Har zuwa shekarar karatu ta 2001/02, ban gushe ba ina koyarwa a Kwalejin Abubakar Gumi dake Zariya. To a wannan shekarar na rike aji ]ayan babbar sakandaren mata a matsayin baban ajin. A }arshen shekarar karatun, ma’ana lokacin da zan yaye su zuwa aji na gaba sai na yi musu wannan wa}ar da na kira da suna Shataletale
Sunan wa}ar yana da dangantaka da kasancewar tana da jigogi masu karo da juna, wato yabo da zambo
Ma’aunin ta irin na wa}ar Almajiri Baran Malami ne.
Ga wa}ar:
1. Nai bisimilla Rabbi kai nake ro}o
Sarki mai zubo ruwa.
2. Yau ga Muhammadu ni nake salati
Jagoran Annabawa.
3. Alaye nasa, har da ma sahabbai
Ba wanda na ke cirewa
4. Ya Allah ka da]an tulin basira
Ni zan yi batu ga ‘yan uwa.
5. Ya Ala sa wa}ar ta tsaru
Kar harkar nan ta zamo da yawa.
6. Yau wa}ar nan ni da zan gina
‘Yayana ni zan ta~owa.
7. Don kuwa yarana aji hudu
Tabbas sun zarce na kowa.
8. Ba ni ne na hukunta sun fi
Kowa ba fa, a’a malamawa.
9. Kowane teacher na fa]in
Ajina ke kan gaba gun karantuwa.
10. Kun iya lissafi da Ingilishi
A Aruli ba ku zaguwa.
11. Kun iya Tafsiri, wajen Hadisi
Kun gado Sallafawa.
12. Kai haka Inter-Science da [an-{asanci
A Adab kun burge kowa.
13. Har Nahawu da wajen karatukan Fiqhu
Akwai ku wajen }wa}walwa.
14. Ko a Balaga ma kuna da hazzi
Kun zarce sa’a da wawa.
15. Mai Insha’i ma yana yabo
Ya ce Rabbi ya }ara baiwa.
16. Ka ga a Tauhidi kuna da sheda
Ta yabo kuma ba ku zaguwa.
17. Ko ni ma na san Translation
Da kuke zai burge kowa
18. Ya Ala }ara wa ]iyan karatu
Da fahimta tai ta }aruwa.
19. Rabbi na ke ro}o ya kare sharri
A gare ku ya kau da damuwa.
20. Rabbi ka }ara wa ]iyan fasaha
Natsuwa, ka hana su shewa.
21. Rabbi ka }ara wa ]iyan ga ilmi
Aikinsu ya zam abin }awa.
22. Don kuwa ka ga yawan karatukan nan
Ba ya hana yin kururuwa
23. Surutu da yawan ka-ce-na-ce
Wannan sam ba ya misaltuwa.
24. {arya, cin-nama, hadin fa]a,
Zagin malumma da ‘yan uwa.
25. Gun surutu har da monita,
Ba wani mai iya tsawatarwa.
26. Kowa in dai babu malami,
Ba ya shiru, da]a ba ya zaunuwa.
27. Kai har ma ko da da malami,
Sai in teacher ya yi tsawa.
28. Kai ko da ya tsawata shiru bai yiwuwa
Sai an kururuwa.
29. Sai in ya zane su, ko ya koro wasu,
Ko ko ya han}urewa.
30. Kai wata ran ma sai da an ka zane kowa
Ba kwa tunawa?
31. Ai bulala an ka yi wa ‘ya’yana
Ran nan na ji damuwa.
32. Sai ka ji an ru]e hayaniya,
Ba wata mai jin ma ta kowa.
33. Sai ka ga mata sun yi }ungiyoyi
Sai gulma suke zubawa.
Sai gulma suke zubawa.
34. Har wani yin }asa ma ake da murya
Don dai tsabar iyawa
35. Kai wani loton in ta kai ta kawo musu
Har da su }yal}yalewa.
36. Sai ka ji an kece da dariya,
Har tafi, wasu har da fa]uwa.
37. Ko ka ga ‘yan mata da ]ammara
Sun kaure juna da kokawa.
38. Ran nan ma har sai da Jummala
Tab buga kan Larai cikin ruwa!
39. In ka ji an ru]e batu ake
Kallon fim da zuwa kalankuwa.
40. Sai ka ji an ce Abida }azama ce
Wai kuma ba ta auruwa!
41. Ko ka ji an ce ke Sa’a Wasila
Ta zarce ]iyan Kanawa.
42. Ai Lerawa sun fito da sabon fim ]in su
43. Ko ka ji an ce ran bikin Talai
Dan Asharalle ya ci kasuwa.
44. Ya buga ganga an yi cashiya
Har da uwar angon a yin rawa!
45. Ko ka ji Delu tana ta ralla }arya
Ba ta koda kulawa.
46. Sai ka ji ta ce saurayinta
Ai pilot ne ]an Larabawa.
47. Ba ya jin hausar garinmu
Wai shi daga Saudiyya yake zuwa!
48. Zu}i-ta-malle, babu ko kare
Wanda yake }aunar ta doluwa.
49. Ko ka ji Jummai na fa]a wa Laila
Cewa wai kin ga Sabuwa.
50. Kullum zagin ki take ta yi
Ta ce ba ki kula da ‘yan uwa
51. Ba ki da gata bak ki hankali,
Wai ke ce karya ta kasuwa.
52. Duk }arya ce don hadin fa]a
Allah raba mu da almurawa.
53. Ko ka ji an ce shegiya Habi,
Ta }i zaman aure a Zankuwa!
54. Ko ka ji an ce Allah tsine Malam Asgar
Sam bai da }yaluwa!
55. Ga shi da }wauro ba ya ba da maki
Kuma ba ya }yale kowa.
56. Ga shi ba}ar magana wajen shi
Tamkar jika gun Kattsinawa!
57. Ko ka ji an ce malamin Adab
Walla yana }aunar ki ‘yar uwa.
58. Ba ki ganin kullum yana yawan kallon
In da kike da zaunuwa?
59. Har ma ko da za ya amshi
Biro na aro, sai na ki Sabuwa?
60. Ke kin ca~a, kin haye, kina jin da]i
Da]a kin yi kasuwa.
61. Sai ka ga takun wawiya gaban malam
Yanzu yana ta canzuwa.
62. Sai far-far da ido, gwalangwaso,
Gun tafiya tamkar tana rawa.
63. In za tai magana ta lan}washe kanta
Ta ce “Malam ina zuwa!”
64. An zuga bera ta ~uge da shirme
Sunanta ku ji shi doluwa.
65. Ran da ake exams, anan na san
‘Yayana sun san cuwa-cuwa.
66. Yin }us-}us, le}e da }ifciya,
Don surutu bai misaltuwa.
67. Ka ga ~arayi ko kala-kala?
Har da takardu ma ake zuwa.
68. Ta boye paper cikin jaka
Ko a }asan bencinta doluwa.
69. Labaran ne ai suna da dama
To don haka ba su kirguwa.
70. Ka ga batun da na yo cikin halin ‘ya’yan nan
Na yawan kwakwalwa.
71. Tabbas ne, domin ko malamai
Duk sun yarda suna yabawa.
72. To haka ma shirme da nai ishara
Shi ma fa yana ta faruwa.
73. Ga ku da kwanya, kun kware a shirme
Kuma kun zarce na kowa.
74. Duk wani farko dole ne ya }are
Koda a daren da]ewa.
75. Ga shi kamar jiya ne muke a first term
Yau session za mu cim ma wa.
76. Kun yi halarci Allah yi wa
‘Ya’yan nan albarka da yalwa.
77. Mun yi zama dangi da ni da ku
Ba rikici kuma babu ]imuwa.
78. Sai dai tilas ne a sami nai laifi
Ko kuma kuskurewa.
79. Dangi don Allah ku yafe laifin
Da na yi muku kun ji ‘yan uwa.
80. Don ni kam ban ware ko guda
Na yafe kowa da kowa.
81. Sai ku ji tsoron Rabbana ku dage
Iliminku ya dosa }aruwa.
82. SS2 in kun ka je a can ma
Himmarku ta }ara ninkuwa.
83. Ya Ala sa Aljanna ce makomar kowa
A cikin mu ‘yan uwa.
84. {aunar ‘ya’yan nan nake ta yi,
Babu ragi kullum tana hawa.
85. Za na ji }unci ni a rai idan mun rabu
Na san zan ji damuwa.
86. Allah ji }an mu da ni da ku
Ya sa za mu haye ranar tsayawa.
87. Zan rufe wa}en nan a nan
Ina ban kwana a gare ku ‘yan uwa.
88. Na gode Allah da yan nufa
Nai wa}ar har }arikewa.
89. Na da]a mika salatuka
Ga Manzo jagoran Annabawa.
90. Tare da Alaye da ma Sahabbai
Su manya ne ga kowa.
91. Sai wata ran danginmu, Allah sa
Za mu game kafin kushewa.
92. Mai wa}en nan Asgari sananne ne
Gun dangi da ‘yan uwa.
93. Wannan ce ai gunduwa ta }arshe
Da a kanta nake rufewa.
12 ga watan Maris, 2002.
Zariya
No comments:
Post a Comment