ABIN MARMARI
Wannan wa}a tana daga cikin wa}o}ina na farko-farko, wa]anda na fara gwada fasahata ta wa}a a kansu.
Asalin abin da ya faru har na yi ta shine, lokacin ina karatu a Legal Misau, wato a tsakanin 1995 kenan zuwa 1997 na kasance mamba a }ungiyar Hausa Fasaha;wadda }ungiya ce ta marubuta da manazartan harshen Hausa. Dukkan ]aliban dake ]aukar darussan Hausa a Kwalejin ‘ya’yan }ungiyarne kai tsaye bisa al’ada.
To amma sai na lura cewa akwai mutane da dama daga cikin ]aliban wa]anda ba su ma so a ce su Hausawa ne ballanta ma a ce suna da wata ala}a ta nesa ko ta kusa da wannan }ungiya, tare da cewa wasunsu ma har da Hausa a cikin darussan da suke nazari a makarantar.
Wannan ya zaburar da ni a kan yin wannan wa}ar don ta zama kamar tunatarwa ga ire-iren wa]annan mutane.
{arin wa}ar na Larabci ne wanda aka fi sani da suna Mutakarib. Yana da kari kamar haka:
Fa-uu-lun Fa-uu-lun Fa-uu-lun Fa-uu-lun
Fa-uu-lun Fa-uu-lun Fa-uu-lun Fa-uu-lun
Ga wa}ar:
1. Da sunanka sarkin dukan duniya
Ya Jalla Tabaraka Sarki ]aya
2. Allahu ka kyautata niyya garan,
Ka kare ni sharri irin na riya
3. Ka kare ni sharri da dukkan tsiya
Ka bani fasahar fa]an gaskiya
4. Na }are }asidar ga ba gargada
Na }are da hairan cikin juriya
5. Salati nake yi da ]imbin yawa
A gun ]an Amina Balarabiya
6. Sahabbansa, matansa, danginsa har
Da sauran wa]anda sukai shiriya
7. Ina so in nushe mu ya ‘yan uwa
Zuwa ga muhimmin batun gaskiya
8. Batun nan nufina akan }ungiya
Ta Hausa Fasaha idon duniya
9. A nan tsangayar babu shakka muna
Da girman isa ba batun fariya
10. Dukan }ungiyoyi muna kan gaba
Idan ka yi shakka tsaya ka jiya
11. Da farko muna da ubanni da ma
Sauran shugabannin da sun ka tsaya
12. Suna mana aiki suna ]aukaka
Batunmu a yau a cikin duniya
13. Shirinmu shirin raya harshenmu ne
Muna son ya ]aukaka duk duniya
14. Ka zauna ka duba ka ]an bincika
Ka ba ni misalinmu in ka iya
15. Tsaya in gaya maka ko ka gwada
Ba za ka iya ba kana shan wuya
16. Ga kalubale gun students a yau
Wa]anda a Hausa suke dubiya
17. Ka gane da cewa kana da haki
Na ]aukar batun ci gaban }ungiya
18. Abin kam da kunya a ce wai a yau
Ana nazarin Hausa nan tsangaya
19. Amma kuma ba a nufin ci gaba
Na harshen, ana ta gudun }ungiya
20. Ku amsa batuna ina tambaya
Ina manufar raina harshen iya?
21. A Hausa karin magana an fa]a
Kowab bar gida ya tsirar da tsiya
22. A wannan batu dole mui azama
Muna nazarin Hausa nan Kulliya
23. Amma mun }iya mun }i mui azama
Da wannan batu ci gaban }ungiya
24. Muna soke hanjin cikinmu muna,
Kirari muna so a ce mun iya
25. Ha}i}a ina ba mu shawarwari
Mu so }ungiyarmu mu ]au gaskiya
26. Mu mi}e mu taru dukan ‘yan uwa
Mu aikata aikin da }arfin tsiya
27. Mu lura da cewa dukan }ungiya
Tana son ta haura mu ko da tsiya
28. Kirana gareku ku amsa mani
Ku ciccike forms ]in shiga }ungiya
29. Muna jin takaicin a ce har a yau
Wannan }ungiya na ta yin zilliya
30. Ina kuke ya ‘yan uwa ]alibai
Da ke nazarin Hausa, zo ku jiya
31. Ku gane da cewa dukan ci gaba
Da ma cin ta baya ga ku zai tsaya
32. Ku san duk abinda ya kai yai kwana
Na ci gaba ku ne abin godiya
33. Ku }ara sanin in ko tad dur}ushe
Ku ne da abin bincike bai ]aya
34. In zaku tuna wanga harshenmu ne
Da shi an ka sam mu a Nijeriya
35. Idan ko hakan ne ina hikima
Ta janye jiki daga harshen iya?
36. Ka ba ni dalilinka ko manufa,
Da tas sa ka ke }in shiga }ungiya
37. Wannan }ungiya dai ta fanninka ce
Tana yi da kai kuma ko ka }iya
38. Abinda kawai ya fi daidai da kai
Ka ba da hadin kanka baki ]aya
39. Ina ma nasiha ina garga]i
Ina sa ka hanya ka san shiriya
40. Ka mi}a wuya ban da janye jiki
Ka sa gudumowarka ya ]an iya
41. Mu harha]a }arfinmu baki ]aya
Mu tallafi wannan uwar }ungiya
42. Iyayen azanci suna ta fa]ar
Wai sarkin yawa na da }arfin tsiya
43. Allahu ka saka wa ‘yan }ungiya
Da hairan, ka kare su dukkan tsiya
44. Da shumagabannin cikin }ungiya
Da sauran iyayenta baki ]aya
45. Anan zana huta da wa}ar da nai
Allah sa mu dace a kan gaskiya
46. Wa}en nan da nay yi akan }ungiya
Ta Hausa Fasaha a nan zan tsaya
47. Sunanta Abin Marmari nai kira
Cikinta a kan kare harshen iya
48. Allah yi salati ga Manzo da ma
Sauran mabiyansa da duk auliya
49. Ka yafe ni duk zunubaina ka sa
Wa}en nan ya zamto abin shiriya
50. Sunana Kabiru Abubakari
Ina da zama ne a can Zariya
51. Na rubuta wa}ar a ranar biyar
Ga watan ga domin bi]ar shiriya
52. Allah ya ha]a mu a Darussalam
Ku amsa da amin gaba ki daya
05 ga watan Yuli, 1997
Misau.
TA|A KI[I
Wannan wata wa}a ce da na yi ta don in ambaci wasu mutane da suke nuna mini }auna. Dalilin da ya sa na kiraye ta da wannan sunan shi ne, saboda na yi ta ne a lokuta mabambamta, wato na rubuta mafi yawancin baitocinta ne a lokuta dabam-dabam. Sai daga baya ne na zo na harha]a su suka ba da wa}ar a jumlace.
Karin wa}ar na ]auko shi ne daga wata wa}a da na ta~a gani a wani shiri na wasan Hausa na musamman mai suna Mu shakata.
A wannan shirin wanda firarraki ne ake yi da taurarin wasan Hausa, }ar}ashin jagorancin kamfanin ha]a finafinai na Mandawari ne aka nuno wata shahararriyar jarumar wasan Hausa mai suna Fati Muhammad tana wa}ar bankwana da wasan na Hausa saboda za ta yi aure.
Amma yana da kyau a nan na ambaci cewa na yi wa karin kwaskwarima ko kuma in ce na sake masa salo ta hanyar mai da shi layi biyar biyar; Layin farko gajere ne yayin da ukun tsakiya suke da tsayi iri guda, sai kuma layin }arshe wanda shi kuma ya fi sauran tsayi.
Wa}ar tana da amshi kamar haka:
Ya Tabara,
Ya Rabbi ka ba mu tsira da dacewa
Maimakon cewa da take yi:
Ya Muhammad,
Sunnarka nake ta so in ta ya]awa
Ga wa}an nan:
1. Ya Tabara
Rabbana ka da]an basira
Baitukan nan duk na tsara
Ka tsare ni ga yin asara
Har na }are ni na zam ba ni sarewa
2. Gun Rasulu
Nai salati gun Khalilu
Rabbi Sarki Zul Jalalu
Dukka rana har da lailu
Shi nake ro}o ya yi mani dacewa
3. Wanga baiti
Nai yabo gun Alu-Baiti
Har sahabbai masu saiti
Ko da Manzo yai wafati
Sunnarsa suke ta bi har da ya]awa
4. Wagga wa}a
Rabbi }ara min haza}a
Baitukana duk na sa}a
Rabbi ro}ona na mi}a
Laifukan da nake da su kai ta yafewa
5. Baitukana
Wanda yau su zani gina
Zuciyata babu }una
Don masoya za ni nuna
Ni Kabiru ina da su ba su }arewa
6. Nura Tela
Gwarzo angon Nabila
Za mu }ara ma da Laila
Wata yarinya jamila!
Su biyun duka sai ka zam za ka aurewa
7. Mai gidana
Ni gareka ina ta }auna
Alheri ne batuna
Sai ka yafe kurakuraina
Don ko Rabbi yana ta son masu yafewa
8. Mai jama’a
Kai ka koya min sana’a
Ka ga ni dai na yi sa’a
Walla ni ba na bara’a
Gun yabo ko ka ga ni ba ni sarewa
9. Zo ka zauna
Kai Mu’awiya ]an uwana
[an tsaya ka ji baitukana
Yaushe za mu wuce Kaduna
Ran bukinka Kaduna can za mu tarewa!
10. [an Barewa
In kana can mui ta kewa
Mui ta burin }arikewa
In ka dawo babu yawa
Allah sa NECO gaba ]ai ka cinyewa
11. Sai gareka
Kai Aliyyu ina yabon ka
Na amince ba ni shakka
Kanka, ba rowa gare ka
Allah sa Hauwa’u kai za ka aurewa
12. Ni uwata
Ba ni daina yabo gareta
Don tana sona, batunta
Duk a kwanan rayuwarta
Addu’a taka yi gareni da dacewa
13. Har da Abba
Abbana na da haiba
Addu’a naka yi ga Abba
Ya Ummi da ke da Abba
Allah sa Aljanna ku za ku komawa
14. [alibaina
Duk cikarsu suna ta so na
Addu’ar kirki a kaina
Gun Tabaraka Khaliqina
Shi suke ro}o da]ai ba su fasawa
15. Zaina Abu
Ya mai kyau babu aibu
Ni ro}o na ga Rabbu
Shi ne Masani na gaibu
Ni ya }addara Abu ke za ni aurewa
16. Sai gare ki
Rabi Asgar na yabon ki
Babu shakka kin yi aiki
Lada Allah ya ba ki
Allah sa ladan zumunci ki kwashewa
17. Na waiwayo ki
Ke Suwaiba kina da kirki
Na jinjina wanga aiki
Ni na yaba taimakonki
Allah sa Firdausi ke za ki zarcewa
18. Har da kai ma
Khamis ya ba da himma
{aunarmu yake da zimma
Allahu ya }ara himma
Gun ibada don ka zam ba ka ta~ewa
19. In na juyo
Gun Amini babu ~oyo
Zan yabo gun masu wayo
Kai Ahijjo ka daina wayyo
Rabbana zai taimake ka da dacewa
20. Auwaluna
Mai Shago zo ka zauna
Na jinjina jarumina
Malami kuma sahibina
Gun hadisi ni da shi naka togewa
21. Ka ga Nura
Shi aboki ne na fira
Mai haza}a ne da lura
Allah sa duka za mu tsira
Ran }iyama duk sira]i mu haurewa
22. Masu niyya
Jarumi angon Badiyya
‘Yar mutunci ce da kunya
Ga ta ‘ya ce mai biyayya
Kai abokina fa ya sami dacewa
23. Jarumina
Albani malamina
Kai nasiha nan gurina
Allah saka ma da Janna
Allah kar~a ayyukanka da sakawa
24. Sannu Gamji
Murtalan sunna da caji
Ko gida ko da a daji
Ba ni shakka kanka ban ji
Ayyukan da kake na hairan da kyawawa
25. Allah saka
‘Yan uwa kun ba ni fuska
Kun bi Allah babu shakka
Ku zumunci kun ha~akka
Rabbi yai baiwa gareku da sakawa
26. Ya masoya
Gaisuwa naka yi masoya
Zuciyata ba }iyayya
Sai batun }auna gareku da godewa
07 Ga watan Janairu, 1999
Zariya
Rabbana "Malam" tsare Shi ## Hassadar makiya a kan Shi
ReplyDeleteKai dadin hikima gare Shi ## Har basira duk ka ba shi
Yai ta ci gaba babu fashi
Dalibin ku:
Muhammad