tsuliyar dodo
Malam Ja’afar Mahmud Adam[1] da ke Kano shahararren malami ne, masanin Al}ur’ani da Sunnah. Ya }ware wajen wa’azin Sunna, tafsirin Al}ur’ani mai girma da maida martani ga a}idojin ‘yan bidi’a da shubuhohinsu.
Wannan irin salo na wa’azi da karantarwa irin na magabata ya jawo mishi shahara da farin jini a wajen masoya Sunna. A ]ayan ~angaren kuma ya jawo masa ba}in jini a wajen }ungiyoyi na ‘yan bidi’a tun daga kan ‘yan ]ari}u da ‘yan shi’a da dai sauran mabiyan wasu hanyoyi da suka sa~a wa Sunna.
Wannan ya jawo wata }ungiyar mawa}an mandiri a Kano wadda ke kiran kanta da sunan Ussha}un Nabiy suka yi wa}a suka zambace shi a ciki ta hanyar zage-zage da yi masa sharri iri-iri. Ba don komai ba sai don ya }ure malamansu, ya wargaza kayan tiredar damfararsu.
Wannan wa}a da suka yi sun yi ~atanci }warai a cikinta, da na saurare ta a kaset hankalina ya tashi, sai na ce da wani abokina mai suna Muhammad Nura Yahya ya kamata a mayar musu da martani.
To shi ne fa muka zauna muka sake sauraron kaset ]in daga nan muka du}ufa wajen mai da martani akan abubuwan da suka farfa]a.
Mun yi amfani da karin wa}ar da suka yi amfani da shi, wanda asalin sa karin wa}a ne da wasu masu mawa}an siyasa suka yi amfani da shi can wani lokaci da da]ewa, tun lokacin jamhuriya ta biyu.
Wa}ar tana da layi biyar-biyar da amshi. A nasu amshin cewa suke yi
Jafaru mun gane nufinka
Ba gina addini kake ba
Mu kuma sai muka ce
{arya ‘yan Ussha}u ke yi
Jafaru ba bidi’a ya ke ba
Ga wa}ar:
1. Ya Allah sarkin iyawa
Mai kyauta mai kyautatawa
Kai ke rayawa, kashewa
Bayarwa hakanan hanawa
Allah ba tamkar mutum ba
2. Allah kai ]ai ni nake ro-
}o, ka da]o Allah ka }aro
Min hikima baiwa na tsaro
Wa}e ba shakka da tsoro
3 ’Yan ussha}u ku daina }wange
Kun wa}a kun zage-zage
Mu kuwa damtse za mu zage
Kan muku raddi za mu dage
Ba kuma tare da karkata ba
4. ’Yan ussha}u kuna da wauta
Har kun kai matu}a a kanta
Kun taba Jafaru za ku sha ta
Ba}ar Magana, don mun iya ta
Amma ba sharri muke ba
5. Malam Jafaru kun ka sara
Kun mai sharri har fitsara
Ga kuma }arya kun sharara
Kun saki layi kun asara
Ku ba ‘yan kirki ba ne ba
6. Kun tono dubura ta dodo
Kun yi tsirara babu wando
Sharri da man kun yi gado
Gun Fir’auna da masu dodo
Ba kuma bin Sunna kuke ba
7. Jarafu malam ne fa babba
Ba ku da tsara gun shi duba
Ya }ure malam na ku babba
Shi ne sai kuka ]auki gaba
Sai aikin sharri da zamba
8. Ga shi fasihi ga karatu
Shi yas sa shaihi ya zautu
Ya }ure duk wani mai gulatu
Da ma dai kun nemi shantu
Don ba addini kuke ba
9. Malam Jafaru ya yi zarce
Ya zam babba abin kwatance
Kai ba ma a Kano ba na ce
Duk a }asa ya zam fitacce
Sannan shi bai fariya ba
10. Kowa na son gayyatar sa
Yai wa’azi da karatukansa
Bauchi da Yobe suna ta son sa
Ana ta yaba masa kan kiransa
Zuwa bin Sunnar [an Suwaiba
11. Ban da [arikawa ~atattu
Don su ba sa son karatu
Ba sa }aunar mai karatu
Su dai bar su ki]a da fatu
Ba }aunar Manzo suke ba
12. Jafaru ]an Mamudu sannu
Ka tsone musu ‘yan idanu
Don kan Sunna kai ka zaunu
Su bidi’a suka sa wa hannu
Ba son mai Sunnar suke ba
13. Ka san Sunna ka karanta
{ur’ani, kuma ba ka maita
Ba ka yin fahari da wauta
Sunna tabbas ka rike ta
Mun gaishe ka bama bari ba
14. Ka koyar da Kano dukanta
Har da na Barno ha]a da Kaita
Zariya ma duka mun fahimta
Kowa ya san kai bajinta
Kan tafsiri ba ba’a ba
15. Jafaru babban malami ne
Shi a ]abi’u kamili ne
Gun wa’azin Sunna gwani ne
Ya wayar fa da kan mutane
Musulmi, ba wai ‘yan ki]a ba
16. Don ya ce Sunnar Ma’aiki
Zai kare, ku kun ka soki
Wannan harka, kun ka ]auki
Gaba, kun zagi na baki
Wai ku sam ba ku yarda yai ba
17. Komai za su fa]a wa Malan
Na sharri ai mun san hakannan
Yahudawa danginsu daman
Sun yi wa Musa ]a ga Imran
Ba mamaki za mu yi ba
18. Sawun arna kun ka taka
Sun wa Manzo ma a Makka
Sharri, }age da nuna hauka
Kuma shi ne kun ka dauka
Sam ba ku sha bambam da su ba
19. Sun san in Sunna ta zaunu
Duk wata cuta za ta tonu
Sai jama’a ka ga sun idanu
Sun zama wayayyu sanannu
Ba dolaye ra}uma ba
20. Malam komai za su ce ma
Bar su da Allah zai gwada ma
{arshe yaya za su koma
Don tabbas sai sun nadama
Wanga batu ba kuskure ba
21. Kun zagai mu mun tare mai
Ya fi gaban shehi a komai
Ciwon ru]ewa ya sa mai
Ba tsaran ku ba ne a komai
Jafaru ba bidi’a ya ke ba
22. ’Yan ussha}u ku ba ni amsa
Don mene ne ba ku son sa
Sunna ba kwa son ya wasa
Wai ko addini na wasa
Kuke, ba wai Islam kuke ba?
23. Ko don ya tono asiri
Na shehunnan }arya da sharri
Macuta ‘yan sane da tsari
Duk aikinsu fa ba na khairi
Ba aikin Allah suke ba
24. Don haka yau ni ga ni ga ku
Zan fa]i halin shaihunanku
Zaluncin da suke da tsurku
Neman mata har da shunku
Koko ku ba ku san hakan ba?
25. Ka ga a addinin [arika
Shaihi zai zina ko da jaka
Zai iya yin hu]uba ta shirka
Wai haka ]in daraja ya dauka
Yin haka ba shegantaka ba
26. Akwai cire gashin munkirawa!
Su suka furta suna cirewa
Sadda suke son shakatawa
Ba sharri a batun ga nawa
Sannan ba }azafi nake ba
27. Ko ka ji an ce wa mutane
Wai can Allah ne a zaune!
Komai gun su Ubangiji ne!
Ni na san wannan ~ata ne
Ba a cikin Islamiya ba
28. Allah [ai ne bai da tamka
Bai da uwa, kuma bai da jika
Ba mata haka bai da kaka
Yana bisa Arshi ban da shakka
Na kuma san ban kuskure ba
29. Kan Arshi Allah yana nan
Shi ya fa]a mun yarda san nan
Kun ce }arya duk bayanan
Kun mur]e ma’ana hakan nan
Ba kuma kan hujja bane ba
30. Don haka dai Allah Guda ne
Na sama kan Arshinshi shi ne
Ai ya fa]a har gu bakwai ne
Amma daidaitonshi shi ne
Ban san yaya yai hakan ba
31. Ka ga ]arikawan ga }atti
Sun je sun }ero salati
Sun ce kowa yai salati
Na manzo baba gun su Fati
Lada nai ba zai yawa ba
32. Salatul fatin nan fa taku
Kun ce lada za ya ninku
Ga wanda yayi ta cikin batunku
Ta zarce wahayi a bar ku
Da kafirci ba }an}ani ba
33. Zindi}anci kun iya shi
Kafirci kun tallata shi
Iskanci kun ha~~aka shi
Shashanci ku kambama shi
Ba son Annabi ai ku ke ba.
34. Girman Manzo kun ka ]auke
Kun ba wawaye ba}a}e
Sai }arya sai sa}e-sa}e
Sharri, ba wani no}e-no}e
Ba aikin kirki suke ba
35. Masu ki]a a wurin ibada
Ga su da wa kabari sujuda!
Sannan kowa ya fa shaida
An cinye makara sa’adda
Nasiru yam mutu ba ba’a ba
36. T.J. shehi ne na zamba
Wai shi bai tsoron azaba
Ka ji mutum da hali na dabba!
Ga jahilci ba ka]an ba
Bai iya yin ko da ]igon ba!
37. Tijjanin ga ma}aryaci ne
Na rantse shi makiri ne
Dan 419 ne ku gane!
Ai }arya ya ka wa mutane
Ba wai bin Manzo yake ba
38. Nairorin jabu ya buga su
An kama shi yana buga su
Ya sha bulala a kan su
To ya za ai wai mu gamsu
Da cewa ba mugu ba ne ba
39. Wai wannan shi ne waliyyi
Mai cuta babban gabiyyi
To Jafar sam bai da koyi
Da masu irin halin sha}iyyi
Ba kuma zai mai rangwame ba
40. Wai wannan shi ne abin bi
Waye zai bi ba}in garibi
Ya sa ka kana yawo da carbi
Sannan ranar yin hisabi
Ka tashi a layin masu gaba
41. Kun ce T.J. malami ne
Mu kuwa mun ce jahili ne
To ku taho bainar mutane
Ku kawo hujjoji a gane
In ba }arya ce kuke ba
42. Ku kawo sunayen rubutu
Na littafai da ya yi fitattu
Da wanda ya koya mai karatu
Da ]alibban da ya yi wa satu
Ba su Harazimi ‘yan tasha ba!
43. Shi kuwa wancan {adirawi
Nasiru bai son Kalarawi!
Allah ji }an shehi Kanawi
Babban malam {alarawi
Bai ma ‘yan bidi’a ragi ba
44. Nasiru wai me za ya ce ma?
Cikin Ramalana ya zo da yamma
Gurasa tai ya ri}o a dama
Cikin jama’a, ba wai ba’a ba
45. Dangi za na yi ]an bayani
Na shehi [ahiru ]an Fulani
Kun san shi sam bai tunani
Sai fahari sai gani-gani
Don ba jin kunya yake ba
46. Alfahari da yawan karatu
Sai }aryar da ta sa ya zautu
Ga maula a wurin fitattu
Masu ku]i na giya ~atattu
Kun ]auka ba mu san hakan ba
47. Ku iliminku na yaudara ne
Kun yi karatu kun yi zaune
Ba kwa koya wa mutane,
Muridanku, sai dai ]iya ne
Ke more ilimi na Baba!
48. Malammanmu na al’uma ne
Ba sa tsubbu ba su binne
Ba kuma sa cutar mutane
Ba sa duba ba su zane
Don mai yi ba zai haye ba
49. Ku manufar ku a daina yi ne
Aikin tsamowar mutane
Kansu dake a cikin tukwane
Na jahilci da yawan bata ne
Shehunnanku ba sa iya ba
50. Sai cutar jama’a kuke yi
Kun hana bayi yau su koyi
Sunnar Manzona Nabiyyi
Wai ku sai }aunar waliyyi
Na }arya ba mai hankali ba
51. Don ko waliyyan damfara ne
|arayin imanin mutane
Su da su Pastor ‘yan uwa ne
Su }wace ku]in mabiya mutane
Ko ba su san cuta a ke ba?
52. Kun saki Allah kun ri}e su
{attin banza ma irinsu
Me suka tanadda wa kansu
Balle ku ‘yan kore gun su
Anya ba hauka kuke ba?
53. Kun mana sharri kan waliyyi
Kun ce ba ma son waliyyi
Wai har mun ce ba waliyyi
To duk }arya ce kuke yi
Don mu ba arna ba ne ba
54. Mu mun yarda da auliyawa
Na gaske na sosai masu baiwa
Wa]anda ka bin Sunna da tsaiwa
Kan addinin Annabawa
Wannan tabbas ban musa ba
55. To amma ku auliyanku
Wa]anda ku kai wa na]i da kanku
Tijjani ko Kaulahinku
Mummuna da kama ta tunku
Duk ba bin Allah su ke ba
56. Ka ji mutane kangararru
Wanda suke da yawan dabaru
Sun iya sa fitina ta faru
Ta shirka, Allah wadan fujaru
Don ba addini suke ba
57. Kafircinku yawa yake yi
{ur’ani ku ba ku koyi
Da shi, Allah wadaran ~arayi
Dake sace Tauhid na bayi
Su ba tsira za su yi ba
58. Sunnoni duk kun aje su
Sai iskanci ba ku son su
Da izgilanci ma a kan su
Ranmu Musulmi ya fa sosu
Mun san ba Islam kuke ba
59. Malam Jafaru ya }ure ku
Ya }ure }aryar malumanku
Ya katse carbin shehunanku
Ya ture rawanin su tunku!
Har malafar duka bai bari ba!
60. To shine duk kun ]imauce
Kun gigice kun makance
Duk kun ru]e kun fukace
Kun yi kamar motar itace!
Don ba son Allah kuke ba
61. Shehunnanku gaba ]ayan su
Bayan Jafaru ya }ure su
Gun Sarki suka kai batunsu
Wai a hana shi ya bar ta~a su
Sarki ba wauta ya ke ba
62. Malam gun Sarki ya je shi
Shi da mutum ]aya yar raka shi
Su ko bila-adadin akan shi
Ya dosa ruwan aya da kan shi
Yak }ure dokin masu zamba
63. ’Yan ussha}u kuna za}ewa
Wai har Jafaru za ku ce wa
Za ku buge shi ku daina shewa
Zan muku warning ba da]ewa
Ba da raha kuma za na yi ba
64. In har kun cika ‘yan ta’adda
To bisimillah ‘yan ta’adda
Wanda ya fasa Rabbi mai da
Min shi siriri ya sanda
Ko ya gaza bai kai hakan ba
65. Tunku]e hular Jafarun mu
To daidai yake mu a gun mu
Da ran shehunnai masu jurmu
Yanzun ba sauran ragi mu
Ba tsoron ta-kife muke ba
66. Duk }azafin da kuke biyawa
Kun ga alamu ne na cewa
Ku Fir’auna kuke biyewa
Ko ko Abu Jahalin kuke wa
Aiki, ku ba ku san hakan ba
67. Mun gama gano lungunanku
Na cuta, zamba da damfararku
Don haka yau sai kui ta kanku
Ku kama sana’ar ci da kan ku
Ba ku tsaya maula kawai ba
68. {arya, sharri kun wa Manzo
Malamman Sunna da kwazo
An musu wai don sun bi Manzo
Don haka kar ku bari ku cazo
Sababbin sharri na gaba
69. Ni ban }aunar ma ku fasa
Wa}ar sharri kar ku nisa
Kar ku bari mu za mu amsa
Duk kule ai cas na jiran ta!
Ba za mui muku rangwame ba
70. Don kuwa mun rantse da Allah
Duk wani mai warin jahala
Wanda yake raini ga Allah
In ya kuma sai ya yi }walla
Ba zai huta duniya ba
71. Maulidi bidi’a kuke yi
Domin Manzona masoyi
Bai ta~a yi ba kuna ta koyi
Da ‘yan coci, sune su ke yi
Bai da shiga gun ]an Suwaiba
72. Ko [an Fodiyo ya rubuta
Cikin Ihya’u mun karanta
Amma don tsaba ta maita
Kun }i ku daina mun fahimta
Ba }aunar shiriya kuke ba.
73. Hujjar nan da kuke kafawa
Kui ta sakin baki da cewa
Ai hujja ita ce hanawa
Ta Annabi, dangi kun ji wawa!
Ai hujja ce kanka babba
74. Don ko Annabi ya hana mu
Yin sababbin ayyukanmu
Wanda dalili ba shi gun mu
Ya shiga “iyyakum” ku duba
75. Tabbas bege ja’izi ne
Shi ko guluwwi karkata ne
Mu mun tabbata ai ~ata ne
Amma duk kun toshe kunne
Don ba son ha}}un ku ke ba
76. Cin doki tabbas halas ne
An ci gidan Manzon ku gane
Ni na san ku jahilai ne
Don ko karatun ]an ka]an ne
Ba wani mai zurfi ba ne ba
77. Don haka mu kam mun ci doki
Nama mai da]i a baki
Kai ma in da ka ci doki
To da ya sanya ka ]oki
Kai ta zuba ba ka ko sani ba
78. Doki naman Annabawa
Babu rabo gun {adirawa
Ko kuma ku Tijjaniyawa
Kai duk ]an iska da wawa!
Doki ba naman shi ne ba
79. Ni na san hauka kuke yi
Tun da Tahajjud ba ku koyi
Wai jam’i bisa me ake yi
Ga hujjoji nan na koyi
Da aikin Manzo ]an Suwaiba
80. In dai har kun san karatu
Duba Buhari kar ka zautu
Kar ka biye wa ki]a da shantu
Mandiri da kuke ta ~a~atu
Ba addini ba ne ba
81. Sannan Manzona mutum ne
{ul innama ana bassharun ne
Mislikumu, malam ka gane
Cikin Kahafi, Fusilat a can ne
Za ka ka duba ba fa]a ba
82. Shi daraja tai ta yi zarce
Ta fi gaban a tsaya kwatance
Don kuwa ba wani ]a na macce
Wanda ya kai shi wajen kwatance
Ko a ina shi ya yi babba
83. Ku sufaye nai kiran ku
In har hujja ke gare ku
Kan kare shegantakarku
To ku taho ku baje batunku
Don mu ba tsoro muke ba
84. In dai ba tsoro ku ke ba
In kuma ba }arya ku ke ba
Ku kawo shehin naku babba
Ya zo a kara ba wai ki]a ba
Jafaru ba tsoro yake ba
85. In dai har hujja ta sosai
Za a kafa mana ai fa to sai
Ai ta ruwan aya, hadisai
Ingantattun nan na sosai
Ba zagi da ashariya ba
86. Bisa tafsirin Annabinmu
Ko na Sahabbai malamanmu
Su magabata ne garemu
Manyan dattawa a gunmu
Ba tsofaffin ‘yan tasha ba
87. Kai jama’a anya da Allah
Cikin aikin nan na su kalla
Kullum sai zagin Izala
Wai don ta zamto fitilla
Ba hanyar cuta ba ce ba
88. Ja-in-ja daga yau ta }are
An }ure }arya babu bore
Ba sauran yawo na kore
Tuba ku bar }arya ku tare
Kan Sunna ba karkata ba
89. Jafaru ya }ure malumanku
Mu kuma mun }ure baitukanku
Ya}in maimai mun yi kan ku
Sunna ta baje teburanke
Ba daraja yanzun ku ke ba
90. Ya Allah Sarkin sarauta
Tona asirin masu ~ata
Tauhidin bayi da maita
Ta cin Sunnar baban su Binta
Masu ~akar aniya ta zamba
91. Wannan tarin baituka ne
Mun yi wa masu batun kawai ne
Masu nufin kore mutane
Ga bin Sunnar kakan Hasan ne
Shi ne Manzo ]an Suwaiba
92. Mu mun shirya ba mu tsoro
Ba ja baya ku je ku tsaro
Sai a kara don babu tsoro
Rago ya yi wuya ga toro
Jafaru ba tsoro yake ba
93. Nan ne za mu tsaya mu bar ku
Don ku tsaya ku tuna da kanku
In udtum udna a kan ku
Mui ta fa]in shegantakarku
Ba za mui muku rangwame ba
94. Ga tanbihi nai gare ku
Ku daina fa]in }arya da tsurku
Ku bar ]aga tutar masu shunku
In kuwa kun ce ku a bar ku
Ba za ku ji da]in lahira ba
95. Bayan Jafaru Malaminmu
Ga wasu manyan malamanmu
Shehunnai masana Ulumu
Wanda muke }auna a ranmu
Tun da suna bin ]an Suwaiba
96. Za mu ziyara ne Kanonmu
Don mu ga Dokta Amadunmu
Dattijo mai kyau da gemu
Dan Ibrahim ka aza mu
Kan Sunna ba }ir}ira ba
97. AbdulWahabi a gai da babba
Sannu da aikin karya zamba
Ka zama gwarzo mai takubba
Na sare kan bidi’a ku duba
Bai mata sauki ko ta}i ba
98. [an Usman liman na Kundi-
la, ka zamto mai jihadi
Na tallan Sunna babu haddi
‘Yan bidi’a kuma sui ta raddi
Za su gaza ba za su kai ba
99. Sai na sako Malam Aminu
Na Daurawa kai ma fa sannu
Ka tsole musu ‘yan idanu
Sun zama ‘yan tanka da shanu
Allah da]o ilimi da haiba
100. Za mu tsaya Zazzau mu gaisa
Da Auwalu Albanin matasa
Wanda gaba ]aya rayuwarsa
Yai wa}afin ta a kan ya wasa
Sunnar Manzo ]an Suwaiba
101. Mu kam Zazzau mun yi sa’a
Don kuwa da har ma da shi’a
Amma Auwalu hina ja’a
Sai ya diran mata kaifa sha’a
Bai }yale ta ta kai tudu ba
102. Ga malam Ahmad na Kauru
Shi ma yai aiki tu}urru
Kan ya ga Sunna ta fa gyaru
Malam ya sha kafsa daru
Da ‘yan bidi’a ba }an}ani ba
103. Malam Garkawi na biya na
Wanda ya ke a garin Kaduna
Saboda kiran shi a tsai da Sunna
Ko daga jin sunan shi auna
Ba zai wa bidi’a ragi ba
104. Bello na Yabo ina yaba ma
Ko ma}iya sun }untata ma
Bayyana ha}}un ba ka }yama
Ba ka ragi ko za su far ma
Ba tsoron ta-kife ya ke ba
105. Ku mabiyan Sunna kiran ku
Nake kan girmama malamanku
Ku kare mutuncin malamanku
Kar ku sake ku saka su tasku
In kuma kun }i ba ta yi }yau ba
106. Kan ilimi kowa ya dage
Mui maza kan ilimi mu zage
Damatsa kar mu sake mu toge
In ka }i ko sai waige-waige
Da sun ritsa ka ba ka iya ba
107. Rabbi tsare mu ga kama shirme
Ko mu bi }arya ko mu zarme
Allah Rabbi ka sa mu kame
Mu bar bidi’a ko bin kurame
Bebaye maciya na gumba
108. Wa}ar nan da muke ta yin ta
‘Yan ussha}u ku dosa bin ta
Allah sa dai kun fahimta
Ba da]a ~arna za ku yi ba
109. Wanda su kai wa}ar ga sune
Asgaru ]a ga Abubakar ne
Nura Yahayya ]a ga Hanne
Masu kwatanta biyar Salaf ne
Ba kuma alfahari mu ke ba
110. Ga adreshin masu wa}a
In ka zo Zazzau a kai ka
In da a ke sallah ya Makka
Markazu nan ne za a kai ka
Mu ba ~oyayyu bane ba
17 Ga watan Disemba, 2003
Zariya.
[1] Allah ya ji kan sa y a ba shi darajar shahada! A ranar Juma’a 13 ga watan Afrilun 2007 wasu ‘yan ta’adda suka shigo masallacin gidansa a Dorayi, Kano , suka harbe shi da harsashin bindiga yana limancin sallar asuba. Ya rasa rayuwarsa a sakamokon wannan harbi. Allah yatona asirin wadannan ‘yan ta’adda ya tozarta su. Amin .
No comments:
Post a Comment