Sunday, January 2, 2011

TA ZARCE

TA ZARCE

Wannan wa}a halin da }asarmu ta shiga a lokacin ana ta ru]anin siyasa da Tazarce ne dalilin da ya sa na tsara ta. A nawa ganin akwai wata irin tazarcen da ke jiran kowa, don kuwa dole ne mutum ya zarce lahira.

Sannan ga alamomin tashin duniya nan sun cika gari, don haka sai na wa}e wa]annan alamomi na kuma kira wa}ar da suna Tazarce.

Wa}ar }war biyar ce. Karin ta na Larabci ne ana ce masa Hajaz.

Ga ta kamar haka

1.  Da sunan Rabbi zan fara
     Batun nan yau da zan tsara
     A wa}en nan da zan rera
     Ina ro}o ya ban fikira
     Na }are babu sarewa




2.  Salati gun RasululLah
     Da Alaye mutan falala
     Sahabbai masu son Allah
     Da sauran masu bin Allah
     Nake yi ba ni ratsewa


3.  A rannan na yi wa}ata
     Batun da na yo na ]alibta
     Da harkoki na malanta
     A yau ma za na fafata
     Bayani za ni fe]ewa

4.  Jawabin yau da zan furta
     {iyama kan alamunta
     A yau wa}ar da zafinta
     Kamar a wuta na ]ebo ta
     Ku saurara ku bar shewa

5.  RasululLahi ya koyar
     A kur’anin da yak koyar
     Da Sunna fassarar ayar
     Gaba ki ]ai da yak koyar
     Jawabi babu ratsewa

6.  A da can wai da sa~ani
     A kan shin za ta riske ni
     Wa]ansu suna da tsammani
     Wa]ansu ko su suna da sani
     Akan sam babu fasawa


7.   Wa]ansu ko har sukan furta
      Su ce sam har su nanata
      Su ce in ma fa ta zo ta
      Suna da rabo na manyanta
      Da]ai wai ba su ta~ewa

8.   Wa]ansu su ce ba zai ai ba
      Wa]ansu su ce da tababa
      Musulmi ko suna a gaba
      A gun su ba za a fasa ba
      Na Allah ba ya }arewa

9.   {iyama babu fasawa
      Hisabi za a wa kowa
      Bala’i har da ru]ewa
      Suna auka wa ]an kowa
      A rannan babu warewa

10.  Muhammadu Annabin tsira
       Alamominta ya jera
       Wa]ansu a yau ku saurara
       Ciki yanzun ko zan rera
       Bayanin ba ya datsewa


11.  Alamomin iri biyu ne
       Akwai manya da ‘yan }anne
       Wa]anda sukai ta sharhi ne
       Da niyyar don a gaggane
       A don haka sun ka warewa

12.  {ananan za ni farawa
       Da na ~ata koko sarewa
       Ku gyara ban da basarwa
       Idan kuwa kun }i gyarawa
       Gaba ]aya za mu ta~ewa

13.  Ina fatan bayanina
       Na yau ]in nan da za na gina
       A gane har a ]au izina
       Sa’annan kun ji dangina
       Ga hujja za ni mannewa

14.  Sarauta in ta fara yawa
       Mutan birni da }auyawa
       Suna da sarakuna kowa
       Sarauta ba a yin rowa
       {iyama ce ta ke zowa


15.  Yawan mata cikin birni
       Da }auye in da duk ka sani
       Da ka le}a da ka ga zani
       Alama ce da ke nuni
       Akan mun doshi }arewa

16.  Da gasar jera benaye
       Ga masu ku]inmu huntaye
       Da zalunci da son yare
       {abilanci da tawaye
       Bala’i ba ya }arewa

17.  Da ha’inci cikin ciniki
       Yawan noma na mamaki
       Da yin kiwo ku sa baki
       Mu ro}i Ubangiji Sarki
       Ya sa mu haye da dacewa

18.  Sa’annan yanzu {ur’ani
       Ku duba ko ko ba ku gani
       Karatu nai cikin birni
       Da kauye rangwamen dini
       A yanzun walla ya yi yawa


19.  Alama ce da ke cewa
       Idan {urra’u sun ka yawa
       Da malanta ta daina yawa
       {iyama ce ta ke zowa
       Ha}i}a ta kusan zowa

20.  Da fajirci na ‘yan mata
       Tsiraici yau suke maita
       Ta sanya skirt ya matse ta
       Ta je aka }ona gashinta
       Jahannama za ta zarcewa

21.  Suna ta fita tsirararsu
       Muhammadu ya la’ance su
       Ya bayyana duk makomarsu
       Jahannama za ta kar~e su
       Sira]i ba su haurewa

22.  Mutane masu bulala
       A ba su ku]i su ]an tsula
       Amana ta zamo matsala
       Ana sakaci da yin salla
       Jihadi ba a jurewa


23.  Masifu har da ma fitina
       Kamar ya duhu suke nuna
       A kullum ka ga mummuna
       Hakannan ba a son Sunna
       Farashi ba shi saukowa

24.  Da ya}o}in }abilanci
       Da ma sha’a da iskanci
       Da arna masu makirci
       Suna auka wa musulunci
       Alama ce ta }arewa

25.  Fari da giya mabambamta
       Wajen sunanta an furta
       A birkice ko a bambamta
       A yau zina an halasta ta!
       Haramun ba a }yalewa

26.  Da malumman cikin fada
       Wa]anda da]ai sukan ba da
       Hukunci don mutan fada
       Su ba su gida da ‘yar Honda! 
       Zuwa Haji ba shi yankewa


27.  Shari’a ba a ko }auna
       Mutane ba su son Sunna
       Ku]i dai ]ai a ke kauna
       A kan su mutum ya kan }una
       Ya daure ba ya sosawa

28.  Mutum wai sai ka ce jaki
       A ce shari’a sa raki
       A ce Sunna ya sa baki
       Yana cewa da mamaki
       Shari’a wai ya ce yawa

29.  Sa’annan ga a}idoji
       Na ‘yan bidi’a suna caji
       Suna garari da karaji
       Abin sam ba nufin canji
       Mu tashi mu nemi gyarawa

30.  Da manya masu zalunci
       {anana masu fadanci
       Suna zuga ‘yan ta’addanci
       Tazarce don munafurci
       {iyama za ta zarcewa


31.  Da cuta tai yawa a gari
       Kamar Sida tana garari
       Tana kashe har da masu gari
       Da ’yan mata ado na gari!
       Samari ba ta }yalewa

32.  Malariya har da ma olsa
       Lamoniya ma tana ta kisa
       Talauci na ta bun}asa
       Musulmi ya kamata mu sa
       Kulawa ban da ta~ewa

33.  Da dutse na amai na wuta
       Mutane sai yawan mita
       Nasiha ba su ma yin ta
       Sa’annan ba su }aunarta
       A don haka ba su gyarawa.

34.  A yanzu muna tazarce ne
       Tazarcen ai }iyama ne
       A don haka sai mu gaggane
       Bayanin nan larura ne
       Da fatan za mu ganewa


35.  Alamomin suna da yawa
       A don haka ka ga bai yiwuwa
       A ce duka za a jerowa
       Bu}ata ta wajen kowa
       Ya sanya ido na ganewa

36.  Tsaya in zana manyansu
       Wa]anda idan fa an gan su
       {iyama ce a bayansu
       Tsaya ka ji zan karanto su
       Ilahi ya ba mu dacewa

37.  Da jagora na ‘yan iska
       Su Dujal babu }yan fuska
       Yana da wuta saboda haka
       Ciki yaka sanya wanda suka
       Kasance ba su yarjewa

38.  Da Isa za ya dawowa
       Ya ce da Mishan da Romawa
       Su yarje wa Musulmawa
       Ku daina ku Kirastawa
       Ku daina halin Yahudawa


39.  Muhammadu ya fa]a Mahadi
        Yana zowa da tajdidi
        Ya mai da }asa ga tauhidi
        Sa’annan Dabatul-Ardi
        Tana nan za ta dawowa

40.  Da Yajuj za su zo su ma 
       Da rana ta fito yamma
       Da {ur’ani a }arshe ma
       Gaba ]aya za ya tashi sama
       Da]ai sam ba ya dawowa

41.  Da zarar an tu}e a haka
       Musulmi za su sha iska
       Da sun sha}a su bar harka
       Gaba ]aya ban da ‘yan iska
       Akan su fa za ta }arewa

42.  Muhammadu Annabin khairi
       Ya ce su ne mafi sharri
       Tana riskar su babu shiri  
       A ranar ka ga jariri
       Da gemu za ya tsofewa


43.  {iyama in fa ta tashi
       Bala’i za a ninka shi
       Bayani nai ku ban bashi[1]
       A nan gaba za na kawo shi
       Da ikon Rabbi mai kowa

44.  Alamominta ka ji su
       Ina fatan ka gane su
       Ka san cewa da damarsu
       A tuntuni an fa gaggan su
       Mu ]au izina da gaugawa

45.  Jama’a sai mu dau hadani
       Mu daina jira na tsammani
       Mu tuba mu kama addini
       Jihadi ma mu ba da jini
       La’alla mu sami haurewa

46.  Gafurun Rabbi yafe ni
       Alimu Ubangiji ga ni
       Ka ban tsira da addini
       Ka sa Manzo ya cece ni
       Zuwa Aljanna son kowa

47.  Ina ro}o wajen Allah
       Ya }ara wa RasululLah
       Aminci har da ma falala
       Jama’ata ku }ara kula
       Wajen Sunna da jurewa

48.  A nan ni za ni ]an huta
       {asidar nan da nai bita
       Ku gane ni nake fata
       Sa’annan sai mu san mafita
       Ha}i}a sai da dagewa

49.  Inai muku sallama dangi
       Ku amsa kun jiya dangi
       Ku tashi ku daina tagagi
       Ku daina biye wa }adagi
       Bala’i ya kusan zowa

26 ga watan Fabrairu, 2001.

Zariya.



[1] Wa}ar za ta zo a can gaba in Allah ya so. Sunanta Mimiyyar {iyama 

No comments:

Post a Comment