WA{EN A{IDAR [AHAWIY
Littafin “Al-Akidatud Dahawiyyah” sananne ne a wajen malamai da ]alibai mabiya Sunnar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Na koyi karatun litttafin a wajen babban malaminmu Muhammad Auwal Adam wanda aka fi sani da Albani tun wajejen shekarar 1996.
A shimfi]ar karatun malam ya yi bayanai masu jan hankali game da muhimmancin littafin musamman akan a}idar magabata, ya kuma kawo zantukan malamai wa]anda suka yabi littafin ko suka yi wa ]alibansu wasiyya da cewa su kula da littafin.
Wannan ya sa mini }auna ta musamman ga littafin, abin da ya ja na yi tunanin ya kamata in fassara shi da Hausa. Daga baya kuma na tu}e a kan tunanin cewa ba fassara shi ka]ai zan yi ba, a’a wa}e ya kamata in mai da shi cikin Hausa.
Na yi amfani da karin wa}ar ha]in kan Afirka ta Malam Abubakar Ladan Zariya. Wadda tun ina ]an yaro nake matu}ar sonta.
Malam Abubakar Ladan yana yawan maimaita wani amshi a wa}ar yana cewa:
Allah ya Allah ya Allah
Hada kan mu Afirka mu so juna
To ni kuma sai na kan ce duk bayan gunduwa goma:
Allah ya Rabbi abin bauta
Kai [ai na ri}a ban shirka ba
Wa}ar tana da layi hur-hudu ne.
Ga ta kamar haka:
1. Allah Sarki ya mai iko
Ya Rahman Rabbi ka ban iko
Allah na kiraya tun farko
Ba na ro}on wani ba shi ba
2. Sarki Mahalicci mai kowa
Ma’abocin girma da uluwwa
Shi ]ai ya kamata a bauta wa
Sam bai dace ai shirka ba
3. Allah yi salati da aminci
Ga Muhammadu manzon adalci
Haka alaye masu karamci
Da sahabbai ni ban ware ba
4. Wa}ar ga a yau zan rera ta
Don in bi a}ida na fa]e ta
Ta [ahawiy yau zan wa}e ta
Kuma ba larabci zan yi ba
5. Ro}ona gun Allah Sarki
Ya yi min baiwar ban mamaki
Na biya ta a gane ai aiki
Da a}ida ba yin shirka ba
6. Dangi ba na son ja-in-ja
Kun san fa a}ida ce daraja
In ka ri}e wannan ba danja
In ba ta ba za ka ji da]i ba
7. Na za~i [ahawiyya ne ni
Don na ga tana da mu}ami ni
Wata ran malam ya hore ni
Bai bar ni na kauce hanya ba
8. Ya ce “La yastagni anha
[alibu ha}}in” summa alahha
Har ‘yan yara koda a raha
A biya masu sam bai ware ba
9. Shi ne naka so na bi doronta
Na biya ta da Hausa na wa}eta
Don yara su haddace manufarta
Har manya ma ban tsame ba
10. Baban Jafar mutumin Misra
Ya yi karatu sannan da kira
Izuwa hanyar manzon tsira
Masani ne ba ko na wasa ba
11. Suka mai sharri suka bata shi
Suka ce wai ]an shi’a ne shi
Don ]ai ya ce a bi manzon shi
Sai yad dage bai zauna ba
12. Ya rubuta a}ida kuma yac ce
Wannan shi ne ni na }udurce
Maganar da suke duka }arya ce
In ba ta cikin littafin ba
13. Ita wagga a}ida ta dace
Don ko ta zam salafiyya ce
Shi wanga batu an tantance
Ba zance ne na ]arika ba
14. Ashabu Rasuli da ogansu
Duka kan ta su kai addininsu
Shafi’i, Malik, da na bayansu
Annu’umanu bai kauce ba
15. Baban Yusuf haka Shaibani
Su ma fa a kan ta su kai ta gini
Limamin Sunna Shaibani
[an Hambali ~ai taba shirka ba
16. Ahlus Sunna sun ha]u kan ta
Sun koyar sun yi ta sharhinta
Yanzun ku tsaya zan wa}e ta
Ba yadda ka san ta da yare ba
17. Tauhidin da muke cewa mu
Muka }ulla hakan a cikin ranmu
Cewa Allah Mahaliccinmu
{waya daya ne rak ba wai ne ba
18. Shi bai da abokin tarayya
Ba mai iya jan Shi da jayayya
Mun tabbata wanga batu hayya
Ka bi tauhidi ba shirka ba
19. Sarki Allah babu kamar Shi
Ba wani Allah in bayan Shi
Kowa kake ba ka buwayar Shi
Bai farko kuma bai }arshe ba
20. Ba Ya }arewa har abada
Jujjujayawa sai Ya yarda
Allah Rayayye ne tun da
Ba Ya mutuwa bai barci ba
21. Sam ba a iya a tunano Shi
Koko ka iya ka fahimce Shi
Don ba Ya kama da halittunshi
Shi yay yi halittu ba wai ba
22. Kuma bai da bukata a wajen su
Allah shi [ai Ya azurta su
Ba Ya wahala gun ci da su
Mai rai Ya kashe bai tsoro ba
23. Haka zai tashe su dukanninsu
Bai jin wahala bisa tashin su
Tun da ma can kafin yin su
Haka Rabbi ya ke bai canza ba
24. Su ]in nan ba }ari ne ba
A cikin mulkinSa da izza ba
Da dukan siffofi bai kau ba
Haka nan kuma ba zai canza ba
25. Ba sai da ya }era halittu ba
Ya zamo Mahalicci ba haka ba
Haka ba sai sanda ya tsara ba
Ya kasance Bariy ba wai ba
26. Shi Rabbun ne a wajen kowa
Don shi ya halicci dukan kowa
Allah Shi ne ke rayawa
Ba sai da ya }era halittu ba
27. Ikonsa yana bisa kan kowa
Haka gun Shi bu}atar ]an kowa
Shi bai da bu}ata gun kowa
Sauki komai yake gun Rabba
28. Huwa Rabbi Sami’un wa Basirun
Haka Allah laisa ka hu shai’un
Khalakal Khal}a summa sama’un
Ba su ~uya ga Allah Sarki ba.
29. A}dar duka shi yas sanya su
Haka yats tsaro ajalolinsu
Ya san aikin da suke yi su
Tun loton bai yi halittu ba
30. Ya umurce su su yi ]a’ar Shi
Haka nan ya hane su su sa~e Shi
{udurar Allah da mashi’ar Shi
Bawa ba zai kuwa haura ba
31. {udurarshi abar zartarwa ce
Bayinsa gaba daya ni na ce
Bisa damar Rabbi abar zarce
Suka juyawa ba su haura ba
32. Ma sha’a lahun wannan kana
In ya }i ko to ai ba kana
Haka Rabbi yake Mahaliccina
Bai ta~a rauni gun iko ba
33. Shiryarwa da ~atarwa sai shi
Falala ga ]ayan adalcin shi
Ya tsare Yai ma jarabawarshi
Allah sam bai zalunci ba
34. Bayi duka kai-kawowarsu
Bisa adalcin Mahaliccinsu
Ko ko falalar wanda ya yi su
Ba sa wuce wanga mataki ba
35. Shi bai da sa’a kuma ba tsara
Ba mai hana aikin da ya tsara
Ko ture hukuncin da ya tsara
Yi masa gyara bai taso ba
36. Ba mai rinjaye a gare Shi
Duka wannan mu mun ka fa]e shi
Mun tabbata wanga da aikenShi
Ba za mu sake mu yi }arya ba
37. Manzonmu Muhammadu bawan Shi
Mun tabbata Shi yaz za~e shi
Ya ri}e shi abin yarda gun Shi
Bayan shi ba zai wani aike ba
38. Jagora ne gun manzanni
Shi ne yak kawo {ur’ani
Ya zamo }arshen ‘yan sa}onni
Khalilin Allah ba wai ba
39. Duk wanda ya zo nan bayan shi
Yac ce Allah ya aiko shi
{arya ce ko wane ne shi
Allah tsine masa ba wai ba
40. Allah ya aiko manzon Sa
Izuwa dukannin bayin Sa
Shiriya yak kawo hasken Sa
Ya haskaka bai bar zulma ba
41. {ur’ani zancen Allah ne
Allah ya saukar wahayi ne
Kar wanda ya ce Makhlu}i ne
Bidi’a sam ba kana ce ba
42. Muminnai sun ce ha}}un ne
Sun tabbata zancen Allah ne
Ba ya kama da batu na mutane
Hakanan yake sam ba tababa
43. Duk wanda ya ce zancen wani ne
Wannan tabbas ya zam arne
Sai ya ci wuta sai ya }one
Matu}ar bai tuba da sauri ba
44. Allah ya ce “uslihi sa}ar”
Duk wanda ya ce “}auli na bashar”
Daga nan muka sam tabbar amsar
Ba zance ne na halittu ba
45. Kafirci ne a sifanta shi
{ur’ani da batun bayin Shi
Ka kula da batun nan da ka ji shi
Kauce masa ba tsira ce ba
46. Wannan zai sa ka yi tsantaini
Ka wuce arna masu bayani
Na za}ewa har ya zamo fanni
Allah da halittu ba ]aya ba
47. Mun yarda akan ‘yan Aljanna
Su za su ga Allah har sui murna
Hakanan {ur’ani yan nuna
Amma bai ce ga yanayi ba
48. Ba ma wuce gona da iri mu
Ba ma cewa da tunaninmu
Mun sallama imanin kanmu
Ba mu kutsa ko tababa ba
49. Wannan ita ce fa a}idarmu
Tafsirin ba ra’ayoyinmu
Ingantattun nassoshinmu
Ba mu yarda da bin son zuci ba
50. Ba wanda ya tsira a addini
Sai wanda ya bar biye }aulani
Ya bi Manzon nan mai {ur’ani
Ga batun Allah bai ja mai ba
51. Shubuha ya buge ta ya ]au haske
{ur’ani kuma yab bi da gaske
Haka sunnoni duka ban da sake
Ba tare da bin sambatu ba
52. Musulunci sam bai daidaita
Sai taslimi ya }asaita
Istislami sai ka furta
Ba neman kaiwa matu}a ba
53. In ko ka za}e kan ilminka
Ga abin da haramun ne kanka
Wannan shi ne zai cuce ka
Ba zai kuma kai ka ga tsira ba
54. Wannan bisa shirka zai kai ka
Ya hana ka fahimtar dininka
Ya raba ka da ]an imaninka
Tauhidin ba zai saura ba
55. Sai dai ka zamo a cikin rikici
Ka fa]i ka tashi munafurci
Ba imani ba kafirci
Kuma kai ba ka ce }arya ne ba
56. Kai ba ka ce wannan daidai ba
Ba ka tabbata }aryar zance ba
Ka sa shakka ba ka huta ba
Kai ba tsantsar mai saiti ba
57. Sai waswasi ka zamo ~aidu
Ba ka a ruwa kai ba ka tudu
Susa ba ta yiwuwa da gudu
Ka yi marmaza kai saurin tuba
58. Duk wanda ya }aryata manzona
Cewa in an shiga Aljanna
Za a ga Allah har ai murna
Ba zai amfana da wannan ba
59. Ko wanda ya murgu]e nassoshi
Yai tawili ya bi son ranshi
Ya guje wa tafarkin manzonshi
Wannan shi ma ba zai sha ba
60. Addinin Allah musulunci
Tawili ko wani ~atanci
Ba su da }ima sai adalci
Sai mi}a wuya ba rikici ba
61. Mai kore sifofin Rabbani
Wannan ya }aryata {ur’ani
Hakanan wanda ya ba shi kamanni
Wannan aiki bai dace ba
62. Siffofin Allah kyawawa
Sam ba su kama da sifar bawa
Sun sha bambam da na ]an kowa
Wannan haka ne ba tababa
63. Ya daukaka Allah Mahalicci
Daga duk wani bawa mabu}aci
Sarki Allah bai zalunci
Ka ri}e wannan ka fa]a a gaba
64. Isra’i mun ce ha}}un ne
Haka ma Mi’iraji tabbas ne
Baitul Ma}adis daga nan shi ne
Yaj je sama ba }arya ce ba
65. Da jikin shi ya je ba barci ba
Ba kuma ruhi ban da jiki ba
Manzonmu ba zai fa]i }arya ba
Bai na}}asa sa}on Allah ba
66. Allah ya ]aukaka manzona
Sallah yab bai wa masoyina
Allahs sa shi zai ceto na
In tsira na zam ban ta~e ba
67. Mun yarda da tafkin da ya ba shi
Don yas shayar da mutanenshi
Babu }ishirwa bayan shan shi
Kuma ]an bidi’a ba zai sha ba
68. Kofin sha ba zai yi ka]an ba
Wawa gun sha ba ta taso ba
Girmanshi ba za ya misilto ba
Sauran zancen sai an duba
69. Ceton shi da zai ai tabbas ne
Shi ne zai ceci mutane
Wannan zance ne fa sananne
Tun ba a wajen malammai ba
70. Allah ya ]au al}awarin Sa
Cewa su za sui bautar Sa
Ba za su yi sa~on Allah ba
71. A’araf aya saba’in da biyu
Bayan ta ]ari kuma in ya yiwu
Ka bi sharhi ban da halin gayu
Kar kai jayayyar ‘yan taba
72. Adadin ‘yan Aljanna dukansu
Da wa]anda wuta ce }arshensu
Allah tuni ya lissafa su
Ba za ya rage ko }ari ba
73. Af’alul Khal}i dukanninsu
Da sanin Sa suke yin aikin su
Aikin da suke Shi yay yi su
Ba su da Allah in ba shi ba
74. Da hukuncin Shi yaw ware su
‘Yan aljanna Ya hukunta su
Haka ‘yan wuta ma Yaw ware su
Allah kuma bai zalunci ba
75. Asalin }adara wani sirri ne
Allah Sarki mai baiwa ne
Shi ]ai ya sani don gaibi ne
Ba mai }adara in ba shi ba
76. Da Mala’ikku, Annabbawa
Ba wanda yake iya ganewa
Kuma ba kyau neman kutsawa
Ba imani ne wannan ba
77. [ugyani ne da ranshin kunya
Ka kiyaye kar ka bi ‘yan baya
Bar waswasi bar zar~a~a~iya
In ka }i ba za ka falahi ba
78. Allah Sarki ya ]auke shi
Ilimin }adara daga bayin Shi
Kuma ya hana nema na sanin shi
Bai yarda a nemi sani nai ba
79. La yus’alu amma yaf’alu
Ayar Allah ce tanzilu
Haka nan taz zo bisa tartilu
Ba zance ne na mutane ba
80. Duk wanda ya ja da hukuncinSa
Ya }aryata ayar RabbinSa
Ya kafirce daga dininsa
Arne ne ba ko musulmi ba
81. Jimlolin nan da na shisshiryo
Zance ne sam ba wani ~oyo
Bawa mabu}aci ]an goyo
Ba zai tsira bila wannan ba
82. Bayin Allah da waliyyanSa
Haka nan ulama’u mutanen sa
Ita sun ka ri}e gun bautar sa
Ba su }aryata Manzon Allah ba
83. Nan sun ka tsaya ba su gota ba
Haddin da a kai ba su keta ba
Gona da iri ba su zarce ba
Bautar Allah ba su daina ba
84. Ilmi ka san fa gida biyu ne
Na ]ayan su akwai shi sananne ne
Shi kau na biyun ~oyayye ne
Allah bai ba bayi shi ba
85. Imani ba shi da inganci
Sai an sa ilmin adalci
An bar kutse bisa jahilci
Ba ra’ayin }artin banza ba
86. Lauhun da {alam mun imani
Dukkan }adara an yi bayani
A rubuce ciki mun imani
Allah ya }adarta ba wai ba
87. In da bayi za sui gayya
Don canza abin da ya shisshirya
{ari da ragi ko jayayya
Wallahi ba za su iya mai ba
88. Jaffal }alamu ka ji batuna
Ma akh]a‘ani bai samu na
Akasin haka koda ban }auna
Ba zai kauce ga bari na ba
89. Bayi ku sani cewa Allah
Tuni yai tsari shi na jimilla
Bisa kan hikimar tsarin Allah
Ba sa haye tsarin Allah ba
90. Kuma babu ragi haka ba }ari
Ba canji komai }amari
Haka cin gyara bar kurari
Ba za ka iya da Ilahiy ba
91. Ba mai iya }ara halittunSa
Koko ya rage masa bayinSa
Ko da a sama ko nan a }asa
Wannan fa da]ai ba zai yiwu ba
92. Wannan a a}ida asali ne
Ka ri}e shi da kyau ko ka gane
Don ko maganar {ur’ani ne
Ba wai maganar bayi ce ba
93. Ahzab, Fur}an ka karanta su
Farkon Fur}an sai ka gamsu
Aya ta biyu an yi batun su
Harkar }adara ba wasa ba
94. Ahzab kuwa aya ta talatin
Da takwas, ka ri}e wannan baitin
Don na shirya da ba}in Latin
Ba zai yiwu in ja ayar ba
95. Allah tsine wa duk wanda
Yas sa wa Allah andada
Zai ]an]ana ku]a tai tun da
Bai zamto mai tauhidi ba
96. Kutse ba kyau kayin }adara
Duk wanda ya }i zai yi asara
Kunya da tsiya da yawan fatara
Tsira ba zai ta~a samu ba
97. Zai fa]a ru]u, ta~ewa
Sai ta aurai ba sa rabuwa
Zindi}anci zai komawa
Ba zai zama mai tauhidi ba
98. Al-arshi da Kursi tabbas ne
Allah daga su mawadaci ne
Bayin Allah mabu}ata ne
Ba za su wadatu da Allah ba
99. Allah ya kewaye Al-arshi
Ba ma yarda mu sifanta Shi
Mun gasgata manzo bawanShi
Manzon Allah bai }arya ba
100. Ibrahim ka ga Khalilun ne
Allah ya ri}e shi ha}i}a ne
Haka nan Musa ko Kalimun ne
Ba za mu bi ‘yan ta’a]ili ba
101. Mun mi}a wuya mun imani
Mun gasgata ayar {ur’ani
Ba ma bin duk wani shai]ani
Ba za mu biye wa son rai ba
102. Mun yarda da manzannin Allah
Annabbawa bayin Allah
Sun kawo addinin Allah
Ba su tauye sa}on Allah ba
103. Mun shaida cewa aikinsu
Wa’azin tauhidin Rabbinsu
Allah da]a tsira a gare su
Ko da ]aya ni ban ware ba
104. Ahlul-}ibla ko musulmi ne
Matu}ar sun yarda suna a sane
Cewa manzo jagora ne
Ba su canza mai addini ba
105. Ba su }aryata Manzon Allah ba
Ba su wa sunnanrsa jafa’i ba
Ba su }etare haddin sunnar ba
Ba mu kafirtar da musulmai ba
106. Ba ma rigima kan {ur’ani
Ba ma sa~i-zarce da mirani
Ba ma rikici kan addini
Ba ‘yan tawaye ne mu ba
107. {ur’ani zancen Allah ne
Wahayi, Jibirilu amini ne
Ya kawo sa}on mun gane
Ba zance ne na mutane ba
108. Ba ma cewa makhlu}i ne
Maganarmu irin ta sahabbai ne
Bidi’ar jayayya shirme ne
Allah bai yarda da wannan ba
109. Dukkan mai kallon al}ibla
Don yai sa~on Sarki Allah
Komai girman sa~on walla
Ba mu kafirta shi da wannan ba
110. Sai dai in ya yi giringi]ishi
Ya }udurce halas ne sa~on Shi
Wannan ya warware dininshi
Shi kam bai zam fa musulmi ba
111. Imani mu ba ma cewa
Bai inganta ga malaifawa
Fata na gari ga musulmawa
Ba mu wa Allah sa~i-zarce ba
112. Mai kyautata aiki muminni
Fatan mu garai gun Rahamani
Ya yi mai rahama ya haye tsani
Ba mu ce ]an aljanna ne ba
113. Duk wanda ya sa~a wa Rabba
Wannan ko muna yi mai tuba
Istigfari gun ya Rabba
Ba mu yanke }auna kai nai ba
114. Ba wanda mu kan ce ya tsira
Ko ya ta~e ya yi asara
Kowam mutu ba ma karara
Ba mu zartar mai da hukunci ba
115. Yankar }auna da amincewa
Ka guje, don kar sui ma yawa
Tsakiyarsu ka zam daidaitawa
Ba wai ka biye wa guda ]ai ba
116. Ba ma hana bawa imani
Don laifi ko don nu}usani
Sai ya musa tushen imani
Wannann ba zai ta~a tsira ba
117. Imani sai ka furta shi
Can zuci ka ce ha}}un ne shi
Da ga~arka ka aikata aikinshi
Malam bai ambaci wannan ba
118. Dukkan ingantaccen nassi
Manzo ya fa]a yay yi hadisi
Mun yarda da su ba tadlisi
Ba mu mur]e batun manzona ba
119. Bayin Allah ba fifiko
Illa ta}awa da yawan tsaiko
Ba su nace wa son zuci ba
120. Muminnai dukka waliyyai ne
Mafiyinsu yakan ]ara ]a’a ne
A wajen Allah mai baiwa ne
Baiwar Allah ba ta }are ba
121. Mene ne ma’anar imani?
Ka sakankance kan Rahmani
Littaffai nai har Manzanni
Tashin duniya ba gangan ba
122. {adarori sai ka amshe su
Ka yarda Ilahi yay yi su
Alheri, sharri akasin su
Da Mala’ikku ban manta ba
123. Wannan fa batun dukkanin shi
Mun yarda da shi yadda ka ji shi
Addini ba ma keta shi
Ba mu gi~are harkar Allah ba
124. Mun gasgata manzannin Allah
Ba ma raba addinin Allah
Duka sun wa’azi kuma sun sallah
Hanyarsu ba tai bambamci ba
125. Bayi na cikin al’ummarmu
In sun zunubi gun Allahnmu
Wuta za su zuwa, Rabbi tsare mu
Sai dai ba har abada ne ba
126. Matu}ar ba shirka suka yi ba
Ko da ba su bar yin zunubin ba
Amma ba su bar imani ba
Ba su kauce wa musulunci ba
127. Allah ya san ya zai yi da su
Ko yai rahama ko hora su
{ur’ani, Mata; surarsu
Ta nuna hakan ba wai ne ba
128. Aya ta bakwai bayan forty
Haka sha shida bayan mi’ati
Da hadisan baba gun Fati
Ba zance ne mara hujja ba
129. Adalci ne ya azabta su
Rahamarsa ya bar su a cece su
Ya zuba su a aljanna dukansu
Allah bai yarda da ~arna ba
130. Allah na son masu biyar shi
Su ko arna da ka sa~on shi
Da wa]anda suke }in ]a’arshi
Sun ta~e sam ba su dace ba
131. Allah bai son su yana }in su
Don sun musa Allah da ya yi su
Allah ka tsare mu ga aikinsu
Ka kashe mu ba mui ma shirka ba
132. Bayan kowa za mui sallah
In ya mutu za mui mai sallah
Barrun, fajir bayin Allah
Matukar bai bar addini ba
133. Ba ma saka kowa mu a wuta
Haka aljanna, ba ma wauta
Shirka in sai shi yaf furta
Ba mu san sirri na zukata ba
134. Ba mu yarda a ya}i musulmi ba
Komai laifi ko ya fi riba
In ba haddi za ai mai ba
Ba za a zubar da jini nai ba
135. Ba ma wa a’imma tawaye
Ko da sun karkata sun lauye
Za mui musu ]a’a, ko waye
Tsine masu ba daidai ne ba
136. In ba sa~o suka ce ai ba
Nan kam ba za ai ]a’a ba
Ba za mu gaza ga du’a’i ba
[a’arsu ko mu ba mu fasa ba
137. Addininmu shi ne sunna
Mu ne jama’ar Ahlus-Sunna
Ba ma raba kai ba ma kunna
Sababin sa~ani ba wai ba
138. In al’amari ba mu gane ba
Allah a’alam ba mu nace ba
Ba mu ce mu mun san komai ba
139. Shafar huffi addini ne
Halin tafiya da gida ]ai ne
Bambamcin na yawan wa’adi ne
Ba mu }aryata manzon Allah ba
140. Hajji da jihadi daidai ne
Zarcewarsu har abada ne
Jagora ko mai sa~o ne
Ba zai hana aikin Allah ba
141. Marubuta mun yarda akwai su
Gadin aikinmu wazifarsu
Allah ya girmama harkarsu
Ba mu }aryata Allah Sarki ba
142. Malakul-Mauti mun yarda da shi
[aukar rai shi ne aikinshi
Azra’ilu wai sunanshi!
Amma bai tabbata suna ba
143. Kabari da azaba tabbas ne
Munkar da Nakir ma mun gane
Sun zo a cikin nassoshi ne
Ba mu }aryata nassi ko ]ai ba
144. Duk ran da }iyama tat tashi
Kowa sai an gwada kayanshi
Littafi nai ya karanta shi
Ba wanda ba zai je gun nan ba
145. Da sawab da i}ab duk mun yarda
Ardin aiki ma mun yarda
Haka nan da Sira]i mun shaida
Haka Mizani ma ba mu ja ba
146. Mun yarda da cewa Aljanna
Da wuta tuni su duka an gina
Kuma wagga a}ida ta nuna
147. Tun kafin khalkin bashariyya
Allah yai Janna da Hawiyya
Yai masu shigan kowacce ]aya
Allah sam bai ta~a barci ba
148. Su ‘yan wuta yai musu adalci
Akasin haka ko ya yi karamci
Allah ke }addara yin barci
Allah bai mance komai ba
149. Samun dama a wajen bawa
Tare da aikinsa take zowa
Shi taufi}i baya yiwuwa
Samun shi ga bawa ba wai ba
150. Amma samun damar }arfi
Da wadata su duka sun shafi
Kafin aikin, ba ma tsafi
Mu sam ba mu soki hadisi ba
151. Mun ce bawa, har aikinshi
Allah Sarki yak }era shi
Amma bawan yai kasabin shi
Ba mu karkata mu ga za}ewa ba
152. Allah ai yai mana sassauci
Takhlifin Allah ba }unci
Allah ya san mai ha’inci
Ba zai wa Allah wayau ba
153. Don babu dabara gun kowa
Ko wayau ko kuwa dambarwa
Allah shi yay isa kan bawa
Ba zai yi gina daga Allah ba
154. Hila, harka ba ta yiwuwa
Gun ]a’a ko kuwa sa~awa
Sai in Allah ya ba bawa
Dama, ka ji wannan ba wai ba
155. Bawa ba }arfi a gare shi
Sai in Allahu fa ya ba shi
Sannan ne ai zai same shi
Wannan ai ba wata tababa
156. Dukkan harka in ta gudana
Da mashi’ar Rabbi take nuna
Ilminshi da }udrar Rabbina
Da }ada’in Allah ba wai ba
157. Damar Allah ai tai galaba
Kan dukka mashi’a ba wai ba
Haka zartarwar Allah Rabba
Ta haura dabaru ba wai ba
158. Allah shi yaf alu ma sha’a
Kuma ba zalunci a mashi’a
Ya tsarkaka Rabbi ga yin su’a
Shi bai dangantu ga ~arna ba
159. Adu’ar bayin da suke raye
In sun yi ga wanda suke wa maye
Za tai amfani, ko waye
Ba zai iya canza }ada’i ba
160. Adu’ar Allah ke amsawa
Da bu}atu shi ke bayarwa
Shi ke yi wa bawa duka baiwa
Bawa bai mallaki komai ba
161. Kuma bai da wadata daga Allah
Ko da }iftawar bismillah
Duk wanda ya ce shi zai }ulla
Yai ridda ba zai ta~a tsira ba
162. Da gadhab da ridha Allah na yi
Bisa bayinsa kuma in ya yi
Ya sha bambam da na mu bayi
163. A a}idarmu da akwai }auna
Ga sahabban manzo na Madina
Shi ne Ahmad ]a ga Amina
Ba mu ware guda muka wurgar ba
164. Ba ma zamewa gun son su
Haka ba ma kyara ga ]ayan su
Ba ma }aunar mai zagin su
165. Sai dai mu kira su da alheri
{aunarsu akan ta muke fahari
|atanci gun su mu ce sharri
Mai yin shi ba zai yi falahi ba
166. Tabbas }in su ]ugyani ne
Kafirci ne da jafa’i ne
Hakanan mun shaida nifa}i ne
Ba aikin mai tauhidi ba
167. A a}idarmu ga halifanci
Bayan manzo mai annabci
Sai baban A’i ga adalci
Ijma’i ne ba a sa~a ba
168. Daga shi kuma sai baban Hafsa
Sannan Usmanu muna son sa
Da Aliyyu uba ga tagwawensa
Sune khulafa ba mu ware ba
169. A a}idarmu ai mun shaida
Cewa su ]in ga da]a da shida
Aljanna su kai, duk an ba da
Ba wai fa da ka muka shaida ba
170. Sauran yanzun zan }irgo su
[alha da Sa’ad da Sa’idunsu
Da Zubairu, Ubaida amininsu
AbdurRahman ban ware ba
171. Duk wanda ya tsarkake harshensa
Daga zagin matan manzonsa
Ba ya muzanta sahabbansa
Wannan bai zam da nifa}i ba
172. Manyan malumma salafawa
Da na bayansu bisa kyautawa
Ahlul-Asari, kuma ‘yan baiwa
Ba za mu kira su da muni ba
173. Fu}aha’u da su mun sanya su
Mu kullum sai dai mu yabe su
Ba ma ~atanci a gare su
Ba mu yarda da mai yin wannan ba
174. Ba ma cewa mu ga waliyyi
Ya zarce mataki na nabiyyi
Sai ma cewa dai da muke yi
Ba zai kamo wani manzo ba
175. Mun ce ma annabi }waya ]ai
Ya zarce waliyyai baki ]ai
Mun yarda karama gun su da]ai
Ba mu }aryata manzon Allah ba
176. Daga nassoshi ingantattu
Don ba ma aiki da matattu
A riwaya sai ta amintattu
Ba mu yarda da zu}i-ta-malle ba
177. Har yau ka sani a a}idarmu
Tashi na }iyama zai samu
Wannan duka sai ya riske mu
Ba za a yi ba wani bawa ba
178. Da alamomi duk na }iyama
Mun imani ba ma }yama
Rana ma za ta fito yamma
Rannan ai ba sauran tuba
179. Sannan Isa ma zai dawo
Dujal ma zai zo yai yawo
Hakanan Yajuju su cinye tuwo
Duka wannan mu ai ba mu ja ba
180. Amma ba ma gasgata boka
Ko ]an duba na cikin bukka
Ko mai tsafi ba ma shakka
Cewa ba kan sunna suke ba
181. Hakanan mai yin da’awar }arya
Mai sa~awa asalin hanya
Ta Muhammadu ango na Safiyya
Aikin ga da]ai ba daidai ba
182. Sannan fa ha]in kai na Musulmi
Bisa kan sunna kan Islami
Wannan daidai ne ba zulumi
Ba mu yarda da yin sa~ani ba
183. In an yi ko to dole a tace
Kan sunna mu kan mun nace
Ita ce daidai mun tantance
Ba za mu bi zancen }arti ba
184. Addinin Allah ai ]aya ne
Musulunci dole guda ]aya ne
Sama har }asa ko a ina shi ne
Sam ba shi da canji ba wai ba
185. Shi ne addinin manzanni
Mun san haka ne daga {ur’ani
Duk mai son }ari na bayani
Ya wuce gun malam ba ni ba
186. Musulunci ka ga madaidaici
Don babu guluwwi, shashanci
Kuma ba ta}asiri ko baci
Allah bai yarda da amni ba
187. Hakanan da iyasi ma ba shi
Jabari, ta’a]ili ture shi
{adari, tashbihi mai yin shi
Da wuya ka ga bai sha kunya ba
188. Wannan shi ne addininmu
Fili da a ~oye a}idarmu
Kuma mun ce mu babu ruwanmu
Da abin da ka }ara ba mu ba
189. Sarki Allah mun ro}e ka
Ka tsare imanin bayinka
Ka kashe mu akan addininka
Ba wai mu zamo mun ta~e ba
190. Ka raba mu da sharrin Shi’anci
Jahamiyyanci da munafurci
Hakanan Kadariyya ~atanci
A gareka ba za mui shirka ba
191. Da dukan hanyoyi na batattu
Ba sa bin sunna ba su batu
Da suke yi ba kan sunna ba
192. Allah Sarki mai zamani
Ya wanda ya aiko {ur’ani
Shi mun ka bi mu mun imani
Ba za mu biye wa ]agawa ba
193. Na kawo }arshen wa}ena
Allah ka cika mani burina
Lada ya Rabbi ga aikina
Ya zamo ba don riya ni nai ba
194. Duk mai son }ari na bayani
Sharhin Hanafiy zai ji bayani
Hakanan ko da a cikin matani
Ba zai rasa sharhi ]ai-]ai ba
195. Hakanan kuma sharhin Albaniy
Ya yi shi da kyau ya burge ni
Ka biye mishi dan ka haye tsani
Shi jahilci ba riba ba
196. Na }are wa}ar zan tashi
Allah sa ba kwa bi na bashi
Kha]a’in da na yi in kun gan shi
Gyara shi ba zai ban haushi ba
197. Ni ne Asgar nai bankwana
Dangi Allah sa kun amfana
Don wannan shi ne burina
Ba wai wa}e ne tsura ba
198. Na sallami kowa zan tashi
Allah ya gama mu da manzonShi
Mu zamo mun sha daga tafkin shi
Ba wai mu zamo korarru ba
199. Ya Allah Rabbi ka yafe ni
Kha]a’i, sahawin da ya faru da ni
Wa}an nan baiti mi’atani
Ba }wara ]ai ban gota ba
20 ga watan Janairu, 2003
Zariya
No comments:
Post a Comment