Sunday, April 3, 2011

BAN KWANA

BAN KWANA

Wannan wa}ar na yi ta ne lokacin da na fahimci ba sauran alamu na samun wata nasara game da al’amarin neman auren Zainab Tukur; yarinyar da na yi wa wa}ar sar}ar bege. Ma’ana lokacin da na cire rai da yuwuwar yin sulhu tsakani na da ‘yan uwanta ballantana a kai ga batun aure.

Don haka ne ma na kira wa}ar ta da suna Ban kwana. Wato ban kwana da Zainabun kenan ko in ce ban kwana da soyayyarmu da ita.

Karin wa}ar na ]auko shi ne daga wata wa}ar ‘yan mandiri da aka fi sani da wa}ar Gidwon; wa}ar da wani bakano ya yi lokacin da aka datse kan wani kafiri mai wannan sunan, wanda aka ce ya goge kashi da fallen takardar Al-{ur’ani mai girma.

Mawa}in na maimata amshin ta da cewa

Hadisi littafin Allah
            In an taba ba za mu bari ba


Ni ko sai na ce:

Abulle zo ki ]an ji batuna
            Ni yau gareki nai bankwana

Ga wa}ar nan:

1.    Allahu Rabbi shi nar ro}a
       Domin ya sa na }ara haza}a
       Wa}en da nai nufin zan sa}a
       Allah ya sa na cimma nufina

2.    Na mi}a ton dubu na salati
       Gun Annabinmu baban Fati
       Sannan na sanya Alul-baiti
       Manyansu har da yara }anana

3.    Su ma sahabu ban manta su
       Manya da sun ka ba da jininsu
       Har dukiya sukai hijirarsu
       Duk sun ka tattare a Madina



4.    Wa}ar ga yau ta ban kwana ce
       Don yanzu dangana ta dace
       Duk shekarun ga sun }i, na nace
       Sun zam abin tuni a wajena

5.    Danginki sun tsaya sun turje
       Kan a’a walla su sun cije
       Ba sa nufin su bar mu mu saje
       Sun tsinka jijiyar begena

6.    Ke kin sani ina }aunarki
       Ni ma ina yabo a gareki
       Don kin ri}o da alkawarinki
       Kai Abu ta gwada min }auna

7.    Duk yanzu ya zamo tarihi
       Duk ya wuce kamar ya subahi
       Ke kin sani batun ga sahihi
       Sam babu kuskure a batuna

8.    Domin a yanzu ni na lura
       Harkar ga babu niyyar gyara
       To baitukan ga sai nar rera
       Domin su zam kamar ban kwana

9.    Allah ya ba ki ladan }auna
       Allah ya sa ki jure rashina
       In kin mace ki je Aljanna
       Ni ma ya yafe duk laifina

10.  Allah ya ba ki mai canjina
       Har ma ya sa ya zarce ajina
       Ni ko ya sa na jure }una
       Allah gareka nai ro}ona

11.  Ke kar ki manta tauhidinki
       Ai duk abin da yas same ki
       Allah ya }addara shi gare ki
       Shi ne Ubangiji Rabbina

12.  Samu da kishiyarsa ga bawa
       Allahu ne yake tsarawa
       Shi ne Ubangiji mai baiwa
       Bayinsa har da ni nan kai na

13.  Matar mutum fa ai kabarinshi
       Wannan batu ki dinga tuna shi
       Allah idan ya tsara abin shi
       Ai babu wanda zai mai ~arna

14.  To tunda an buga an }ara
       Ce-ce-ku-ce akai an kaura
       Kullum batu kamar na gadara
       Ni Abu na fa yanke }auna

15.  Yau shekara biyar ba }ari
       Muryar maza tana kakari
       Kullum batun yana da]a wari
       Raina yana ta famar }una

16.  Duk fa]i-tashi ni na sha shi
       Kan son ki an gwada min }yashi
       Wallahi sun zubi na adashi
       Ran kwashiya akwai jin }una

17.  Sun ce mijinki ai sun za~a
       Mai arziki da yalwar te~a
       {arya fa walla ai sun shar~a
       Allah wadai da wannan ~arna

18.  Sun takura ni har ke kan ki
       {arshenta har da ma dokoki
       An ce ki bar fita ]akinki
       Wai don mu daina kallon juna

19.  {arshenta yanzu sun ]auke ki
       Sun ce fa tun da ba ki da kirki
       To yanzu za ki bar danginki
       Yanzun zamanki sai a Kaduna

20.  Sun toshe duk kafar da muke bi
       Don saduwarmu babi-babi
       Sharri da }age ko sun bib-bi
       Sun ya]a zantukansu a kaina

21.  Allahu Rabbi Shi ne shaida
       Zai kunyata ku ni ko ya fidda 
       Shi Rabbi gaskiya zai tsaida
       Allah ya sa ku gane batuna

22.  Tun da fa mun zubar da hawaye
       To yanzu alfijir ya waye
       Ha}}in da kun ka zam kun tauye
       Allahu za ya fid da kaina

23.  Share idonki kar ki yi kuka
       Mi}a wa Rabbi dukkan harka
       Allah ya ba ki duk albarka
       Allahu Jalla mai jin }ai na

24.  Girmanku ya riga ya fa]i
       {arya ku kai kuna jin da]i
       To yanzu sai ku daina nisha]i
       {aryarku babu sauran }una

25.  Ya Abu ke ]iya mai kirki
       Mai hankali, batun ga gare ki
       To ]an tsaya ki ]an ja birki
       Domin ki ji ni hasken }auna

26.  Zan dakata a nan in huta
       Wa}ar ga wadda nay yo bita
       Allah ya sa ana ta fahimta
       An gane martanin zancena

27.  Nai sallama da fatan hairi
       Allah ya ba mu babban jari
       Sannan da dukkanin alheri
       Allah ya kai mu duk Aljanna

11 ga watan Yuli, 2002

Giya]e.

No comments:

Post a Comment