sassauci wajen farillan harka
Sam  ba ni tatsuwa.

36.       Ga ni gwanin yanka cikin aji
Mugu, yautai, ba ni radduwa!


37.       Kai dangina kun yi }o}ari
Tabbas kun cancanci gaisuwa

38.       Kun yi karamci, kun yi dauriya
            Kun sha gwagwagwa da damuwa.

39.       Ladan aiki in da gaske ne
            Ya Allah ya biya ku ‘yan uwa.

40.       Yadda kuke yi kar ku karkace
            Himmar taku ta }ara ninkuwa.

41.       Ran jarabawa na yi dariya
Na sha kallo na ga ]imuwa.

42.       Na ri}e baki don ta’ajjibi
            Al’amarin ya sa ni ru]uwa.

43.       Kowa no}ewa yake ta yi
             Nafsi – nafsi, ba ta ]an uwa!

44.       Wasa tare ake cikin raha
            Ranar ci kai ke ta ~alluwa.


45.       Mai wayon sata ana ta le}e
            Amsar kuwa ta }i satuwa.

46.       Ran da takardu ko suke fita
            Malam na shan tir da tsinuwa!

47.       “Ai mun gane ba ya son mu oh
            Kin ga abin da ya bai wa Sabuwa!”

48.       “Can da tsiyarsa bakin munafiki
            Alli ne ajalinsa damuwa!”

49.       Yaya ma za ai ki cinye exams
            Bayan ba kya karantuwa?

50.       Ba kya bita kin fi saniya ci
            A aji sarkin kururuwa.

51.       Ga ki gwanar ]iban faten gidan suna
            Party ma kina zuwa.

52.       Sai ta]i, kallon fina-finan Dan Ibro
            Sannan da yin rawa.


53.       Shi kuwa har zuga sakarai ake
            “Baba ka hadu ba ka kaduwa.”


54.       “Ai gifted ne shi wajen karatu
            Ka ji mazaje ba su saruwa!”

55.       “Ka ga dashen Allah cikin mutanensa sahihai
Sannu kainuwa!”

56        Ga }arshen tsarinka kai ake shukawa
Ba ko ]igon ruwa.

57.       Ban ce kar a yi love ba sahibi
            In ba hubbu ina ga rayuwa?

58.       Kai shanyar garin tuwo ka }yale
Bayan ka san da guguwa?

59.       Ka ]au aska ka da~a cikinka
            Daga baya ka hau kururuwa?

60.       Sai da wuta fa maza ka shan zuma
            In ko babu su dosa harbuwa.

61.       Kwashi rabonka ka daina }orafi
            Gode Allah ban da rainuwa.

62        ‘Ya’yan dangi sai a kara himma
            Da ka]an aka tara mai yawa.

63        Ka ga rabon kwa]o yana }asa
            Ko ya hau sama za ya }waluwa.

64.       Ya Allah sa gurbin wuya a kullum
Da]i ne ke ta wanzuwa.

65.       Ban cika son sabo da masu so na ba
Dare daya mui ta ~alluwa.

66.       Za ai hutu za ku je gida
            In kun je kwa gai da ‘yan uwa.

67.       ‘Yar rabuwar na zazza~a ni
            Nai alhini na ji damuwa.

68.       Na san tilas ne cikin zaman nan da mu kai
An sami sa~uwa.


69.       Na faye rauni, daina bincike
            Laifi na san ba ya }irguwa.

70.       Ga ni gaban ku ku yafe laifuka
            Rabbi yana son masu yafuwa.

71.       Ko ba]i ka san naka naka ne
Dangi ka san ba ya canzuwa.

72.       Ko an tirsasa ya tauna namanka
            {ashin ai ba ya taunuwa.

73.       ’Yan Higher ban ]au guda ba
            Na yafe kowa da kowa.

74.       Zan dasa aya don na sha}i iska
Sai zango mai biyowa.

75.       Ni ne Asgar zan tsaya a nan
            Rabbi da]an ilimi da garkuwa.

76.       Sa shida kan saba’in ka }irga baitocin
Koko na yi mantuwa?

19 ga watan Oktoba, 2000.

Zariya








[1] Asalin sunan kasuwar an aro shi ne daga  tarihin adabin larabci na zamanin jahiliyya, wanda a lokacin larabawa na amfani da wannan kasuwa a matsayin kasuwar baje-kolin Adabi
[2] Sunaye ne na wasu malamai da ke cikin kwamitin ladatarwa na Kwalejin

No comments:

Post a Comment