BAKANDAMIYAR KULLIYA
Wani lokaci can baya a watan Yuli na shekara ta 2002 ina zaune a gida da yamma, zan iya cewa ina hutawa ne ko kuma ina kokarin murmurewa daga wani zazza~i da bai da]e da saki na ba. Sai na ga dacewar in yi wa malamai abokan aikina a Kwalejin Abukar Gumi wa}a. Na yi haka ne da nufin wa}ar ta zama wani kundi na bayanai da zan iya amfani da shi wajen tuno su ko bada]e ko bajima.
Wa}ar kwar hudu ce, tana da karin Larabci ne da ake ce masa Wafir. Sunanta ko kamar yadda ka karanta a farko “Bakandamiyar Kulliya”
Ga wa}ar:
1. Da sunan Rabbi wa}a za na fara
Ina ro}o gare Shi ya ban basira
Da]an hikima Alimu ka bani lura
In tsara yabon da zan yi wa ‘yan uwana
2. Ina da]a sallama kuma nai salati
Ga manzona uba gun Binta Fati
Da manyan masu tsarki Alu-Baiti
Inai muku gaisuwa a cikin batuna
3. Sahabbai ku gaba ]aya na yabe ku
Ha}i}a babu wanda ya kai kamarku
Rasulu kuke wa ]a’a babu shakku
A Makka da sanda yay yi zama Madina
4. A yau wa}ar ga Higher zana yi ta
In bayyana martabar ta in karrama ta
Ku bi ni a hankali duk za na furta
A wa}an nan da zan yi wa malamaina
5. Higher Islam ta Zariya sayyida ce
Gidan ilimi, ha}i}a ta kasance
Uwa mai ba da mama ha]a]]iya ce
Gaba ]aya ba kamar ta jihar Kaduna
6. Karatu ~angaren boko akwai shi
Na addini ko nan ne dandalin shi
Dukan fanni na ilmi to akwai shi
Bila shakkin nake saito batuna
7. A Higher za a koya ma karatu
A}ida, har da Kur’ani ka saitu
Ka waye kanka ba ya cikin akwatu
Dukan ilimi ka san shi ka zarce sauna
8. Kimiyya har da lissafi akwai su
Da Larabci da Turanci ka ji su
Ka zamto malami ka }ware a darsu
Ka zarce sa’a da sauran alamina
9. Ina teachers na Higher kun yi kirki
Kuna koyar da yara babu birki
Inai muku sannu na yaba wanga aiki
Rahimu ya sanya sakamakon ku Janna
10. Aliyyu Principal ai jarumi ne
Wajen ilimi da kamewa gwani ne
Tafarkin ayyukan shi abin yabo ne
Rahimun Rabbi kare malamina
11. Cikin zamaninka ne Higher ta farka
Ta ]aukaka har ta zarce sa’a a harka
Gaba ]aya ci gabanta yana gareka
Ha}i}a na yaba ma shugabana
12. Aliyyu Rufa’i kai ma na kira ka
Inai ma jinjina kuma na yabe ka
A mulkin duk da kai ba ma da shakka
A kan ka kama hanyar adilina
13. Hakan nan Vice imam ne, zahidi ne
Abin koyi, wajen fi}ihu gwani ne
Ba zan manta da kai ba cikin batuna
14. Rabo ]an Abdu Musa ya yi aiki
Wajen ]a’a, yana da hali na kirki
Gwanin kyauta da karrama malamaina
15. Ina ]an Shisu ango ne ga Fati!
Wajen Adabi yana bayar da baiti
Bi fadlika kan Adab an sami saiti
Kabiru yana yaba maka ]an uwana
16. Basiru Abu-Habiba ina yabon ka
Wajen iya furta sauti ba kamarka
Gwani ne kai kana cika ayyukanka
Ilahi ya taimaka maka jarumina
17. Jawabi ka iya shi }warai Haruna
Wajen hikima da hujja ka fi sauna
Wajen aikinka ba wasa Haruna
Ina fatan musun nan za ka daina!
18. Fari mai kyan hali AbdulMaliki
Wajen Nahawu ha}i}a ka yi aiki
Hakannan ba ka yin rowa ga maki
19. Habawa Alhajin Allah Jamilu!
A Mathematics fa dole a sa Jamilu
Ina rokon Ilahi Zul Jalalu
Ya ma baiwa ta aure sahibina
20. Uba ga Nusaiba KB malamina
Inai maka jinjina ya sayyadina
{ira’an nan da kak ke kar ka daina
Ilahi ka ninka ladan ]an uwana
21. Imamu Sa’id ina kai gaisuwata
Uba ne kai wajen yara da mata
Mutum ne kamili kuma bai da mita
Allahu ya kare gwarzon malamina
22. Muniru Abubakar na zo gare ka
Inai ma jinjina don ba kamarka
Kana bun}asa ilmi ba ruwanka
Da wawayen mutane zalimina
23. Habu Sabo mutum ne mutunci
Da kamewa, sa’annan ga kawaici
Akwai ha}uri wajen sa da salihanci
Inai ma jinjina ya ]an uwana
24. Uban Jummai da Mathematics Zubairu!
Shahadar Maths inai maka ni Kabiru
Professor kake gun Maths Zubairu
A fannin babu tsara gun gwanina
25. Iyayen ka’ida Malam Habibu!
Tsakanina da shi kun san da hubbu
Allahu ya taimaka maka ya Habibu
Bisa tsare ayyuka don kar ka daina
26. Tazarce Rabi’u, gwarzo a Higher
Akwai shi da kwarjini ba ya musayya
Lawal Garba ina gaishe ka lauya
Allahu ya sa ka zam gwamnan Kaduna !
27. Mutan birni su Salisu na kira ku
Wajen Business a Higher na kamarku
Ka sai da tufa ka koyar babu shakku
Allahu ya ba ka dacewa batuna
28. Hasan Sabo uba ne shi na kowa
Primary tashi ce kowa da kowa
A gai da Hasan uba gun ]alibaina
29. Da malam Amadi mai Hausa sannu
Akan aikinka ba ka }yale dainu
Ina gaishe ka sannan na yi sannu
Tabaraka Rabbi kare jarumina
30. Kabir M.K. da Gboko ina yabonku
Da Yusufu Imtihani ]an uwanku
Aliyyu da Sani na dawo gareku
Primary taku ce ya ‘yan uwana
31. Da malam Nasirunku da Jafaruna
Da Auwal Sani shi ne malamina
Da shi da Aliyyu babban sahibina
Inai maku sallama ya malamaina
32. DhiyaudDini na dawo gareka
A safe da yamma ba gwarzo kamarka
Wajen aiki da bayyana mazhabinka
Ka saurara gareka nake batuna
33. Umar Sheshi Kabiru yana kiranka
Da kai da Umar Abas ai babu shakka
Kuna tsayuwa akan aikin da harka
Kuna daga martabar Higher wurina
34. Bashiru Lawal fitaccen malami ne
A fannin Arabiyya hazi}i ne
A boko ya wuce raini ku gane
Ya Rabbi ka }ara ilmi gun gwanina
35. Ina Ironmu [an Asabe gwanina
Mutum ne kamili kuma bai hiyana
Yana cika ayyuka da tsare amana
Sakin fuska ]abi’ar malamina
36. Lawal ango na Hauwa da na kira ka
Ka amsa kai da Hauwa uwargidanka
Da kai da ita kuna ]aga wagga harka
Ta Higher Allah saka malamaina
37. Lawal sarki na teachers sai gareka
Ina kake malamin Higher in gan ka
Kana koyar da tafsiri da kanka
A da can ya akai yanzun ka daina?
38. Bala ]an Bauchi ne ai ]an garinmu
A don haka koda yaushe kuke ganin mu
Muna yin fira labarin jiharmu
Ta Bauchi }asar da can ne assalina
39. Haba M.A. ka saurara ka ji ni
Ka tabbata ka fi raini ni gare ni
Gama kai ne fa Master yau gare ni
Ina fatan ka dara kan batuna
40. Da Malam Abdu kai ne walfayanmu
Kana kuma nuna jin tausai garemu
Kana samar da hallin mushkilarmu
Ina rokon Ilahi ya }ara }auna
41. Da NuridDini Exams Officer ne
Ina ]an Bello Shehu abin yabo ne
Dama AbdulAzizi mujahidi ne
Ina gaishe ku ya ku malamaina
42. Habun Shika har Sulaimanu gare ku
Da Hamza Abas da sauran ‘yan uwanku
Primary ku ku ke gyara da taku
Kuna aikin a-zo-a-gani wajena
43. Ina kake ya Namata ina kiran ka
Da Shisu da Mustafa Allah ya saka
Da Hamzatu malami ne babu shakka
Inai muku jinjina ya malamaina
44. Mutanen nawa kun ga yawa garesu
A don haka bai yiwo na }ididdige su
Wa]ansu da }yar fa in ma zan tuno su
Ku min uzuri ku yafe kuraraina
45. Ku min afuwa wa]anda na tsallake ku
Gazawa ce da rauni gun }aninku
Ku yafe, }addara ce ta fa auku
Allahu ya sa ku gane dukan batuna
46. Ina ro}on Ilahi ya }ara himma
Ga dangina ya ba su sifa ta girma
Su zarce sa’a su kere dukka tsama
Ya }yautata ayyukansu ga ]alibaina
47. A nan zan dakata domin na huta
Da wa}an nan da tun tuni nai ta bita
Bakandamiya ta Higher nak kira ta
A dandamalin Ukaza nake batuna
48. Kabir, kun san ni ba ba}o bane ni
A wa}ar Hausa ba sabo bane ni
A da can na yi nan gaba za ku ji ni
Da ikon Rabbi Sarki Khalikina
49. Inai muku sallama dangi ku amsa
Abin da kuke na kirki kar ku fasa
A nan zan ]an tsaya domin na nisa
In ce Allah ya saka malamaina
27 ga watan Yuli, 2002
Zariya.
How to play Baccarat on the online casino
ReplyDeleteBaccarat is an ancient card game which is played at the 바카라 사이트 카지노 판 village of Yucatan. It was the first to become available in the United States for two