Sunday, December 26, 2010

SAI WATA RANA

SAI WATA RANA

A shekarar karatu ta 2003/04 na rike aji shida na babbar sakandaren koyar da ilimin Larabci da Addinin Musulunci ta Abubakar Gumi da ke Zariya bangaren mata a matsayin baban aji.

Bisa al’adar makarantar akwai bikin yayen ]alibai da ake yi wa masu fita a }arshen kowace shekarar karatu bayan kamamla jarabawar }arshe, duk wanda aka bai wa baban irin wannan ajin dole ne ya yi ruwa ya yi tsaki don ganin cewa bikin ‘ya’yan nashi ya yi armashi.

Akan gudanar da abubuwa iri-iri a wajen bikin na wuni ]aya, kama daga kan jawabai, wasannin kwaikwayo, lacca ko wa’azi, walima da dai sauransu.

To shi ne ni kuma na rubuta wannan wa}ar a daren ranar da za a yi bikin na ba ]aya daga cikin ]alibai masu fita ]in, sunanta Hajara AbdurRahman Muhammad ta rera wa}ar a filin wannan taro, abin da ya jawo da dama daga cikin ]aliban suka bar dandalin taron suna share hawaye.

Wa}ar kwar biyu ce. Na kuma yi ta ne da wani karin Larabci wanda ake ce da shi Hazaj.

A sha karatu lafiya


1.   Inai muku sallama dangi
      Ku amsa min ma}ala ta

2.   In mi}a yabo ga manyana
      Iyayena mafifita

3.   Wa]anda su kai ta koya min
      Karatu har zuwa na fita

4.   Iyayena a gaishe ku
      A aikin naku ba wauta

5.   Dukan wahala fa sun jure
      Wajen koyar da makaranta

6.   Kuna koyar da ‘ya’yanku
      Dukan fanni su ilmanta

7.   Kuna ha}uri da shirmenmu
      Da duk aiki na mai wauta

8.   Kuna “Allah ya shirye mu”
      Kuna adu’a da yin kyauta


9.   Ha}i}a kun jihadin ku
      Ilahi ya sa ku nanata     

10. Ya sa ku cika da imani
      Ya sa ku cikin ma’azzurta

11. Ya ]aukaka martabarku duka
      Ya sa ku zamo mafifita

12.  Ina ro}on iyayena
       Ku yafe kure da ma wauta

13.  Da ni da dukan sa’o’ina
       Aji shida wanda za su fita

14.  A ban kwanan da za na muku
       Hawayena suna ta fita. 

15.  Saboda ina ta alhini
       A kan rabuwar da ba mafita

16.  Ina kuke ‘yan uwa na aji
       Kiranku nake da muryata


17.  Ina so ne ku yafe ni
       Ku rangwanta ma heart ]i ta

18.  Mu yayyafe wa junanmu
       Mu ]au hali na manyanta

19.  Ku san cewa a yau ]in nan
       Batun rabuwar mu ba mafita

20.  Hala ha]uwa ta ]an yi wuya
       Da }yar ne ma ta maimaita

21.  A gai da Principal baba
       Nasiha mun ji da]inta

22.  A gai da Munir yana son mu
       Yana aiki na jarumta

23.  Da shi da Kabir Mahaifinmu
       Da Uncle R. da Barista

24.  Abu Jummai a gaishe ka
       Sa’annan har da Hedmasta


25.  Da Malam Salisun Higher
       Da duk sauran mahallarta

26.  Aliyu Rufai gaishe ka
       Da sauran masu yin bauta

27.  Na safe da malaman yamma
       [iyarku tana ta zancenta

28.  Hakan nan ‘yan uwa dangi
       [iyan Higher ta ‘yan mata

29.  Ina cewa da ku bye-bye
       Da alheri nake fata

30.  Kuren da na yi ku yafe ni
       Ku ]an daure ku gafarta

31.  A wanye lafiya dangi
       Cikin aiki na jarunta

32.  Salamu alaikumu na fa]a
       Ku amsa don na ]an huta


33.  Ma-faa-ii-lun Ma-faa-ii-lun
       A nan zan }are wa}ata.

13 ga watan July, 2004.

 Zariya











                                      

No comments:

Post a Comment