Wednesday, April 6, 2011

MAKOMA

MAKOMA[1]

Tun sanda nai wa}ar Tazarce nake son in yi wa }iyama wa}a. Allah bai sa na sami ikon yin hakan ba sai a wannan lokacin.

Na yi amfani da Karin wa}ar baka ne a wa}ar. Asalin karin na ji shi ne a wata wa}a ta ]an uwa Zil}ifilu Muhammad Basir.

Na kawo ta a }arshen wannan kundi nawa ne bisa la’akari da cewa makomarmu itace }iyama. To bisa hakan sai na sanya wa}ar da ke batu a kan wannan makoma a matsayin }arshen kundin. Kamar dai ace ina mai yin arashi ne da ita. Don haka ne ma na kiraye ta da sunan Makoma.

Allah ka sa mu yi }ya}}yawan }arshe ka kuma bam u makoma mai }yau ta ni’ima. Amin.

Ga wa}ar:

1.  Zan wa}e ran }iyama Rabbi Sarki ka }ara ban hikima

2.  In na tuno ta zuciya da dukkan jiki su ]au kyarma

3.   Hantar cikin jikina sai ta motsa kai har da ma nama
 
4.   Kullum ina nadama laifukana da nay yi ko zulma

5.   Lakar jiki ta narke sai ka ce wanda yaf fito fadama

6.   Domin tuno da lokacin da ranar ga za ta sauko ma

7.   Ranar da za a tara duk halitttu rannan akwai fama

8.   Kowa ya zo tsirara babu wanda ya zo da takalma

9.   Matar da ke da juna biyu nan take za ta haife ma

10. [an }an}anin mutum  a lokacin nan zai zama mai girma

11.  Har ma da furfura, kowa tsaye don ko babu tabarma

12.  Kowa ka gan shi ya firgita ya }e}ashe kamar tsumma

13.  Rana tana ta }ara zafafa kuma ba batun lema

14.  Don bainaha wa baina ‘yan adam mil guda take a sama

15.  Ba wane babu mai mu}ami sai Jalla Rabbi mai rahama

16.  Har za ya tambaya ya ce “A yau wai ina mazo girma?”

17.  Ba wanda za ya amsa wanga question kowa yana kyarma

18.  Sai shi da kansa za ya ba da amsa  ya Rabbi mai hikima

19.  Baki ]aya mu amsa babu ya Rabbi dole an bar ma

20.  Dogon wunin ga za a sha wuya ‘yan uwa mu ]au himma

21.  Kowa yana shiru abin da ke faruwa akwai girma

22.  Ceto a lokacin ga ran }iyama shi ne abin nema

23.  Babanmu Adamu, da Nuhu in an ka ce su je su ma

24.  Musa Kalimu har da ]an gidan Maryamu ha]a har ma

25.  Babban bada]iyi gurin Ta’ala ba wata alfarma

26.  Kowa cikin biyar ]in ga ya ce walla yau fa ba dama

27.  Amma ku je ga wane ni da kaina a yau nake fama

28.  Na tafka laifuka, gun Rabbana yau ina bi]ar rahama

29.  {arshe a zo ga ]an Amina manzonmu sai ya ]au azama

30.  Zai je wurin Ilahi ni da kai mu fa za ya ro}o ma

31.  Sau}i da rangwame wurin hisabi, dangi mu ]au himma

32.  Domin mu san shiga cikin shi ceton nabiyyi mai girma

33.  Sannan a ce da shi ya kwashi dubbai cikinmu al’umma

34.  Aljanna za ya kai dukansu sun tsira sun shige ni’ima

35. Allah Ubangiji nake ta ro}o yai mini alfarma

36.  Domin na zam cikin wa]anda Allahu zai yi wa rahama

37.  In tsallake sira]i ni da abbanmu har da ma umma

38.  In sha ruwa a tafkinsa na haura cikin yawan salama

39.  In tsere duk azaba ta wutar Hawiya da Jahannama

40.  Duk wanda ran }iyama a ka }ona shi ba shi ba girma

41.  Ya zam abin kwatanci na asara ya rasa duk }ima

42.  Dangi mu ba da gaskiya da Allah mu daina yin zulma

43.  Sannan mu daina shirka da fasadi da duk abin }yama

44.  In mun tuna da laifuka mu tuba, mu daina yin gulma

45.  Sannan mu dinga bin rasuluna za mu sami alfarma

46.  In mun biye wa zuciya da son ranmu walla ma zarma

47.  Don ran da za a ta da mu nadama ba ta da da ko }ima

48.  Duk masu yin ta za su ]an]ana, za su fa]i ba girma

49.  Ni ko da yaushe tausaya wa kaina nake musamman ma

50.  In na tuna da laifukan da nai  wanda ba su }irgo ma

51.  Allah ka yafe ]an Abubakar Asgari yana nema

52.  Tsira gurin ka kai ka]ai Ta’ala kai ne kake rahama

53.  Ranar da za a auna ayyuka, litattafai a kwaso ma

54.  In ka yi ayyukan kwarai a mi}a a ce ka sa dama

55.  In ayyukan ko sun zamo na banza to sai ka sha fama

56.  Kowa a rarraba a kai musulmai cikin gidan ni’ima

57.  Su ko munafikai da kafirai sai a kai su Jahannama

58.  Ni ko a nan nake nufin na }are batun ga don da ma

59.  [an tsokaci nake nufin na furta gare ku al’umma

60.  Allah ka yafe kuskuren da nai har da inda naz zarma

61.  Nan za na sa ]igo na tashi, }arshen batun da nai salama

07 ga watan Nuwamba, 2007

Zariya




[1] Ita ce wa}ar da nai ishara a can baya a cikin wa}ar Tazarce cewa zan yi wa}a akan lahira 

No comments:

Post a Comment