Thursday, January 20, 2011

GAISUWA GA ALBANIY

GAISUWA GA ALBANI

Malam Muhammad Auwal Adam Albani na Zariya sanannen mutum ne da ya shahara a harkar karantar da Sunna da a}idar salafiyya.

Tun wajejen 1997 nake koyon karatuka da dama a wajen shi, musamman a fannonin Hadisi, A}ida, Usul, da sauran fannoni na addinin musulunci.

Na da]e ina tunanin in yi mishi wa}a, amma hakan bai samu cikin gaugawa ba. Sai a shekarar 2005, sa’adda na sami damar yi masa wannan wa}a.

Karin wa}ar na same shi ne a wajen wani mawa}i da ya yi wa {ur’ani wa}a a gidan rediyon Nagarta. Shi cewa yake yi a amshinsa

Mu kama karatu
Mui ta riko da zancen Allah
Kur’ani



Ni kuwa sai na ce:

A gai da min kai
Babban malamin salafiyya
Albani

Ga wa}ar:

1.    Da sunan Allah Sarki ni nake farawa
       Ina ro}on Allah Sarki ya karan baiwa
       Cikin wa}en da a yau zan yi wa ]a mai baiwa
       Muh’d Auwal Adamu wanda shi aka ce wa
       Albani

2.    Ina ta salati gun Manzo uba gun Fati
       Sa’annan na sanyo a ciki da Alul-baiti
       Da su da sahabbai manya ne da sun yi wafati
       Akan bin sunnar Manzona da tsantsar aikin
       Imani
  
3.    Masoya Sunna yau ku tsaya ku ]an saurara
       Ku karka]e kunne zan wa}a ga masu basira
       Uban AbdulBarri gwarzon da ya wuce tsara
       Ba}iyyatu ahlil-khairi wajen hadisi da sanin
       Kur’ani

4.    Idan fa ana dara dole uwa akan fid da ta
       Wajen ilimi Malam Auwal yana da bajinta
       Yana da fasaha sannan ba ya son mai wauta  
       Ina gai da ka ina ta yaba wa wannan gwarzon
       [anmasani

5.     A fannin ilimin {ur’ani ha]a da Hadisi
        {wararre ne shi bai saba wa khairin-nasi
        Wurin fatawa in dai har ya tarar da hadisi
        Ba zai mai tawili ba a gai da kai ya Malam
        Albani

Ina gai da ka
Allah ya tsare ka
Ya kare nufinka
Ya ]aukaka harka
Ba shakka
Kana da nufin kashe sa~ani

6.     Sa’annan ya san fannoni na duk tarihi
        Da fannonin Larabci duk yanai masu sharhi
        Wajen kafa hujja bai hada munkari da sahihi
        Wajen fikihu ma ya yi fice da gaske nake ba
        Tsammani

7.    Ku gai da min Malam masani akan komfuta
       Yana kera ta idan ta baci zai gyarata
       Yana da sani kan duk ilimin da yas shafe ta
        Ku bar mamaki don nace da ku ya san kowane
        Fanni 

8.     Mutum ne mai baiwa da take da ban mamaki
        Masoya Allah sun san ba guluwwi a ciki
        Idan nac ce Albani za ya cinye maki
        Idan da za ai mai exam wajen maki kuma ai
        Tsanani

9.     Ba zan ~oye ba Albani yana burge ni
        Saboda biyar sunnar Manzonmu dan Adnani
        A kanta Muhammadu ke wa’azi yana ta bayani  
        Yana cewa dangi sunna mu bi ta mu bar yin
        Sa~ani


10.   Yana ta kiran dangi don ]ai su bi magabata
        Su daina biyewa jahilci da aikin wauta
        Su gyara a}ida kan Sunna su inganta ta
        Ya ce wannan hanya ita ce ka]ai a ciki ba
        Ru]ani

Ina gai da ka
Allah ya tsare ka
Ya kare nufinka
Ya ]aukaka harka
Ba shakka
Kana da da nufin kashe sa~ani

11.    {wararren malam ya yafe wa mai zaginsa
         Ya ce ba komai don Allah yake aikinsa
         Ya ce da masoya su da wa]nda ke }yamarsa
         Dukansu guda ne don yace dukanku Musulmi
         Ikhwani

12.    A gaida min kai, kai mana maganin‘yan shi’a
         Da su da iyayensu manya dake masha’a
         Gaba ]aya su da wa]anda suke ta aikin bidi’a
         Ka tona asirin tsarinsu da ~arnarsu kai ta
         Bayani

13.    Wa]anda suke zagin sunna ko ka bi ta kansu
         Wajen yin raddi ba ka yin ragi a garesu
         Kana kyararsu da tsabagen ba}in aikinsu
         Nufinka ya zam tsantsar sunna ta danne aiki
         Mai muni

14.    Muhammadu Auwal malam ne da bai da mugunta
         Wajen koyar da karatu ba ya yi ma }eta
         Yana yin dalla-dalla mas’ala ya baje ta
         Wajen reference zai baka tuli ka je ka ji }ari
         Na bayani

15.    A halayenshi Muhammadu babu yanke zumunta
         Da]ai ba ya zagi, }arya ko bai }aunar ta
         Ka bar shi wurin tallan sunna da kuranta ta
         Da bayyana ha}}un ko da ‘yan ]ari}a za sui
         Gurnani

            Ina gai da ka
Allah ya tsare ka
Ya kare nufinka
Ya ]aukaka harka
Ba shakka
Kana da da nufin kashe sa~ani

16.    Ina kake malam wanda ku]i baza su saye ba
         Ku daina tayawa don ni na sani ba riba
         Ba zai canza ba don ‘yan kyautukanku na zamba
    A don haka ne ma bai kar~a, bare wa’azi nai
    Yai rauni

17.    Ina kake malam ]an baiwa da babu irinka
         Wajen iliminka da tsarin rayuwar da ka ]auka
         Da gogewa kan harkar rayuwa da nufinka
         Na alheri, kullum sunna ta }ara gaba kowane
         {arni

18.    Ina ro}on Allah Sarki ya }ara haza}a
         Da ]umbin ilmi, don da’awa ta zam ta mi}a
         Ku zo ku bi sunna ‘yan bidi’a ku daina zala}a
         Idan kun bi ta, kun dace da tsarin Allah
         Kur’ani

19.    Ka je maktab ]in malam don ka sha mamaki
         Ka bai wa idonka abinci ya kalli kayan aiki
         A nan ne za ka ga littaffi ka bu]e baki
         Muhammadu Auwal ya tara su ya tsara fanni-
         Fanni


20.    Yabon da nake wa malam ni a nan zan huta
         Idan an kwana biyu wata}il na ]an maimaita
         Ya Rabbi ka kare min malam ka }ara fahimta
         Ka sa mu ci amfanin ilmin Muhammadu Auwal
         Albani

Ina gai da ka
Allah ya tsare ka
Ya kare nufinka
Ya ]aukaka harka
Ba shakka
Kana da da nufin kashe sa~ani

21.    Inai muku bankwana danginmu sai wata rana
         Idan kuka tad da Muhammadu sai ku mi}a yabo na
         Ku ce masa Asgar ya gaishe shi, nai masa murna
         A kan kyan aikin da yake ya]a sunnar Manzo
Adnani

22.    Ku ce masa Allah na ro}a ina }arawa
         Ya ba shi sawaba har ranar shigar shi kushewa
         Ya sa Manzona zai cece shi ranar tsaiwa
         Ya zarce Aljanna, Allah ka kare min Sheik
         Albani

23.    A wannan baitin zana rufe ku ]an ban uzuri
         Ina da larura zan tare ya-nawa da sauri
         Ku mun ha}uri don wa}ar tawa ba ta da tsari
         Saboda }arancin baiwata da tsantsar fikira
         Mai rauni

Ina gai da ka
Allah ya tsare ka
Ya kare nufinka
Ya ]aukaka harka
         Ba shakka
Kana da da nufin kashe sa~ani

23 ga watan Agusta, 2005

Zariya.


4 comments:

  1. M.Allah ya saka da alkhairi,shikuma da Allah ya dauki kwanansa Allah ya yasa mutuwan shahadah yayi ya kuma albarkaci iyalansa da ya bari da kuma dalibansa

    ReplyDelete
  2. Allah ya jikan malam da rahma
    Allah ya karbi shahadar shi
    Allah ya haskaka qabarinsa
    Allah ya kyautata tamu bayan tashi

    ReplyDelete
  3. Allah SWT ya Saka da alkhairi , ya Kai haske qabarin Malam.

    ReplyDelete