Tuesday, April 5, 2011

MARDIYYA

MARDIYYA

Mardiyya Ahmad Bello wata yarinya ce da ta nuna mini }auna }warai! Babu shakka wata ‘ya ce wacce ba zai yiwu na manta ta da wuri ba. Duk da Allah bai }addara mata ta ce ba, kamar dai mafi yawan ‘yan matan da suka nunan }auna wa]anda Allah bai }addara aure tsakaninmu ba.

Na yi mata wannan wa}ar ne lokacin tana tashenta a zuciyata. Kamar in ce tukuici ne na }auna.

Wa}ar }war hu]u ce. Karinta karin baka ne.

Ga wa}ar:

1.    Bismillah Allah Rahmani
       Allah Sarki mai zamani
       Ni ro}ona gun Rabbani
       Ya ba ni basira mai riba




2.    Ni na yi salati mai tsoka
       Ga Muhammadu babban manzonka
       Da sahabbai manyan bayinka
       Alaye ma ban ware ba

3.    Nai ro}o gun Allah Rabbi
       Wa}en ga ya zamto ba aibi
       Allah ka hana ni zama gabi
       Allah ka raba ni da tababa

4.    Yau wa}a ta ta masoya ce
        Mardiyya sai ki sakankance
        Ki ji wanga batu da na tantance
        Wa}ar ba mai ]aci ce ba

5.     Mardiyya ]iya ce mai kirki
        Akwai ha}uri a ]abi’unki
        Kabiru yana yaba halinki
        Ba zan manta da karamci ba

6.     Ha]uwarmu da ke ban manta ba
        Tun ma ba ki }are aji shida ba
        Balle fa a ce kin zam babba
        Har yanzu ba ai wata ba ke ba

7.     Ke wajen haza}a ba dama
        Kullum karatu babu zama
        Duk karatuka ba kya }yama
        Ba wanda kike }i ko gaba

8.    Kwanyarki tana ja gun hadda
       Allah sa ki kunyata mahassada
       Sune wa]anda suke kasada
       Mardiyya ki zam ke ce a gaba

9.    Doguwar ]iya mai kyaun fuska
       Mai murmushi da yawan fa]aka
       Mai zakira, Allah san barka
       Manya kuke kune a gaba

10.  Na sani kina matu}ar sona
       Wallahi kina nunan }auna
       Tabbas karamci kin nuna
       Allahu ya saka ‘yar baba

11.  Mardiyya ki gane ai cewa
       Ko da yaushe walla ina kewa
       Don tuna ki ‘ya ce mai baiwa
       {aunarki da]ai ban fasa ba

12.  Ni a rayuwa yau burina
       Mardiyya ki zam mai ]akina
       Domin ki sanyaya ruhina
       Sai na zam da]ai ban ta~e ba

13.  Ko da yaushe ni a tunanina
       Ke nake tunawa ko a ina
       Kin zamo batun birnin raina
       Ba tare da na numfasa ba

14.  Ke first class ce ‘yar gata
       Ko gidanku ke ce ‘yar auta
       Ban da wadda tai matsayi ya ita
       Ki ji wannan har ki fa]a a gaba

15.  Matan garin ga tsaya ki jiya
       Duk yawansu kan ke ]ai na tsaya
       Allah sa batun ga da nai ya biya
       Ba zai zam na yi a banza ba

16.  Don Allah ki ]an rage kishinki
       Zafi na so a kwakwalwarki
       Tuntu~e yake ga haza}arki
       ‘Yar uwa ki zam mai hanga gaba

17.  Mai halin kamala Mardiyya
       Mai kyaun kama, jikar manya
       Muryarta za}wai ya balarabiya
       Ga ta ‘yar fara da kalar kwalba!

18.  Dukka ayyukan shirme ki bari
       In kin }i ko kya sha mari!
       Har ma ina fatan }ari!
       Dariya kike ba kuka ba?

19.  {yaliya da neman jayayya
       Ki bari, hakannan yin }arya
       Bar taimakon mai kusheyya
       Don yin hakan bai dace ba

20.  Mardiyya ki saurara ki jiya
       Nasihohi ne za na biya
       Don cika wa ha}}in soyayya
       Ba wai akan ~atanci ba

21.  Farko ki tuna da a}idarki
       {addara ta Allah Rabbinki
       Ki yarda ki bar nuna fushinki
       Ba za a wa Allah wayau ba

22.  Kin sani ina matu}ar son ki
       Allah ya sa in aure ki
       A sannnan za ki ga }aunarki
       Ta bayyana ba da ragowa ba

23.  Karatoci ki kula kin ji
       Ko da yaushe dole ki ]au caji
       Aiki ki yi shi kamar inji
       Ba wai ki zamo mai rauni ba

24.  In kin ka kula mun daidaita
       In kin }i tabbas mun ~ata
       Ba na jure sakarci da ~ata
       Ba zan kuma jure takaici ba

25.  Harka ta shirme babu fita
       Shirmantaku da yawan mita
       Ba sa iri ]ai da nagarta
       Hala ba ki gane batuna

26.  ’Yar da Asgari ke }aunarta
        Dole ne ta zam kan saitinta
        Hankali, haza}a siffarta
        Ai kina da su ba wai ne ba

27.  Ki tsaya mu gyara jawabinmu
       Mu ri}e amanar junanmu
       Gaskiya ta zamto cinikinmu
       Yadda sam ba za mu saranye ba

28.   Ba miskilanci ba gaba
        Banda raina yaro ko babba
        Haka nan ki bar nuna manuba
        Ban yarda da wannan ko ]ai ba

29.   Wa}ar ga nan zan }are ta
        Allah sa kina saurarenta
        Har ki gane komai ki fahimta
        Allah sa batun bai tsauri ba

30.   Bissalami nai miki ban kwana
        Allah sa mu gane halin juna
        Sannan mu zauna da amana
        {aunarmu ba }arama ce ba

31.   Zunubanmu Rabbi ka gafarta
        Matsalarmu Rabbi ka yo mafita
        Zuciya ka sa mu fi }arfinta
        Ko ba ki ji? Ba ki amsa ba

32.   Tammat bi hamdil Lahi, tsaya
        Sai an jima ke Mardiyya
        ‘Yar gidan karamci, tarbiyya
        Ba zam manta da karamci ba

03 Ga watan Maris, 2002

Zariya.




1 comment:

  1. A guide to all casinos in your area, including casinos, bingo
    In the USA, the 아시안부키 minimum deposit in online 블랙 잭 룰 casinos is $10. 라이브바카라게임 BetMGM 벤 델핀 casino, an 벳인포해외배당흐름 online bingo, has a minimum deposit of $10.

    ReplyDelete