AIKIN TELA
A tsakanin shekarun 1998 zuwa 2002 na yi aikin tela, tun daga kan koyon sana’ar har zuwa }warewar da na samu.
Amma asalin dalilin da ya sa na yi wannan wa}ar shi ne, a watan Ramadan na shekarar 1423 bayan hijira na yi ]inkin da ya wahalar da ni }warai.
Kusan kwana arba’in na yi ina kwana a shago in ka ha]a da ‘yan kwanakin da ke kafin azumin da kuma kwanakin bikin Salla don dukansu na yi su ne a shagon.
To da na auna sai na fuskanci ba wata riba ga irin wannan aiki na kwana ]inki. Duk da yake na sami ku]i sosai amma na rasa inda suka shiga, don ko ]inkin Sallah na al’ada ban yi ba, ma’ana ban sami halin ]inka yadin da na saya don kai na ba. Sannan ba wata ibadar kirki; Ba karatun {ur’ani, ba Tahajjud, ba zuwa wuraren Tafsiri! Wuni kawai nake ina kwana ]inki.
Ga mutane wa]anda ba su sami ]inkunansu ba suna ta ganin ba}ina. Da dai sauran matsaloli, wa]anda na ambaci mafi yawansu a wa}ar.
Wa]annan dalilan su suka sa na yi wannan wa}ar saboda takaici da ya addabe ni.
Wa}ar layi ]ai-]ai ce. Karinta na wata wa}ar fim ]in Hausa ne wadda Misbahu Ahmad yayi, ya na mata amshi da cewa
Iyye iye duniya labari
Ni ko sai na ce
Iyye iye tela sarkin aiki
Ga wa}ar:
1. Allah ni nake yabo ban fasawa
2. Gun manzo nake salati da yabawa
3. Alaye, abokanai ban warewa
4. Har matanshi Sayyadi na sanyawa
5. Aikin tela yau na ke son wa}ewa
6. Don na yi shi shekaru ban mantawa
7. Na san duk lago da wayau da iyawa
8. Gun koyon shi na iya har sabawa
9. Bayan na iya na zam ban hutawa
10. Aikin tela babu damar holewa
11. Wahala ce kawai ciki ba }arewa
12. Kullum ]inke-]inke ko ko farkewa
13. Ko kuma yanka yaduka ko gogewa
14. Ko facin da dole sai an toshe wa
15. Wani tsoho ya takura bai }yalewa
16. Al}awarinmu ba mu tsoron karyawa
17. Costumer ido yake zazzarewa
18. Ha}uri sai mu ce ya yi ko }yalewa
19. Sai uzuri muke fa]a ko bayarwa
20. Keken babu mai tana gun gyarawa
21. Ai mutuwa akai, buki bai }arewa
22. NEPA ba wuta zare na tsinkewa
23. In azumi ya zo wuya aka ninkawa
24. Kwana yanka riguna ko ]inkawa
25. Yin rambul ga wanduna har hantsewa
26. Aljihunmu bai cika bai batsewa
27. Kai wata rana ban da asi na kashewa
28. Ga basir yana shiga bai fasawa
29. Ba ma yin tahajjudi don ta~ewa
30. Sai neman ku]in da ma tarawa
31. Ga }arya wajenmu ba ma jurewa
32. Idi ban da mu ake lissafawa
33. [inki bai barin mu domin holewa
34. Kowa ya yi ]an wuya don ramewa
35. Ga barci idonmu ya kusa cinyewa
36. Ba ma yin shi ba mu samin hutawa
37. Jam’i ban da tela komai dagewa
38. Kifi ne a rijiya bai motsawa
39. Bai jure wa zolaya bai daurewa
40. Yadin ‘yan uwa ya zam zai cinyewa
41. Ko ya sayar, ku]in ga banza ya kashewa
42. Matsalolinmu ‘yan uwa ba }arewa
43. Na bar tela ba ni fatan komawa
44. Wannan ja’iba da]ai ban jurewa
45. Laifin ya wuce batun iya yafewa
46. Don jama’a suna yawan tsittsinewa
47. Mu fatanmu Rabbana zai yafewa
48. Dangi sai ku ba da }aimin dagewa
49. Ko za}in aya ku san za ku yabawa
50. Allah sa batun ku zam kun ganewa
51. Nan zan dakata batu zai }arewa
52. Sai wata rana Allah sa zamu gamewa
53. Don wai kar ku zam da ni kun mancewa
54. Dangi kun sani fa ai ba canzawa
55. Nai salama ku tabbata kun amsawa
56. Sunana Kabiru ko za ku ri}ewa
57. Ya Allah ya ba mu mu duka dacewa
25 ga watan Yuli, 2002
Zariya.