Thursday, February 17, 2011

Danniya

DANNIYA
 
Khadija AbdulLahi Usman suna ne da ba zai yiwu in manta da shi da wuri ba.
Wata yarinya ce da aka ta~a sa mani ranar aure da ita! Sai da abubuwa da shirye-shirye suka kankama, sai mahaifinta ya ce ba zai yiwu ba, bisa dalilin rashin fahimta tsakanin shi da wasu ‘yan uwansa sa }auye kamar yadda ya ce, sakamakon haka komai ya wargaje.

Duk da yake ba wai na damu ne fiye da }ima ba, amma na ga dacewar in sajjala abin da ya faru a wa}e, don tarihi da kuma biyan bu}atar zuciyata ta adabi.

Wa}ar tana da layi bibbiyu ne. Karinta na wa}ar baka ne. Kuma na same shi ne daga wani fim din Hausa mai suna {ugiya. Duk da yake har zuwa yanzu da nake rubuta wa]annan bayanan ban kalli fim din ba! Ina dai jin wa}ar ne kawai a bakin yara da mata.

Ga wa}ar:

1.    Na gode wa Rabbana
Sarki ne ]aya

2.    Na yi yabo da gaisuwa
            Tun daga zuciya

3.    Gun baba ga Fatima
            Khairul Anbiya

4.    {unci ya yi dandazo
            Ya cika zuciya

5.    An zalunci mai ita
            An masa danniya

6.    Manya sun yi yaudara
            Sun yi halin tsiya

7.    Bayan sun yi rantsuwa
            Alkawari ]aya

8.    Sun karya shi kai tsaye
            Sun }i su tausaya

9.    Allah Rabbi ya sani
Ba su da gaskiya

10.   Hujja wacce za su ban
            Sun rasa ko ]aya

11.   Sai dai kame-kame
            Sun ma ban dariya

12.   Dije ]iyarka ce na’am
            Sai dai ]an tsaya

13.   Zan maka ]an tuni a nan
            Don ka rage tsiya

14.   Aure gun ta dole ne
            Komai zilliya

15.   Duk da kana ganin kamar
            Kai mani danniya.   

16.  Ai wani za ka bai ita
            Ko da ka }iya


17.  Komai son ta ba ka
            Aure wannan ]iya

18.  Dole ka ba waninka
            Har yai mata kishiya

19.  Kuka na ina ta yi
            Gun Allah ]aya

20.  Allah ya isa na yi
            Sam ba yafiya

21.  Ka zalunci rayuwar
            Dijale ‘yar ]iya

22.  Ka raba so na gaskiya
            Ka yi abin tsiya

23.  Ka hana ‘yarka yin
            Karatu don }aniya

24.  Ka sanya ta ta yi fail
            Allah wadan tsiya


25.  Tir da uba irin ya kai
            Ya mara zuciya

26.  Wanda kwa]ai ya haukata
            Mai wautar tsiya

27.  Dije ki han}ure kawai
            Kad da ki dulmiya

28.  Ba ki da hope wurin uba
            Don bai gaskiya

29.  An }wacen ki jarumi
            An miki danniya

30.  Na rufe baitukan anan
            Don ban son tsiya

23 ga watan Agusta, 2005.

Zariya

No comments:

Post a Comment