Thursday, February 24, 2011

BABA DA 'YAN DIYA


BABA DA ‘YAN [IYA

Yana da wahala wanda ya ]an]ani za}in sana’ar Adabi ya halarci Kasuwar Ukazan da ke ci a Kwalejin Abubakar Gumi duk }arshen zangon karatu na farko ba ta burge shi ba

[alibai da Malamai wa]anda Allah yai wa baiwar wa}a sukan baje kolinsu da wa}o}i a kasuwar.

Wannan wa}a tana daga cikin abubuwan da kasuwar ta haifar a shekarar karatu ta 2004/05.

A lokacin nine nake matsayin baban aji ]aya ‘A’ na }aramar sakadare. Sai na ga dacewar in ]an wa}e ‘yan yaran, saboda la’akari da cewa akwai wasu ubannin azuzuwan da su ma sun yi wa azuzuwansu wa}a.

Karin wa}ar iri ]aya ne da na wa}ar Danniya



Ga wa}ar:

1.    ’Yan One A da ku nake
             Yaran gaskiya

2.    ’Yan kirki na ke kira
             Amsa bai ]aya

3.    Yara masu laddabi
            Don ba sa tsiya

4.    Ba sa latti don haka
            Ba sa shan wuya

5.    Sun gane karatuka
            Babu da}i}iya

6.    Yara masu kwalliya
            Babu }azamiya

7.    Gun kyau ba kamar ya su
            Ko zinariya

8.    Har mamanku Raudatu
            Ka ji masoyiya

9.    Na gaishe ki na yaba
            Nai maki godiya

10.  Yarana ku ]an tsaya
            Zan muku tambaya

11.   Waye za ya ja da ku?
             Ba shi a Kulliya

12.   ’Yan One B ina suke?
             Ba su da zuciya

13.   ’Yan One C fa ya suke?
             Ka ji gidan wuya

14.    Ku One D ku ba ni gu
             Ba ku da zuciya

15.    ’Ya’yana abin yabo
             Su duka bai ]aya

16.    Ga ladabi da hankali
             Ga su da juriya

17.    Allah ba su illimi
             Ya Sarki ]aya

18.    Imani da]a masu
             Sun zama auliya

19.   Aljanna ka sa su je
             Can Firdausiya

20.   Gun aure ka sa su samu
             Marasa tsiya

21.   Ba duka da tsangwama
             Ba kuma shan wuya

22.   ’Yan One A da Asgari
             Baba da ‘yan ]iya

23.   Ma’assalam da ku nake
            Yaran gaskiya

30 ga watan Disemba, 2004.

Zariya.

No comments:

Post a Comment