DARUL HADITH
Na yi hidimar }asa wayo a shekarar 2005 a garin Abeokuta , babban birnin jihar Ogun. A lokacin da na zo tafiya sansanin matasa masu yi wa }asa hidima a Shagamu, sai na ga dacewar na yi wa wasu ]alibaina na makarantar Darul Hadith bankwana na musamman a wa}e. Don haka ‘yan kwanaki kafin na bar Zariya zuwa Shagamu sai nu rubuta wannan wa}ar.
Wa}a ce mai kwar hudu. Karinta ina tsammanin asalin shi na wa}ar ga]a ne. Amma ni dai na ]auko shi ne daga wakar ]an uwa Malam Adam Abul-Abbas wadda ya yi mai suna Hijabi.
Ga wa}ar:
1. Darul Hadisi ina son ki
Da ke da duk ma’abotanki
Ina nufin ]alibbbanki
Gare su nai shaidar kirki
2. Darul Hadisi gidan Sunna
Ajin da ya zarce ko ina
Ga ]alibai marasa sakana
Wa]anda raina ke }auna
3. Mun yi karatoci da yawa
Littattafai har saukewa
Duk Juma’a ba fasawa
Karatuka muka bayarwa
4. A da mu kan yi da an sauko
A juma’r kowane mako
A yanzu ko loton farko
Na safiyar Juma’ar mako
5. Mun ka karanta [ahawiyya
Wurin a}idar salafiyya
Mun sauke Allah ya biya
Ya ba mu iko na biyayya
6. Da Tabsira mun sauke ta
Ka sanya Umda bayanta
Sanya Adab sai ka dakata
Akwai ragowa zan furta
7. Ina nufin Talkhisin nan
Na Siffantun malam din nan
Albani ta hadisan nan
Da ma Janaza kuma san nan
8. Mun ka yi littafin Nahawu
Da Sarfu kui ta biyar sawu
Na baitukan in nai sahawu
Ku ]an tuna mani kui afwu
9. Da Musdalah mun koye shi
Shi da Usul don mun yi shi
Dukan su komai da ka ji shi
Dalla-dalla ba }unshi
10. Ya ]alibai gani gareku
Ina yabawa dukaninku
Don kuwa in dai da ba ku
To ai ba makarantarku
11. Kuna ta jure zuwa darasi
Ko da ba ku da ko sisi
Allah ya sa ranar ba’asi
Mu garzaya duka Firdausi
12. Ai dole na jinjina ma wasu
Wa]anda ke cika aikinsu
Wa]anda ba sa latti da su
Nake batu, ku kun san su
13. Da masu latti da ‘yan fashi
Da ni da su sam ba bashi
Babu yabo izuwa sashi
Na masu ]an banzan fashi
14. Masu fahimtar darusana
Allah ya sa ku a Aljanna
Duk wacce ko ta zamo sauna
To walla ni babu ruwana
15. Na so a ce na kira suna
One-by-one na mutane na
Amma yawan ku shi ya hana
Don kar a zo a ji haushina
16. Don ko hala in mance wata
Ko ko a ce na zage ta
Amma ha}i}a ba mafita
Don wasu kam sai na furta
17. Irinsu A’isha mai naci
Na tambaya ba ta sakaci
Cikin aji ba ta barci
Tana kiyaye da lokaci
18. A’isha da ke da Firdausi
Ai tuni nai muku lasisi
Yaran da in dai ga nassi
Ba sa sa~a wa hadisi
19. Allahu Rabbi ya biya ku
Ya sa ku aure tamkar ku
Sannan ya }ara fahimtarku
Ya yau}a}a muku }arshenku
20. Kada ki ce na manta ki
Asma’u yarinyar kirki
Dukan ajin nan }annenki
Don kin riga su a gaishe ki
21. Dake da duk ‘yan }annenki
Walla kuna nunan kirki
Amma na kan sha mamaki
Yadda kike fashin aiki
22. Khadijah ke ba kya wasa
Irinki yaya ga Nafisa
Wacce a yanzun tai nisa
Wacce a ke ce wa Hafsa
23. Kada ki manta burinki
[anki ya zam yaron kirki
Ya zarce Ibnu Hajar, sonki
Yai ta wa sunna jan aiki
24. Ya karya wannan }alubale
Da tuntuni aka daddale
Allah ka sa yaron ya }ale
Kar burin ya bi kwale-kwale
25. ‘Yar Bilkisu da Jamila
Har ma na sanya da ‘yar Sala
Na kan tuno ku da madalla
Ban so ai maku bulala
26. Ku daina latti da ke Murja
[iyar da ba ta da ja-in-ja
Da Aisha sai kin canja
Tsawon hijabi }asa ya ja
27. Dole na sanyo Aishatu
Da Rabi har da Suwaibatu
Ko da a yanzun sun ‘yantu
Sun sauke ba su karatu
28. Ina kiran ku da alheri
Allah ya kare dukan sharri
Ya sa ku auri maza na gari
Wa]anda basa yin mari
29. Ina kike Auntie Sadiya
Ya wacce ba ta jayayya
Ina tuna ki a zuciya
Allah yai maki sakayya
30. In na tuno Auntie Sadiya
Na kan ji }unci a zuciya
Allah kai mata sakayya
Ka ba ta lada na biyayya
31. Kai mana canjin alheri
A madadin wanga ha]]ari
Allah ka }ara mana jari
Na dangana bisa mu}addari
32. Rashida yarinyar kirki
A gai da ke har Antinki
Ga shawara ta a gare ki
Ki }ara }wazo gun aiki
33. Kun ga cikin lissafina
Dole na sanya da Hassana
Sannan Nafisa Hasan na tuna
Mata ga Garba na jinjina
34. Halima T. Shehu na Kano
Safiyya ma kan ki zan kwano
Ke da Faridatu na gano
Cewa kuna fa da alfano
35. Fatima matar malam ce
Bintoto mai son darasi ce
Ki dinga rokon Rabbi ki ce
Allahu ya sanya ki yi fice
36. Na kusa in manta da Sa’a
Da ke da Safiyya mai sa’a
‘Yar Asama kin buga sa’a
Tun da kina }in masha’a
37. Dije Lawal }anwata ce
Da Rabi sun }ulla }awance
Allah ka sanya kin dace
Aurenki da hankali kwance
38. Ke Abu }anwa gun Dije
Tsaya in ]an yi maki jaje
Don kan fashi kin cije
Da ke da Dijale kun saje
39. Harira na can ]akinta
Tana biyayya ga mijinta
Ya Rabbi biya bukatunta
Ka ninka lada a gareta
40. Maryamu yaya ga Sakina
A gai da babbar Antina
Kanwarki ni ta shiga raina
Ina ta nuna mata }auna
41. Ke ko Sakina ki saurara
Gare ki zan ]an yi ishara
In dai har ni kika aura
Wallahi kin tsere asara!
42. Ya Rabbana na ro}e Ka
Ka taimaka ma bayinKa
Wa]anda ke bin manzonKa
Wanda ya kawo sa}onKa
43. Ya ‘yan uwana kui hakuri
Wa]anda ba su cikin tsari
Wa]anda nam manta, buri
Na wa}e Daru bila fahari
44. Ya ]alibaina ku ]an tsaya
Ga hanzarina guda ]aya
Don ko karatu za ya tsaya
Ba na son mu yi jayayya
45. Ni za na je NYSC
Don haka dole mu bar darasi
Kui hakuri kar kui kwafsi
Duk farko sai yai akasi
46. Allahu ]alibbai ga su
Rabbi ka biya bukatunsu
Ka yafe dukkan laifinsu
Ka shirya dukkan zuriyarsu
47. Ka sa su more wa ilimi
Su dinga aiki da ilimi
Don ya kasance ko lazimi
Na zana wanga da al}alami
48. Ina wa dangi ban kwana
Ku yafe dukkan laifina
Mu ro}i Allah duk ya mana
Sakamakonmu da Aljanna
49. Ai rabuwa ba ta da da]i
Bayan sabo da nisha]i
Mui hakuri har zuwa ba]i
Mu jure dukkanin ra]a]i
50. Allah na ke ro}o ya mana
Falalar gamuwar mu da juna
Ya sa mu jure da amana
Da girmamawa gun juna
51. Ma’assalam ni naka cewa
Don lokaci na ta }urewa
Zan ha]a duk nawa-ya-nawa
In tafi neman dacewa
52. Shi kenan sai na dawo
Har tsaraba zan ]an kawo
Ai baitukan sun ]an yi tsawo
Amma a nan zan sa tsawo
53. Nai adu’a a wajen Allah
Tare da mammatse }walla
Na ce ya }ara min falala
Da gafara da yawan sallah
27 ga watan Yuli, 2004
Zariya.
No comments:
Post a Comment