Sunday, April 3, 2011

Dokta Dije

DOKTA DIJE

Wa}a ce da na yi baitocinta a wurare dabam-dabam, a lokuta dabam-dabam na nisha]i ko tuno wasu abubuwa da suka faru a gare ni musamman na neman aure ko ‘yan matan da na ta~a yin soyayya da su. Kusan a ce wa}ar tana kama da lissafin sunayen ‘yan matan da suka so ni a lokuta mababmbamta.

Sunan wa}ar ya samo asali ne daga sunan Khadijah AbdulLahi Usman, wadda a kanta na fara asalin baitocin da sune na farko a wa}ar, Dokta Dijen la}abi ne da }awayenta da wasu abokaina suke kiranta da shi.

Wa}ar }war biyu ce. Mai karin larabaci ce wanda ake kira da suna Hazaj a larabce, wanda yake kamar haka:

Ma-faa-ii-lun  Ma-faa-ii-lun
Ma-faa-ii-lun  Ma-faa-ii-lun
           


Ga wa}ar:

1.     Khadijatu ‘yar gidan Audu
        Kabiru yana ta gaishe ki

2.     Mijin da yake ta }aunarki
        Yake da nufin ya aure ki

3.         A da can na yi soyayya
            Da ‘yan mata gabanin ki
           
4.         A har kullum suna so na
A tun kafin na ma san ki

5.         A yanzun ma suna so na
Cikinsu da ma sa’anninki

6.         Ina Dijen }asar Borno
            [iyar Kanuri mai kirki
           
7.      Fara mai kyau da annuri
Gidansu akwai ]iyan banki

8.         Kamar Zainab ]iya ga Tukur
            Da Mardiyya ]iyar kirki



9.      A da can ma da Sadiyya
         [iyar da ta ba ni mamaki

10.    Wurin magana da lallashi
          A zuciya ko akwai miki

11.       Da Zara tana da kyaun }ira
            [iyar manya gidan mulki

12.    Ha}i}a Zara na da aji
Akwai ilimi na mamaki

13.       Sa’annan ga ta ‘yar gayu
            Gwanar }unshi da sa taki

14.       Da A’i ]iyar mutan Gombe
            Tabawa gwana wajen girki

15.       Zubaidatu ma fa ta so ni
            Da Saratu wacce ta san ki

16.    Da Maryamu ‘yar mutan Bauchi
            Ina shaidar ta gun kirki

17.    Da ma Hasana ]iyar Ado
            Da tan nace wa angonki!

18.    Da Asiya ma tana so na
            Tana da hali na mamaki

19.    Tana da nufin na aureta
            A bayan na fa aure ki

20.    Da Mairo ]iya a gun Goggo
            Da Sadiyyar garin Paki

21.    Akwai ma wadda ke ki ka ce
            Tana da nufin ta canje ki

22.    Tuna da batun da kin ka jiyo
            Ba}in kishi ya dame ki

23.    Ki kai ta fushi kina kwafsi
            Abin kunya da mamaki

24.    Akan maganar da ba hujja
            Ki ce Allah ya yafe ki

25.       Da Fauziyyan kasar Neja
Gwana gun sanya jan-baki

26.       [iyar da a kan ta an ka mani
            Abin da ya ba ni mamaki

27.       Abokai har da ma dangi
Suna magana suna tsaki

28.       Batun da suke maras tushe
            Idan na ji ba na sa baki

29.       Akwai takwara da sunanta
            Iri daya ne da ma na ki

30.       [iyar Sule Kugu yarinya
            Fara mai kyau da yin wanki

31.    Da Raudatu ‘ya ga [ansabo
            Da wacce ake kira Balki

32.       Halinsu guda wajen natsuwa
            Da]ai ba a sakin baki

33.    Da Aisha ‘yar gidan Mamman
Farar aniyarki jalinki

34.       Haba zo kin ji yarinya
Kabiru yana tunaninki

35.       Gidansu gidan mutunci ne
Gidan ilimi, gidan kirki

36.       Ina ma so ya zam samu
Na aure A’i  bayanki

37.       Saboda na sami dacewa
            Da mata har da ma suruki

38.       Batun da nake ta yi ha}}un
Ki yarda ki daina yin tsaki

39.       Ina da farin jini sosai
            Hala ya ]ara akan naki

40.       Gama duk inda nas sauka
            Na kan ci karo da tamkarki

41.       [iya mata suna so na
            Suna nunan halin kirki

42.       Ki san dai walla na yi fice
            Wajen mata sa’anninki

43.       Suna so na suna bi na
            Kamar mota maras birki

44.       Ki san ni ]in ga hot cake ne
            Akwai }alubale kanki

45.       Ki bi ni a sannu ‘yan mata
            Ki zam adu’a da ]an masaki

46.       Wajen Allahu mai rahama
            Gama shi ne ka]ai Sarki

47.       Maji ro}o, Abin bauta
            Gwanin hikima Gwanin mulki

48.       Ki mai bauta, ki ro}e Shi
            Ki tsarkake dukka aikinki

49.       Ki san shi yah ha]a ni da ke
            Ya sa naz zam abin son ki

50.    Abin da ya sa na lissafo
            Ki ]au izina ki san aiki

51.    Yana da yawa idan kika ce
            Kina da nufin ki zo ]aki!

52.    Da sunan ke amarya ce
            Da tad dace da ]an kirki

53.    Saboda akwai a har yanzun
            Wa]anda suke ta saran ki

54.    Suna kishi suna ta nufin
            Ina ma dai su canje ki

55.    A don haka ga nasiha ta
            Tsaya ki jiya da kunnenki

56.    Ki gode Rabbana Allah
            Akan kyautar da shi ya miki

57.    Ta’ala shi ya za~e ki
            Cikin dubbai ya tsamo ki

58.    Sa’annan sai ki san cewa
            A dole ki nuna }aunar ki

59.    Gareni ki zam a ko yaushe
            Kina kare masoyinki

60.    Ki daina yawan fushi, kishi
            Ki yi shi a kan abin kirki

61.    Ki zam hakuri da sassauci
            Da yin afuwa ga angonki

62.    Idan na kure ki yafe min
            Kamar dai yadda za na miki

63.    Zaman aure ki san cewa
            Da yin ha}uri yake taki

64.    Honesty ma makami ne
            Kamar ya rufi na kan ]aki

65.    Idan kika nuna }aunar ki
            Garan zan ba ki mamaki

66.    Ki zam matar a-zo-a-gani
            Ki zam model ga }annanki

67.    A }arshe dole ne na yaba
            Wa halayenki ‘yar kirki

68.    Hakika ni fa nai dace
            Da mata mai cikar maki

69.    Fara, mai kyau da annuri
            Abin so gun mutan kirki

70.    Ina ki ke Dokta Dije tsaya
            Ki ]an dara wa angonki!

71.    Ina tuna zantukan da muke
            Ina tuna ‘yar harararki!

72.     Ina fahari da kirkinki
             Basirarki da halinki

73.    Da yadda kike da kamewa
            Da kunya kwalliyar kirki

74.    Ki daure gun karatunki
            Ki je Medicine da karfinki

75.    Da kin gama yi ki zam likita
            Ki amfanar da danginki

76.    Anan da za na ]an huta
            Da wa}en nan da nay yi miki

77.    Da fatan za ya zam cewa
            {asidar nan ta burge ki

78.    Idan kuma na ga ya dace
            Hala zan }ara tsamo ki

79.    Ki }yalkyala dariya da yawa
            Ki ce well done da bakinki

80.    Ki basar kan kuren da na yi
            Ki manna min ku]a]enki

81.    Allahu ya bar ni tare da ke
            Ya zam aurenmu babu saki!

82.    A ce mutuwa idan ta zo
            Ta dauke ni ta dauke ki

83.    Sa’annan Rabbana Allah
            Ya ba mu gida na mamaki

84.    Cikin Aljanna Firdausi
            Ya sa manzo ya cece ki

85.    A ceton har da angonki
            Uban ‘ya’yanki gwarzonki

86.    Ki ce amin ki }ara fa]in ta
Amin Rabbi ya Sarki

87.    Ka amsa min ka yafe ni
            Ta’ala Sahibul Mulki

88.    Ana nan sai ta canza zani
         Iyaye sun ka }ware ki   

89.    Khadijatu kin ga na so ki
         Ubanki ya ba ni mamaki

90.    A bayan ya amince min
         Muna ta shiri irin na biki

91.    Dare ]aya sai ya zo shi kwatsam
         Ya ce in daina neman ki

92.    Ya ce ba za ya ban ke ba
         Da hujjar wai a danginki

93.    Akwai wasu masu son girma
         Da ke son kar na aure ki

94.    Suna cewa akwai yaro
         Abin so gun su ]an kirki

95.    Ya ce wai sam ba zai yiwu ba
         Ya sa~a, don ina son ki

96.    Na han}urce na ce na ji
         Na yarda da }addarar Sarki

97.    Abin bauta da shi ya haramta
         Aikata duk ba}in aiki

98.    Ilahi ya yi min canji
         Da ‘yar da ta zarce tsarar ki

99.    Iyayen ‘yar ko sun zarce
         Irin tsarin iyayenki

100.  Sakinatu ke nake }auna
         Ina zimmar na aure ki

101.  Iyaye har }awayenki
         Suna nunan halin kirki

102.   Mutunci har halin girma
          Da so, harkar da mamaki

103.   A yanzu ina da tabbas ni
          Hani gun Rabbi shi Sarki

104.   Idan ya yi shi gun bawa
          Ya kan zam gun mutum taki

105.   Ya canza mai da alheri
          Kamar dai yadda yai kan ki

106.   Ya canza min da yarinyar
          Da nab bai wa dukan maki

107.   Wajen ilimi na addini
          Da ma boko da yin wanki!

108.   Ina godewa Allahu
          Sa’annan ba na yin raki

109.   Sakina a yanzu har kullum
          Kabiru yana ta }aunarki

110.   Ki sha kurumin ki yarinya
          Ki san wallahi tarkonki

111.   A yau ya kama mai girma
          A don haka ki ta yin mulki

112.   A Zuciya babu tamkarki
          A fili babu tsararki


113.   A randa ko duk na aure ki
          A rannan kya ga mamaki

114.   A sannan za ki san cewa
          Ina fahari da }aunarki

115.   Ina fatan kina ji na
          Kina ta yaban a kan aiki

116.   Kina yin murmushin }auna
          Yana haske a fuskarki

117.   A nan zan dakata yanzu
          Da niyyar don na ]an bar ki

118.   Ki ]an huta da zancena
          Da fatan za mu hau doki

119.   Na }auna mui ta yin sukuwa
          Muna taku cikin mulki!

120.   Salamul Lahi zancena
          Ki ]an amsa wa angoki


121.   Iyakar baitukan kenan
          Da fatan za su burge ki

04 ga watan Janairu, 2007

Argungu.

No comments:

Post a Comment