BABA DA ‘YAN [IYA
[alibai da Malamai wa]anda Allah yai wa baiwar wa}a sukan baje kolinsu da wa}o}i a kasuwar.
Wannan wa}a tana daga cikin abubuwan da kasuwar ta haifar a shekarar karatu ta 2004/05.
A lokacin nine nake matsayin baban aji ]aya ‘A’ na }aramar sakadare. Sai na ga dacewar in ]an wa}e ‘yan yaran, saboda la’akari da cewa akwai wasu ubannin azuzuwan da su ma sun yi wa azuzuwansu wa}a.
Karin wa}ar iri ]aya ne da na wa}ar Danniya
Ga wa}ar:
1. ’Yan One A da ku nake
Yaran gaskiya
2. ’Yan kirki na ke kira
Amsa bai ]aya
3. Yara masu laddabi
Don ba sa tsiya
4. Ba sa latti don haka
Ba sa shan wuya
5. Sun gane karatuka
Babu da}i}iya
6. Yara masu kwalliya
Babu }azamiya
7. Gun kyau ba kamar ya su
Ko zinariya
8. Har mamanku Raudatu
Ka ji masoyiya
9. Na gaishe ki na yaba
Nai maki godiya
10. Yarana ku ]an tsaya
Zan muku tambaya
11. Waye za ya ja da ku?
Ba shi a Kulliya
12. ’Yan One B ina suke?
Ba su da zuciya
13. ’Yan One C fa ya suke?
Ka ji gidan wuya
14. Ku One D ku ba ni gu
Ba ku da zuciya
15. ’Ya’yana abin yabo
Su duka bai ]aya
16. Ga ladabi da hankali
Ga su da juriya
17. Allah ba su illimi
Ya Sarki ]aya
18. Imani da]a masu
Sun zama auliya
19. Aljanna ka sa su je
Can Firdausiya
20. Gun aure ka sa su samu
Marasa tsiya
21. Ba duka da tsangwama
Ba kuma shan wuya
22. ’Yan One A da Asgari
Baba da ‘yan ]iya
23. Ma’assalam da ku nake
Yaran gaskiya
30 ga watan Disemba, 2004.
Zariya.