Tuesday, April 5, 2011

TURA TA KAI BANGO


TURA TA KAI BANGO

Wa}a ce da ke da ma’aunin Larabci mai karin

Faa-i-laa-tun    Faa-i-laa-tun

Wato karin da a ke ce wa Ramlu a larabce.

Na yi ta ne a kan soyayyarmu da Zainab M. Tukur da na ba da labari a baya. Lokacin da na ga cewa mutanen da suka shiga tsakanin soyayyarmu da tsakanin cin nasararmu sun tsaya tsayin daka don ganin cewa sun kawo }arshen dangantakarmu ko ta halin }a}a.

Ga wa}ar:

1.    Asgari zai rera wa}a
       Rabbi }ara min haza}a
       Baitukan su yi kyau ya sa}a
       In gama ban karare ba




2.    Nai salati gun Rasulu
       Amadi shi ne Khalilu
       Gun Ilahi Zul Jalalu
       Ban ga gwarzo ni ya kai ba

3.    Alu baiti ina yabon ku
       Ku sahabbai na sako ku
       Masu ]akin Mahi har ku
       Ni ba zan ware guda ba

4.    Yau }asidar ba nisha]i
       Baitukan sam babu da]i
       Yau tsaya ki ji wanga ta]i
       Abu ba zan ba da ke ba

5.    Rayuwata ta yi }unci
       Na nutse a cikin ka]aici
       Ba ni ko da cin abinci
       Lafiya ba dai garan ba

6.    Ko da yaushe ina tunani
       Ko ka ji ni ina bayani
       Sai ka ce wani mai jununi!
       Ba jununin ko garan ba

7.    Sai bala’in so da }auna
       Ni da Abu muke wa juna
       ‘Yar da yanzu tana Kaduna
       Abu ba yau za ta zo ba

8.    {ila ma ta wuce Abuja
       Kai batun nan babu ko ja
       In ta je ta garin Abuja
       Ta yi nisa ba ka]an ba

9.    Abu ‘ya ce mai mutunci
       Ta kasance mai karamci
       Yanzu ta fa]a ka]aici
       Don ba ta gana da ni ba

10.  Tun da dai kin }aunace ni
       Ba ki son aibi gare ni
       Abu ni kin tallafe ni
       Ni ba zan manta da ke ba

11.  Ni ha}i}a kin biya ni
       Kin ka killace so gare ni
       Shi ya sanya kin ka gan ni
       Ban ha]a ki da kishiya ba

12.  Duk wuya kin sha a kai na
       Har bala’i har da }una
       Kin ka nunan so da }auna
       Ba ki yaudari zuciya ba

13.  Zan ri}e ki bisa amana
       Rabbi }aro so da }auna
       Har ya zam mun auri juna
       Ba mu zam mun tarwatse ba

14.  Hassada da yawan mugunta
       ‘Yan uwa ku bari da }eta
       {addarar Allah ku bar ta
       Ba ku ce wai za ku ja ba

15.  Kun ka tsangwani ‘yar uwarku
       Kun hana ta zama cikinku
       Don tana so na, ganin ku
       “Wai ba zai dace da ke ba”

16.  Annabinmu ko ya hane ku
       Kan ku tilasa ‘yar uwarku
       Kun sani, kun kau da kanku
       Ba da hujja ko guda ba

17.  Ni yabo na gun Ilahi
       Don a}idata falahi
       Ban da shi Allah Ilahi
       Ban fa yarje ma wani ba

18.  }addara Allah ka yin ta
       Rabbi mai tsarin bajinta
       Mai cikar }udurar sarauta
       Bai yi tsara ko guda ba

19.  To idan shi yan nufata
       Za na zam fa miji gare ta
       Walla dole ku ban hanunta
       Ku ba za ku iya da ni ba

20.  In ko Allah bai nufa ba
       Bai zamo ya }addara ba
       Sam ba zan aure da ke ba
       Ko ba kui lura a kai ba

21.  Na sani in har na samu
       Rabbi ne ya nufa na samu
       Sanda duk na rasa Alimu
       Shi ya tsara ba da wai ba

22.  Dan Adam sarki na rauni
       Bai da }arfi don ya ba ni
       Ni da ku sam babu  raini
       Da a ce ba ku tsangwaman ba

23.   Ko ya ce wai zai hana ni
        Wagga }arya ce ta raini
        Rabbi dai shi za ya ba ni
        Ba da sa hannun mutum ba

24.   Ni da ku mu zuba mu je mu
        Kar ku fasa nufinku har mu
        Rabbi Allah agaje mu
        Ba ka bar mu da ‘yan uba ba!

25.   Kan kwa]ai kun kau da kanku
        Kun rufe ijiya da jin ku
        Za ku fa]a ku a teku
        Can cikinta ba za ku sha ba

26.   Wai a samo masu harka
        Alhazai manya na Makka
        Mai zuwa safara Amurka
        Ba student wai ya ni ba

27.   Wai batunku a sami dokta
        Mai yawan naira ku ba ta
        Wanda zai tsotse jininta
        Ba da alfarma ta so ba

28.   Ko a ce manaja na banki
        Ko sarakai masu doki
        Masu ji da isa da mulki
        Inda sam ba a san wuya ba

29.   Arziki Allah ka yin shi
        Har talauci kishiyar shi
        Babu wanda ka yi da kan shi
        Rabbi bai ga sa’a da]ai ba

30.   Ba yabon kaina nake ba
        Kun ga ni ba jahili ba
        Ba kamar wanen ku ne ba!
        Ba da}i}i ne fa ni ba

31.   [alibi ne mai haza}a
        Mai cikar ladabi a hal}a
        Kar ku nuna min zala}a
        Don ko walla ba za ku sha  ba

32.   Don akwai future gare ni
        Mai alamar kece raini
        Don akwai baiwa gare ni
        Ba kucaki zan zamo ba

33.   Kai ku koma hankulanku
        Don ku daina zubar da kanku
        Sai ku }yale ‘yar uwarku
        Ba ku zam ‘yan tsangwama ba

34.   Sai ku tuba gurin Ilahi
        Don ku zam samun falahi
        Rabbi shi yay yo subahi
        In ka }i shi ba za ka sha ba

35.   Zuciyata ta yi }una
        Yau tsaya ka ji martinina
        Kun ci bashi walla guna
        Sam ba zai da]in biya ba

36.   [an halas ku ka wa fitsara
        Kar ku ]auka za ku dara
        Don ko fansa za na tsara
        Ni ba zan yafe da]ai ba

37.   Basuka na kun ka ]auka
        Ran biya ai za ku koka
        Ran da fansa za na ]auka
        Ba da tausai za na zo ba

38.   Ramuwa ai ta fi gayya
        An wuce zamani na kunya
        Ba kawaici babu sanya
        Ni ba zan sake nufi ba

39.   Wanga aiki ya ishe ni
        Babu sauran }yale raini
        Ba ]agu na kafa gare ni
        Martani ba za ya kau ba

40.   Rabbana Sarki Alimu
        Mu gare ka muke batunmu
        Addu’ar da muke ka ba mu
        Khairi, karami da babba

41.   Laifuka Allah ka yafe
        Tun na da, har yau da safe
        Har na nan gaba duk ka yafe
        Babu mai haka ban da kai ba

42.   Dukanin khairi ka ba mu
        Hassada, Allah tsare mu
        Har da makirci da jurmu
        Ba mu zam mun karkace ba

43.   Nan nake so za na huta
        Wagga ‘yar wa}a da nai ta
        Tuntuni ne kar ku manta
        Kar ku ce ai ban fa]a ba

44.   Sallama naka yi gare ku
        Sai ku amsa ban da tsurku
        Bai da amfani gare ku
        Ko da dai ba ku san hakan ba

27 ga watan Yuliya, 2002.       

Zariya



1 comment: