Saturday, January 22, 2011

AIKIN TELA


AIKIN TELA

A tsakanin shekarun 1998 zuwa 2002 na yi aikin tela, tun daga kan koyon sana’ar har zuwa }warewar da na samu.

Amma asalin dalilin da ya sa na yi wannan wa}ar shi ne, a watan Ramadan na shekarar 1423 bayan hijira na yi ]inkin da ya wahalar da ni }warai. 

Kusan kwana arba’in na yi ina kwana a shago in ka ha]a da ‘yan kwanakin da ke kafin azumin da kuma kwanakin bikin Salla don dukansu na yi su ne a shagon.

To da na auna sai na fuskanci ba wata riba ga irin wannan aiki na kwana ]inki. Duk da yake na sami ku]i sosai amma na rasa inda suka shiga, don ko ]inkin Sallah na al’ada ban yi ba, ma’ana ban sami halin ]inka yadin da na saya don kai na ba. Sannan ba wata ibadar kirki; Ba karatun {ur’ani, ba Tahajjud, ba zuwa wuraren Tafsiri! Wuni kawai nake ina kwana ]inki.

Ga mutane wa]anda ba su sami ]inkunansu ba suna ta ganin ba}ina. Da dai sauran matsaloli, wa]anda na ambaci mafi yawansu a wa}ar.
Wa]annan dalilan su suka sa na yi wannan wa}ar saboda takaici da ya addabe ni.

Wa}ar layi ]ai-]ai ce. Karinta na wata wa}ar fim ]in Hausa ne wadda Misbahu Ahmad yayi, ya na mata amshi da cewa

Iyye iye duniya labari

Ni ko sai na ce

Iyye iye tela sarkin aiki

Ga wa}ar:

1.    Allah ni nake yabo ban fasawa

2.    Gun manzo nake salati da yabawa

3.    Alaye, abokanai ban warewa

4.    Har matanshi Sayyadi na sanyawa

5.    Aikin tela yau na ke son wa}ewa

6.    Don na yi shi shekaru ban mantawa

7.    Na san duk lago da wayau da iyawa

8.    Gun koyon shi na iya har sabawa

9.    Bayan na iya na zam ban hutawa

10.   Aikin tela babu damar holewa

11.   Wahala ce kawai ciki ba }arewa
  
12.   Kullum ]inke-]inke ko ko farkewa

13.   Ko kuma yanka yaduka ko gogewa

14.   Ko facin da dole sai an toshe wa

15.   Wani tsoho ya takura bai }yalewa

16.   Al}awarinmu ba mu tsoron karyawa

17.   Costumer ido yake zazzarewa

18.   Ha}uri sai mu ce ya yi ko }yalewa

19.   Sai uzuri muke fa]a ko bayarwa

20.   Keken babu mai tana gun gyarawa
21.   Ai mutuwa akai, buki bai }arewa

22.   NEPA ba wuta zare na tsinkewa

23.   In azumi ya zo wuya aka ninkawa

24.   Kwana yanka riguna ko ]inkawa

25.   Yin rambul ga wanduna har hantsewa

26.   Aljihunmu bai cika bai batsewa

27.   Kai wata rana ban da asi na kashewa

28.   Ga basir yana shiga bai fasawa

29.   Ba ma yin tahajjudi don ta~ewa

30.   Sai neman ku]in da ma tarawa

31.   Ga }arya wajenmu ba ma jurewa

32.   Idi ban da mu ake lissafawa

33.   [inki bai barin mu domin holewa
34.   Kowa ya yi ]an wuya don ramewa

35.   Ga barci idonmu ya kusa cinyewa

36.   Ba ma yin shi ba mu samin hutawa

37.   Jam’i ban da tela komai dagewa

38.   Kifi ne a rijiya bai motsawa

39.   Bai jure wa zolaya bai daurewa

40.   Yadin ‘yan uwa ya zam zai cinyewa

41.   Ko ya sayar, ku]in ga banza ya kashewa

42.   Matsalolinmu ‘yan uwa ba }arewa

43.   Na bar tela ba ni fatan komawa

44.   Wannan ja’iba da]ai ban jurewa

45.   Laifin ya wuce batun iya yafewa

46.   Don jama’a suna yawan tsittsinewa
47.   Mu fatanmu Rabbana zai yafewa

48.   Dangi sai ku ba da }aimin dagewa

49.   Ko za}in aya ku san za ku yabawa

50.   Allah sa batun ku zam kun ganewa

51.   Nan zan dakata batu zai }arewa

52.   Sai wata rana Allah sa zamu gamewa

53.   Don wai kar ku zam da ni kun mancewa

54.   Dangi kun sani fa ai ba canzawa

55.   Nai salama ku tabbata kun amsawa

56.   Sunana Kabiru ko za ku ri}ewa

57.   Ya Allah ya ba mu mu duka dacewa

25 ga watan Yuli, 2002

Zariya.




No comments:

Post a Comment